Sashe 100
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da Babana da Jabir sun cuceta " Cikin kuka Chuchu ta ce"Ammy ita Asmy ba laifin ta bane Allah duk laifin su yaya ne Kinga su Suka tsoratata akan zata rasa ta shysa tayi haka"Goge hawayenta Ammy tayi ta ce "Hakane Maza kiramun Jabir kice duk Inda Yake inason ganinsa saiyayimun bayanin dalilinsu na na yin haka wlh zasu fuskanci b'acin raina da basu tab'a gani ba Dan iskanci idan aure yake so ba har lokaci Hajiya ta basa yayi ba Dan Raini da wulakanci Shine zaije yayi Aure a b'oye su wulakanta yarinya maza kiramunshi" Chuchu na laluben number Jabir harta samesa ta kira yana d'auka Ammy ta amshe wayar cikin fushin da baisanta dashi ba ta ce "Na baka nan da minti Talatin kome.kake ka sameni a gida" hankali tashe ya ce "Lafiya Ammy?Inkazo zakaji koma.meye minti Talatin na baka" tana gama fad'ar haka ta katse wayar tana huci minti Talatin bai cika ba Jabir ya iso gidan yakira Chuchu ya shaida mata yana palour baki daya suka fita palourn Wanda kallo d'aya zakayiwa Ammy kasan ranta a matuk'ar b'ace yake "har kasa Jabir ya gaisheta ya ce " Ammy Lafiya wannan kiran gaggawar"tana binsa da harara ta ce "ba lafiya ba munafukai watau daman da munafurci da kuka k'ulla k0 to asirinku ya tonu munji komai Abu d'aya nakeso ka fad'amun gaskiyar magana yanda take kuma wlh ka sake kamun karya zaku fuskanci Karin wulakancin da zan muku daga kai har babana fad'amun Gaskiya Had'in baki kukayi da Dr wajen Auren zahra sannan dalilinku nayin hakan wannan amsar biyu kawai nake buk'ata" Hankali tashe Jabir ya d'ago yana Kallon Ammy tuni harya fara zufa cikin muryar Rashin Gaskiya ya ce "Ammy wa ya fad'a maki maganar nan" ya fad'a a rarrabe "Ammy nabinsa da harara ta ce " a tunaninki bazamuji ba ko To asirinku ya tonu Daman ance rana d'aya ta barawo rana d'aya tame kaya ba bani amsar tambayar da nayi maka fak'ad"Ammy ta fad'a cikin d'aga murya"Innalillahi Jabir ya shiga nanatawa a ranshi Tabbas dole ne ya fad'awa ammy Gaskiya Dagowa yayi kallo d'aya zakayi masa kasan ba Gaskiya ya ce "Ammy zanyi miki bayanin komai Amma Dan Allah kiyi hakuri sannan karkiyi fushi" Inajinka oya ka fad'amun karka dinga b'atamun lokaci"numfashi yaja kafin ya labartawa Ammy komai d'aya faru bai boye mata komai ba saboda daman yasan da irin wannan ranar dukda yayi mamakin yanda akai Ammy tasan da maganar Salati Ammy tayi ta tafa hannu ta ce "Naga ta kaina ni Fatima daman a saboda Amera ne kuka aikata wannan Abun kunji kunya kun rako maza wlh Babana yaban mamaki bantaba tunanin zaiyi irin wannan Rashin imaninba Ya sanya yarinya a cikin wani hali kawai saboda shegiyar amera kayan bannza kawai a saboda banzar biyan bukatarku kuje ku auri yarinya ba sanin iyayenta Kuyi mata wayau ku tsoratasu kuga mugaye azzalumai wlh babana sai yayi nadamar abunnan d'aya aikata zaisan mu yayiwa haka zaisan zahra ba a banza take ba wlh tallahi saina kwatar mata hakkinta zan mance cewa ni na haifeshi na kwatawa zahra hakkinta tamkar Nina haifeta bana zalinci sannan bana goyon zalinci Kenan so kukayi ku cuceta ta haihu ku kaiwa waccen y'ar Iskar d'an da ita kanta tarbiya bata isheta ba bare harta tarbiyar da wani mu kuma ayi mana lullubi ko to ai dayake a cikin abun ba Allah gashinan asirinku ya tonu hada had'o karyar Amera ta samu ciki toni bansan wannan wani irin so da tsoro ne babana yake yiwa amerarnan ba Abu saikace an asircesa A baka damar kayi Aure kawai saboda gudun