← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 129

Sashe 35

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina kika shiga tun jiya hankalinmu tashe munyi ta kira bakya d'auka kuma yanzu motar waye naga ya saukeki momcy hada sauya kaya" Banda fad'uwa babu abunda gaban Zarah yake wannan tirkiya da Chuchu ke shirinyi mata Asmy ce tayi charab ta ce "Ohh wai ko uncle Abba ne yazo Naga motarsa ce" Cikin Sauri Zarah ta ce "Eh eh shine yazo jiya nafita ya kirani ya ce yazo garin shine ya tafi dani Funtua muka gaisa dasu Aunty Yau ya maidoni saboda lecture" Ajiyar zuciyar Asmy ta sauke ta kalli Chuchu ta ce "k,'anin mahaifinta ne" Ajiyar zuciya Chuchu ta sauke ta ce "Ayya Allahsrk ai da kinkiramu momcy karkiga yanda na damu"Zarah ta ce " wayarce A silent kuma ina zuwa ban waiwayeta ba shiyasa "Chuchu tace " Allah sarki "wayarta ce tayi ringing dubawa tayi ta ga Yayanta cikin Sauri ta d'auka "basuji me akace mata daga dayan bangarennasa sai tsalle suka ji ta daka tare da Cewa " Da gaske Yaya na gani nan yanxu yanzunnan Dan Allah karka tafi"yana katse wayar ta kallesu cikin d'oki ta ce "yayana ne ya shigo garin yace bazai Iso ba nan na samesa a Hanya bari nayi Sauri karya wuce ta fad'a tana barin Wajen batare da ta jirayi amsarsu ba " tana tafiya a tare suka sauke ajiyar zuciya Asmy taja hannun Zarah suka wuce hostel ko zama basuyi ba Asmy ta ce "Ina kika kwana Zarah"... Nan Zarah ta fad'a mata abunda ya faru " Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wlh hankalina duk bai kwanta ba sai yanzu " Allah ya sanyama nayiwa Chuchu dabara Dan kartayi miki wata fassarar ta daban "Uhm kawai Zarah ta ce tare da kwanciya ta lumshe ido " Da damuwa Asmy ta kama hannunta ta ce "Are you okay Dia Bakyajin komai " Gyada mata kai Zarah tayi ta ce "Am okay" Asmy ce ta ce "Amma dai kinyi Amfani da maganin hana d'aukar ciki ko?cikin Sauri Zarah ta mik'e gabantane ya bada daram ta dafe daidai saitin zuciyarta ta ce " Na shiganga bansha ba wlh kina ganin sau dayan nan saina iya d'aukar ciki"Asmy ta ce "Chab Aiko wlh mu nemo ki dinga sha Dan Wlh Ana iya d'aukar ciki indai muna San asirinmu ya rufu tunda dai sun dage sai wata taran ya cika yanzu yaza ayi?Zarah ta ce " ke zaki fad'a"Asmy ta ce "idan mukaje chemist ko asibiti da niyyar saya za a iya mana mummunar fahimta sannan Kinga ba sanin Wanda baida illa mukayiba bare mu kasada mu saya kai tsaye karkije kisha abunda zaiyi miki illa shawara mafi sauki ita ce Ina wannan Dr Halima da jiya kikacemun gidanta kikaje me zai hana ki mata magana ta rubuta miki Tunda Dr ce kuma Kinga D'aukar Matar Aure take maki(Nikam Hajjo nace da Ba ta Auren bace) kamar yanda kika ban labari yanzu" Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce "Kuma hakane bari na jaraba " .........cikin shagwaba ta ce "I really miss you yaya na na fa d'auka zolayata kake nayi mamakin jin wai kazo Zaria gashi naga ko security baka taho dasu ba baka tsoron Mugaye kake yawo ba Escord please nidai ka daina yawo haka kaikadai" Kallon ta yayi Ya ce "To aku sarkin surutu kingama " Dariya tayi ta ce "Gaskiya ce Yaya kadaina yawo kai d'aya "lakutar