← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 129

Sashe 114

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk Kallon mamaki suke bin Baba dashi shiko nuna zahra kawai yake "MD ne yayi k'arfin halin cewa " Dan Allah Baba kayi mana bayani ina kasan wannan "hawaye na fita daga idon Baba ya ce " y'ata ce d'aya tilo dana mallaka Nina haifeta a tare Nida ita akayi mana harin da har kuka tsinceni tsawon shekaru bansan Inda take ba a tunani ma ta rasu saboda Bansan Inda sukayi da ita ba "cike da mamaki Ammy ta ce Ka nutsu dai Baba wannan ba y'arka bace Mahaifinta Yana Chan Funtua kuma wannan yarinya ce ma bata kai shekarun da kake Tunani ba kadai duba Baba" mik'awa MD yaron Baba yayi ya nufo Inda Zahra take da duk a tsorace ta ke kama hannunta dake d'auke da zoben da awarwaran da tunda Baba ya bata yake hannunta yayi Kallon zoben da awarwaran yake Yana murmushi yana hawaye ya ce "Kece Mamy ashe daman idona zai sake nunamun ke ina raye Mamy na nine Mahaifinki Mai kaunarki ko kin manta ni zahra'u ko kema sun juye miki kwalwar ne Dan karki tona musu asiri kamar yanda suka juyemun tawa Mamy ki tuna mahaifinki Malam Abdussalam sai kuma ya Rungumeta tsam a jikinsa ya ce " Alhmdllh Alhmdllh Allah na gode Maka da ka nuna mun wannan yara y'ata da na shekara da shekaru ina begenta yau gashi Allah ya had'amu ta yanda banyi tsammani ba "ido ido kawai ake tsakanin Ammy da MD har Chuchu zahra ko Itama kuka ta fashe dashi Tabbas wannan din shine kakanta shine mahaifin Mamanta dukta k'are MD ne ya taso yayi kokarin raba su ya ce " ka nutsu Baba kayi mana bayani wannan ba wacce kake tunani bace "Sassauce ruk'on da Baba yayiwa zahra yayi ya juya ya kalli MD ya ce " Haba yaro ya zakamun gardama na haifi y'ata na kasa ganeta"Juyawa yayi yana kallon zahra dake Kuka ya tallabo Fuskarta kallonta ya dingayi yana son yaga banbanci tsakanin ta da mahaifiyar Ta" motsa bakinki "ya fad'a a hankali zahra ta motsa mamaki ya kama Baba ya ce "To ya haka da sanin da nayi mata tun yarinta abun nan d'aya gareta amma yanzu naga biyu " Cikin muryar kuka zahra ta ce "Ba waccen Da kake magana bace y'arta ce " ta fad'a tana hawaye"duk mamaki yagama. Cikasu Ammy ce ta ce "Kamarya y'arta ce kunsanyani cikin duhu fa Dan Allah ku warware mana " Zaunawa Baba yayi jibis yana mamakin jin Abunda ya fito daga bakinta MD ne yaja numfashi ya ce "da Alamun akwai wani Abu a kasa please ku nutsu ku warware mana muna cikin duhu " cikin muryar kuka zahra ta ce "Babana ya bani labarin mahaifiyata yana aikin noma.ya tsinceta a lokacin Bata cikin hayyacinta har aka samu akayi mata magani Dan da ko magana batayi sai daga baya da aka dage da rokon Allah kasancewar gidansu babana duk malamai ne koda ta farka bata iya tuna komai ba sai sunanta ta ce Musu sunanta " Zahra"a haka har Allah ya sasinta kansu da babana sukayi Aure Wanda suka zauna a funtua wajen sana'arsa yace bata tab'a tuna wani nata ba ko ita kanta wacece Sai lokacin da ta haife ni Wanda a nan ta ciro zoben wannan da awarwaro dake hannu na ta basa ta ce idan na girma ta bani zasu taimaka mani wajen gano danginta daga nan bata Kara ce dasu Komai ba game da asalinta Har Allah yayi mata cikawa"Ta k'arasa fad'a cikin kuka "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Ashe karshen saduwata da Zahra'u kenan a rayuwa ,ashe bazan sake ganin y'ata ba d'aya Dana mallaka Allahu akhbar Su mudan basu samu damar kasheta ba kenan Allah mai iko zahra Har saida ta haihu ashe Allah sarki zahra'u Allah ya jikanki yayi miki rahama yasa kina cikin rahama hakika mamy baki mutu da hakkin iyaye ba Kinyimun biyayyar da bakowani d'a zaiyiwa mahaifansa haka ba allah ya jikanki Ashe bazamu kara saduwa ba sai a darussalam Zahra'u ke kika rigani tafiya ashe ba rabon mu sake ganawa yana hawaye ya kamo hannun zahra ya ce " Tabbas ni nan nine kakanki Nina Haifi mahaifiyarki Wannan awarwaron da zoben Tabbas nata ne ko babu su kamanninki da mahaifiyarki kadai sun isa duk wani ahalinmu ya ganki ya shaidaki Allah ya taimaka Mudan bai ganki ba na tabbata da ya ganki tofa da ya zama dole ya kasheki "Mudan " Ammy ta maimaita zahra ko jin abun take tamkar almara wai yau itace gata ga kakanta,yau itace taga jinin mahaifiyarta ,Allah sarki wasu hawayen farinciki ne suka zubo mata tana murmushi ta ce"Kana nufin kaid'in kaka na ne kai ka haifi mahaifiyata daman da rabon zanga dangin Mama a duniya "ta fad'a hawaye na zubo mata saikuma ta Rungume Baba ta ce " Alhmdllh Allah na gode Maka da ka nunamun wannan ranar tamkar almara Baba najima da bakincikin Rashin sanin dangin mahaifiyata bantaba kawowa a raina ba zan hadu dasu Cikin Sauki haka meya kawoka gidan nan har yayi silar haduwata dakai Baba"ta k'arasa fad'a tana hawaye "Rungumeta sosai Baba yayi yanajin kaunarta kamar yanda yakejin k'aunar y'arsa data rasu " sosai su Ammy suka girgiza dajin al'amarin nan Chuchu da Ammy da Hajiya kaka da bata jima da shigowa ba hada hawaye MD ko mamaki ya gama cikasu cewa yayi "mezai hana Baba ka bamu labarin abunda ya raboka da garinku da wadanda sukayi harin rayuwarka da ta iyalanka " Saida suka saki juna daga rungumar da sukayi da zahra kafin ya goge hawayen bak'inciki da takaici ya ce "Yau zan baku labarin asalin waye ni da kuma silar shigarmu cikin wani hali ta dalilin d'an uwa Nida y'ata asalinmu haifaffun Jihar jigawa ne ina da mata d'aya Hajiya Saratu ina da kanne Shida Wanda muka fito ciki d'aya uwa d'aya uba d'aya sai Wanda muke uba d'aya Mudan Wanda shine autanmu shi kadai mahaifiyarsa ta Haifa har Allah yayiwa iyayenmu gaba d'aya a hankali a hankali rasuwa dalilin wannan ya sanya muke matuk'ar sonsa muke jansa a jiki bamu tab'a nuna masa y'an ubanci soyayyar da nake nuna masa ko Wanda muke uwa d'aya uba d'aya bana nuna musu tun ina yaro daman ni natashi mutum ne mai neman na kansa na kasance Dan kasuwa tun ina K'ananan kasuwanci da noma har Allah ya habaka na zama Babban attajiri a garinmu Wanda daidai ne zaka fad'a suna na Alhaji abdussalam Mai fata na samu sunan nan da dalilin Kasuwancinsu fatocin da nayi Mata ta d'aya Hajiya Saratu wadda tsawon shekaru bamu tab'a haihuwa ba sai Bayan shekaru har manyantaka ta fara kamani Allah ya bamu haihuwar y'armu Fatima wacce taci sunan kakarta ne ta wajen uwa hakan yasa Muka fiyan kiranta da "Mamy " Gata da soyayya ba irin Wanda bamawa Zahra'u kasancewarta y'a daya tilo a wajenmu amma dukda gatan da muke bata baihanamu bata ilimin boko da