b'acin ranta kaje ka yi Aure a b'oye ka zalinci yarinyar mutane wlh Duka a cikin abunnan banga laifin Zahra da Kawarta ba ko Kad'an kune manyan mugayen da kuka tilastasu suka amince muku macuta mayaudara Tsaffin munafukai Ka tashi kaban wuri wlh saikunyi mamaki na Akan Lamarin nan daga kai har shi Babban munafikin sannan Ka fad'amun gidan da yake idan ka fita saika kirasa ka fad'a masa ga yanda mukayi kace ya gudu da ita kaga abunda zai faru"Jabir dukya tsure ya ce "Dan girman Allah Ammy kiyi hakuri wlh nikaina nayi Nadama tsaki Ammy taja tace" ai nadama baku fara ba ma ka fad'amun gidan da yake da ita " kasa yayi da kansa yace "buzu quarters "Mikewa Ammy tayi ta ce " Saura kakirasa ka fad'a masa munyi haka tunda kunsaba munafurci tare "Kasa yayi Jabir da kansa yana muzurai saurin barin palourn Ammy tayi Chuchu dake tsaye duk tayi shock kafafuntama ji tayi sun kasa daukarta sosai Abun yazo mata yanda bata tab'a tunani ba wai Yayanta ne Mijin zahra kuma shine uban cikinta Shine sukayi *Auren wata tara* da ita idan ta tuna saitaji kamar almara Kallon screern din wayarta tayi ganin kiran da Asmy ke mata mema zata ce mata " Muryar Jabir ce ta dawo ita daga dogon tunanin data Lula ya ce "Chuchu please waya fad'awa Ammy zancen nan taya tasan wannan din" Turo baki gaba tayi Dan duk haushinshi takeji har yayan nata ta ce "Saika bi Ammyn ka tambayeta" tana gama fad'ar haka ta juya "Mikewa Jabir yayi zuciyarshi chunkushe da tunannika ta wani bangaren kuma yaji dadin da Ammyn sukasan da maganar ko ya fita daga sarkarkiyar d'aya shiga tsaka Baiyi yunkurin kiran MD ba Koda wasa Dan yasan yana fad'a masa guduwa zaiyi da ita koma subar k'asar Wanda bazaiso hakan ba Tunda asiri ya tonu gwara kawai ta fanjama " Ammy sosai ranta ya b'aci Hijab kawai ta sanya da takalmi ta fito Chuchu ta biyota ta ce "Ammy ina zaki kuma Yamma tayi fa" daga mata hannu tayi ta ce "Ki koma yanzu zandawo zanje na taho da yarinyar nan tun yanzu kafin abokin munafurcin nasa ya kirasa " Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke Ammy na fita ta kwalawa driver kira Ta ce ya kaita Abuja cikin Sauri "Ba bata lokaci motarsu ta dauki hanyar Abuja ana gab da magriba Suka isa Kai tsaye buzu quarters suka nufa......MD na zaune a Palour ya na dafe da kansa Saboda yau ba k'aramun kuka zahra tayi masa ba akan ya maida ita gidan iyayenta ga Allah ya isa da ta dinga ja masa yau ko.abincin kin ci tayi duk ta chaza masa kai yajiyo knking Kamar bazai Mike ba saikuma yaje ya bud'e gabansane ya bada daram cin karo da Ammy tsaye fuska ba wasa lokaci guda Alamun Rashin Gaskiya suka bayyana k'arara a fuskarsa a rarrabe ya ce " Am my "ka bani hanya na wuce " Ammy ta fad'a a tsawace 'sosai yayi mamakin abunda baitab'a gani daga Ammyn nasa ba Hankalinsa sosai ya tashi waigawa yake Kar zahra ta fito Ammy ta ganta asirinsa ya tunu"tsawar da Ammy ta daka masa ce ta sanyashi matsawa ba shiri daidai sanda zahra ta fito daga daki cikin doguwar Hijab Fuskarta jab'e jab'e da hawaye Tsaye Ammy tana kallonsa tana kallon zahra sosai zahra tayi mamakin Ganin Ammy a gidan Gabanta banda fad'uwa ba abunda Yake Sosai ran Ammy ya k'ara b'aci tunkarar wajen zahra Ammy tayi tare da kama hannunta tajata itadai zahra binta kawai take har suka isa Inda motar take ammy ta ce "shiga " ba musu zahra ta shiga motar Kallon Ammy MD d'aya biyosu yayi cikin tashin hankali ya ce "Ammy" Daga masa hannu tayi cikin Tsawa ta ce ..............✍