kumatunta yayi ya ce " To Autar mu ya school din "Alhmdllh yaya lecture ta dau zafi Next week zamu fara exams hutun 2weeks zamuyi mu dawo mu shiga level 4" wow Karatunki yana Sauri Auta ki dage sosai zanyi miki special gift insha Allahu idan kika gama "Ihu ta buga tare da cewa " yeyeyeye my yaya Shiyasa nake sonka wlh insha Allah zan dage ai bantaba samun c o ko d'aya ba yaya Ina maida hankali kuma momcy ta na taimakamun sosai Dan duk abunda ban ganeba ita ke koyamun kuma na gane Ai yaya Kai kanka sai kayi mamakin baiwar kokari irin na Momcy Wlh idan tana bayani saika d'auka wata professor ce ga Ilimin addini idan tana rera karatu saika d'auka a madina take tsabar iya qiri'a nima fa ita keyi mun karin karatu yanzu haka natafi hizif hamsin yaya gashi ta had'u Tana kyau sosa....is okay uwar zuba zaiiizaiii ba full stop ina rabaki da shegen surutun nan fa ya fad'a ya na Jan kunnanta "Aucchhh yaya da zafi ta fad'a Sosai suka sha Hira da kanwartasa dukda ba Sosai yake biyewa surutuntaba dukda a mota ne sunjima kafin Suyi bankwana Bayan yayi mata transfer 200k har bakin get d'in makaranta ya ajeta kafin ya juya daman saida yaje gida ya sauya mota tukwana Suka hadu Dan karma ta gane motarsa ce Dan waccen ba kowa ya sansa da ita ba Ita Chuchu bama tasan gidanshi na Zaria ba Dan garuruwan da yake da gidaje Allah yayi yawa dasu Kai tsaye Kaduna ya nufa Dan ya k'agara yaga Ammynsa saboda lokacin da ya dawo daga America Kano ya sauka ya d'auko hanya ne ta kawosa Zaria har ya had'u da Zarah dukda da farko ba ganeta yayi sosai ba dalilin ma daya kawoshi zaria....." Haba Zarah me ya kaiki ga planning yarinyarki karama Auren farko ko haihuwa bakiyi ba Kice wai kina son kiyi planning Gaskiya ina baki shawarar ki bari saikin haihu tukwana"Dr Halima ta fad'a daga cikin wayar "Marairaicewa Zarah tayi ta ce " Ba haka bane Aunty Ina school ne to na kusa kammalawa Dan kar nasha wahala Shiyasa nace zanyi kona shekara ne kafin na gama"wannan ba wani Babban uzuri bane kanwata mutum nawa suke hada karatu da haihuwa Tukunnama mijin naki ya amince"Cikin Sauri Zarah ta ce "Eh Shima yace nayi" kin tabbatar kuwa Zarah?Eh Aunty shiyace"Okay to shikenan gobe idan naje wajen Aiki zan sai maki maganin da zakiyi amfani dashi saiki sameni a asibitin ki amsa nayi maki bayani wajen 12 na rana haka "Nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauke ta ce " nagode Aunty "washegari Daidai lokacin taje asibitin kasancewar shigar Hijab da nikab tayi hakan yasa ba Wanda ya ganeta har Dr Aliyu Office din dr Halima taje Bayan sun gaisa nan ta bata maganin da tsarin yanda zata sha Godiya sosai Zarah tayi wa Dr Halima saida ta biya kasuwa tayi musu Sayayyar chefane kafin ta koma tana zuwa Chuchu ta d'ora musu miya Dan provision d'insu hade yake daman tare suke girki....da misalin goman dare kwance Zarah ta ke ta lumshe ido mood d'insu na Daren jiya ya shiga dawo mata cikin kwalwa wani felling na taso mata saurin barin tunanin tayi Dan zata iya shiga wani hali taja tsaki ta ce mugu kawai " waye mugun"cewar chuchu"Ta d'auka a zuci tayi maganar ashe a fili ne "k'in bata amsa tayi Sai Juyawa tayi ta