na arabi ba Gabak'i daya Na d'auki yarda na bawa Mudan Wanda Duka huldar kasuwanci na Shi na sanya a ragamar abun kasancewar girma ya fara kamani shi kuma lokacin yana tashen yarinta duk wasu garuruwa da nake huld'a dasu shi yake zuwa ya wakilceni sosai na dorasa akan dukiya ta saboda yarda Wanda a ido ya nunamun yafi kowa kaunata tare da iyalina ina son mudan har cikin raina Wanda har sauran y'an uwana sukance Nafi kaunarsa akansu Nayiwa mudan duk wani gata na Gina masa Gida Tafkeke na saya masa mota sannan koda ya tashi neman Aure Nina tsaye masa Akan hidimar komai duk wani gata da Dan uwa ke yiwa Dan uwa nayiwa mudan da gangan nake sakar masa kofar dazai samu alheri ina sane saboda ina son Shima yazama wani Abu ko Bayan raina ya zama shine zai kula da iyalina da dukiya ta hakan yasa bana boye masa komai yasan duk wani sirrina yana kanena amma bani da abokin shawara sama dashi ashe bansaniba soyayyar ido mudan yakemun bansani ba ashe mudan Makasar rayuwata yake nema k'watsam wata rana da bazan tab'a mantawaba ranar bak'inciki,ranar da ta kasa goguwa a cikin tarihin rayuwata muna kwance tare da iyalina a lokacin Zahra'u ta zama budurwa Har anfara shirye_Shiryen Aurenta Dan mutane da dama bama jigawa kadaiba har sauran jahohi sukan fito su nuna.suna son zahra Saboda yarinyace mai matuk'ar nutsuwa da hankali Ga kyau uwa uba tarbiya Dan zahra bata tab'a b'atamun raiba ita da mahaifiyar ta mariganyiya Muna cikin bacci mukaji barayi sun duro mana sosai hankalinmu yayi tsananin tashi ba wacce muka tunano sai y'armu Duk mun rikice mun dunkule waje guda a haka mukaga Shigowar garda_gardan samari Wanda bazan iya cewa ga yawansu ba saboda tashin hankalin da muka shiga gabak'i d'ayansu suka zagayemu da bindiga gaba d'aya fuskokinsu a rufe Na tsakiyarsu ne ya bud'e fuskar Wanda saida na kusanyi sumar tsaye ganin Mudan ne tsaye da bindinga ya saitani dak'yal na iya D'aga baki cikin tashin hankali na ce "Mudan ,mudan" Kecewa yayi da wata mahaukaciyar Dariya ya ce "Kana mamakin gani na a nan ko to ka daina mamaki nidinnan da kake gani makashinka ne da hannuna zan kasheka yau na kashe iyalanka gabak'i d'aya zan mallaka gabak'i daga dukiyarka Tun Asali daman ni ba Kaunarka nake ba dukiyarka kawai nake So kuma Alhmdllh lokacin amsarta yayi saboda Nasan Duka gaba d'aya ilahirin adadin dukiyarka da kadarorinka ina son Ka daukomun duk wasu takkadun kadarorinka da baka bani ajiyarsu ba ka mik'omun da hannunka kafin na kasheka" sosai hankalina yayi tsananin tashi Dan uwana Ace akan dukiya zai iya kasheni nashiga tashin hankali da rudun da bantaba shiga ba ranar ina hawaye na ce "Mudan zan mallaka maka Duka dukiyar daka buk'ata amma ka sani Amana Bazata barka ba mudan ka mance cewar ni jininka ne ka zab'i da ka kasheni Akan dukiya daudar duniya Tabbas yau na yarda da cewar d'an Adam bashi da Tabbas" wata irin Tsawa ya dakamun ya ce "Bana buk'atar jin wani Wa'azi daga gareka ka bani abunda na fad'a" Suna tisamun bindiga aka naje na D'auko masa gabak'i d'aya takaddun kadarorina sannan nasa masa hannu a wasu takaddun da tashin hankali baisa na tuna takaddun menene Matata cikin tashin hankali da bak'inciki ta ce "Amma kaidai
Chapter 114 · 0% Book details