Sashe 118
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
musu Dariya ya ce "oyoyo my kids I really miss you so much please karku sake nesa da daddynku zai shiga wani Hali"Daidai shigowar Zahra Cikin hijab sab'e da Alkhbar tunda ta shigo palourn MD ya kafeta da kallo Bako kiftawa yanajin wata irin kauna da soyayyarta na Kara fusgarsa ji yake kamar yaje ya rungumeta Harta zauna Yana kallonta a sace Zahra ta kellesa idonsa suka sartse Cikin na juna sauri tayi ta kauda Kai gabanta na faduwa nauyayyar Ajiyar zuciya mD ya sauke yanajin wani irin sanyi na ratsa sa shiru Zahra tayi Bata tanka ba jabir ne ya ce "Hajiyarmu ina yini Kodai har yanzu fushin ake damu nidai ina bada hakuri Kuma ina wanke laifi na "Dan Murmushi Zahra tayi ta ce "Ina yini Yaya jabir anzo lfy"lafiya qalau ya triple dinmu "Alhmdulillahi"ta fada Kasa Kasa Tana wasa da zoben hannunta"MD bai daina kallonta ba kamar zai cinye ta Biyun ya aje kan sopa kafin ya koma kujerar da take kamar zai shige jikinta saurin matsawa tayi tare da satar kallonsa suna hada ido ta Galla Masa harara"Mika hannu yayi ya amshi little dake Zillo a hannunta Ajiyar zuciya ya sauke tare da kissing din little ya ce "i Really miss you my All above I love you so much my beloved daughter ina sonki Sosai takwarar Ammy na Kuma Favorite wife d'ina gaki Kuma daughter ta "ya fada Yana mata Dariya kamar tasan me yake cewa tahau Masa Dariya hada Zillo "Tabe Baki Zahra tayi Tana Shirin mikewa ya ruko hannunta juyowa tayi tare da tsatsaresa da Dara daran idanunta tare da juyasu ta ce "ka sakeni meye haka gaban mutane da Allah"ajiyar zuciya ya sauke Yana kallonta ya ce "Please ki dawo ki zauna Dan Allah muyi magana wajenki nazo"Kamar bazatace komai ba saikuma ta ce"Inajinka Amma ka.sakeni"Ai na sakeki nasan tafiya zakiyi Dan Allah ki dawo ki zauna" to ka sakeni Mana ha a saikace wata yarinyar nace ba inda zanifa "sakinta MD yayi ganin Bata tafi ba ya sanyasa sauke ajiyar zuciya Bayan ta zauna Dan nesa dashi Tana wani hade fuska Cikin kakkausar murya ya Fara magana Cikin sigar lallashi da kwantar da Kai ya ce"Dan Allah Dan girman Allah Mamy kiyi hakuri ki janye fushin da kike Dani wlh nayi regrade duk Abunda nayi maki bana daidai ba Ina sonki Mamy son da bazan iya kwatantashi da komai ba son da bantaba yiwa wani mahaluki irinshi ba Mamy shigowarki rayuwata nasan abubuwa da Dama Wanda a chan da ban sanshiba Mamy shigowarki rayuwata nasan meye so inasonki son da ni kaina bazance ga adadinshi ba Ina sonki fiye da yanda nake son kaina Mamy Dan Allah kiyi hakuri ko bazaki Soni ba yanzu Ina neman alfarmar da kidawo gareni mu shimfida sabuwar rayuwa irin ta kowasu ma'aurata mu gyara kuskuren da mukayi a baya mu tarbiyantar da yaranmu sannan mu Basu Kula irin wacce kowasu iyaye ke bawa yaransu Dan Allah Mamy Ina kaskantar da kaina akan kiyi hakuri ki dawo gareni insha Allahu zan koya Miki Sona da kaunata Zan Kula dake Zan soki na kaunaceki na baki duk wace kulawa Dan Allah ki ceci rayuwata please Mamy"Sosai Zahra tayi mamakin Jin furuccin nashi a gareta wai yana sonta tunani tayi bafa ita yake so ba kawai saboda yaranshine da yake mugun so shekara goma bai samu haihuwa ba shine zaiyi mata wayau yace Yana sonta ta koma gareshi Ya wulakantata shida matarshi karshema Kila ya saketa ya kwace Mata yaran tunanin wanannne ya dira tsam a cikin zuciyarta Sosai taji ranta ya b'aci lokaci guda ،mikewa tayi tare da kallonsa ta ce "zamana da Kai ya Kare babushi bazan koma gareka ba ka koma chan Wajen matarka Amma ni Nan da ka gani karka Kara tunanin wai zan koma maka inma mafarki kake. Ka farka kagama tafiyata"Tana game fadar haka tabar palourn Cikin sauri tanajin wani daci da zafi a cikin zuciyarta Jin yaudarar da suka shirya Mata a cewarta"Tashi MD yayi Cikin tsananin tashin hankali ya bita, tuni tabar palourn dafe kanshi da yayi matukar Sara Masa yayi ya ce "Innalillahi wa Inna ilahiraji'un "Ganin Yana Shirin faduwa ya sanya jabir yayi sauri ya tallabeshi ya zaunar dashi Shi kanshi jabir baiji dadin Abunda Zahra tayi ba yarasa wata irin bakar zuciya ce da ita shi har yanzu baiga wani laifin zo a ganin da MD yayi Mata ba take wahalar dashi Haka idan taimakonema ita MD ya Fara taimaka bataji laifin kawarta ba saishi mamakin MD yake Akan wani irin so ne wannan yake yiwa Zahra da har take Masa irin wanna wulakancin Yana shanyewa Wanda tunda yake bai Tana tunanin akwai macen da MD zaizo tayi Masa haka ba matanda rububinshi sure Amma ya like yarinyar karama na Shirin nakasashi "MD. Wani irin zafi yakeji a cikin zuciyarsa kamar zai fashe da kuka ya kalli jabir ya ce...........✍️