kwanta........" Ammy kenan Bakya missing Dina kenan shiyasa har kike cewa Na fiya zarya "Shafa kanshi Ammy tayi ta ce " Ba haka bane Babana Dan karka dinga shiga hakkin ita Matar taka"Tsaki yaja a ranshi Dan tunowa da irin rainin wayan da Amera tayi masa ya ce "Ai Ammy ita ce batason zuwa shiyasa " sannan ya d'ora kansa bisa kafadarta kamar wani k'aramun yaro ya ce "Uhm Ammy yunwa nake ji" Murmushi d'auke da fuskarta ta ce "Me kake son Kaci Baban Ammy" Murmushi yayi yana Shafa sajensa ya ce "Tuwo Miyar kubewa"da Daren nan Babana " Cewar Ammy"Eh Ammy "Tana shirin Mikewa Ta ce " Bari Naje na girka maka tunda akwai kayan hadi Dan tasan Dan nata bayacin abincin Maid House idan yana nan daman Chuchu keyi masa girki ko kuma yaci na restaurant "(nikam nace meye marabar dambe da fad'a") kamo hannun Ammy yayi ya ce "da wasa nake maki Ammy taya zan wahalar da Ammy na guda "indai kana so babana ka bari nayi maka " girgiza kai yayi tare da mik'ewa ya ce "Da wasa nake Ammy Hug d'inta yayi ya ce " Good night Dear mom"Shafa kanshi tayi ta ce "Have a nice dream my Beloved son god bless you " koda ya kwanta Kasa baccci yayi tunanin mood dinsa da yarinyar na Daren jiya ya shiga dawo masa lokaci guda yaji Yana neman burkutawa kansa lissafi Tsaki yaja a ranshi ya ce "Stupid kawai marar Kunya mata matsala ne Wlh " Kafin kuma ya ce "Amma yarinyar ta na Da dad'i over" Lumshe ido yayi ya ce "Zan kwashi gara kafin 9 months din stupid kawai villager girl " (Nikam nace kaidai ka sani MD). Washegari Azahar a Gombe tayi masa Daga shi sai Jaber kamar yanda suke zuwa haka suka isa a sirrance. Kallon dattijon dake kwance kamar ko yaushe MD yayi shiko yana ganinshi ya Fad'ad'a fara'arsa dukda baya iya komai Amma daga ganin fuskarsa zakasan yana cikin farinciki "Shima murmushin MD ya mayar masa tare da kamo hannunshi ya murza a hankali ya ce " Sannu ko Baba"Lumshe masa ido yayi tare da bud'ewa "Kamashi MD yayi ya tasar dashi Fruit ya dinga bashi a baki yana ci yana yi masa murmushi Har saida ya koshi ya daina Amsa tukwana ya d'auko Handchiep ya Goge masa baki kafin ya kwantar dashi Kallon dattijon dake gefenshi yayi ya ce " jiki ya fara sauki sosai naga"Da fara a tsohon ya ce "Alhmdllh yanzu kam Kamar ma ya dawo hayyacinshi Dan wani lokacin saika samesa yana kuka wani lokacin kuma murmushi sannan yanzu har motsa hannunsa yanayi ya ma fara amfani da hannun" jinjina kai MD yayi ya ce "Insha Allahu zai dawo daidai da yardar ubangiji Ai Babu Abunda yafi k'arfin Allah Sannan Shima na Asibitin a dinga basa magungunan Baba Karka gajiya Kaima Ladarka na wajen Allah " Tsohon ya ce "Insha Allahu kaima dai Allah yayi maka albarka ya kareka daga sharrin makiya da mahassada " Ameen MD ya fad'a Koda ya Mike Zai tashi sai na kwancen ya kamo hannunta Juyawa MD yayi ya Kallesa saiyaga hawaye nabin kumcinsa cikin Sauri ya koma ya zauna tare da Rik'e hannun tsohon cikin muryar girmamawa ya ce "Kayi hakuri Baba Zandawo insha Allahu bada jimawa ba zaka samu sauk'i da yardar ubangiji"Ta ido dattijon ya nuna masa da ya gamsu kafin ya saki hannun nasa.....a hanyarsu ta zuwa Airport Jaber
Chapter 35 · 0% Book details