← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 129

Sashe 110

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amera koda isarta jikin dadynta ta fad'a ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah dad ku fad'amun me yake faruwa bansan abunda ya faru ba hankali na bai kwanta ba " Lallashinta ya dingayi akan ta nutsu ba komai bane ta Bari ayi bincikike tukwana washegari dak'yal ta Bari gari ya waye ba yanda Mamanta batayi.da ita ba akan ta Bari a bincika aji gaskiyar Lamarin ta kiya ta ce "saitaje gidan Ammy tunda shi tayi ta kiransa kusan 1 week baya dagawa abunda baitab'a yi mata ba " girgiza kai mamanta tayi ta ce 'Ai daman Amera na fad'a maki tun ba yanzu ba akan ki tsaya kiyi zaman Aure kwata kwata rayuwar da kika zab'awa kanki ba rayuwar y'a mace mai mutunci bace"da Allah mom Ni kibarni Naji da abunda ke damu na fisabilillahi"ta fad'a tana yin gaba tana gunguni "Girgiza kai Hajiya Farida tayi ta ce "Allah ya kyauta"Dadynta ko zirga zirga kawai yake...k'arfe 7:am zaune suke a palourn Dagashi sai Ammy Bayan kiran gaggawa da tayi masa shiru yayi ya maida hankalinshi ga sauraron abunda take son fad'a masa fuska ba wasa Ammy ta ce " d'ago ka.kalleni babana"ba shiri ya d'ago yana fuskantar mahaifiyar tasa "Hannu Ammy ta mik'a masa ta ce " bani takardar Saki ukkun zahra "Lokaci guda MD yaji wani irin tashin hankali ya ziyarce sa a matuk'ar rude ya ce"Ammy saki kuma" Eh saki ko kana da wata maganar ne daman ba Dan ka saketa ka aureta ba,ba Dan ta Haifa maka d'a ko y'a ka aureta ba to ai burinka ya cika ta Haifa maka yara har Ukku kaga ko amfaninta a wajenka ya k'are dan haka ka saketa ta kama gabanta itama taje tayi Aurenta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa "Cikin tsananin tashin hankali ya ce "Ammy kiyi hakuri kibar maganar nan please ni har yanzu Mamy matsayin mata ta take kuma haka zataci gaba da zama insha Allah please Ammy kiyi hakuri kawai ki barmun matata kodan yaran nan Ammy kinsan d'an sai uwa please Ammy ina begging d'inki kidaina maganar sakin nan ba Ni Gaskiya bazan iya sakin Uwar y'ay'a na ba" ya fad'a kai tsaye "Sakato Ammy tayi tana kallon ikon Allah kafin ta tab'a hannu ta ce " ikon Allah daman Kasan da ruk'on d'a sai uwa ka shirya rabata da Y'ay'anta ka kaiwa Matarka Matar so da.kafi sonta da kowa inbanda asirinku ya tonu to wlh baka isa ba saika saketa"Hankali tashe ya d'ago ya ce "Ammy Dan girman Allah ki daina maganar sakin nan nifa bazan saketa ba period magana Zan zauna da ita na bata kulawa kodan yaranta Dan Allah Ammy naci darajan yaran nan"baka isa ba wlh watau nufinka Zama ka zauna da ita zaman Y'ay'anta lallai Babana kai harka isa ka zauna da zahra zaman Y'ay'anta zahra harta isa tayi zaman ,y'ay'a to bazata zauna dakai ba sannan zata baka Y'ay'anka kaje ka kaiwa duk ubanda zaka kaiwa ka kaiwa Amera uwarka ko iyayenta su rik'e maka y'ay'an amma.koni bazan rik'e maka su ba Tunda baka da mutunci sannan zahrar ma bazata rik'e maka su ba bari naje na D'auko maka su sannan na k'ara ganin k'afarka a gidannan Zakaga mamakin irin Rashin mutuncin dazan maka tunda Haihuwarka nayi bakai ka haifeni ba " ta fad'a a fusace tana Mikewa"Cikin sauri ya yi Sauri ya riko k'afar zanen Ammy Ya ce "Baki fahimce ni bane.Ammy Dan...bai k'arasa abunda yake son fad'a ba ta fusge zanenta cikin Sauri ta haura sama " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ya fad'a yana dafe goshinshi Daidai shigowar Amera d'akin a matuk'ar rikice "kallonta yayi yanda tashigo da itama d'in shi take kallo kafin ta karaso palourn cikin tsananin tashin hankali ta fashe da kuka tare da kama.hannunshi ta ce " Ka fad'amun Gaskiya MD me yake.faruwa Wasu Yara ne ake zancen an Haifa maka Bayan Banida masaniya ka fad'amun gaskiyar cewar bakai bane wasune kawai suke.karya da yaranka ne"Ba karya bace Yaransa ne halak malak Shiya haifesu da Matarsa da ya aura kina Chan kina yawon tambadewa a jirgi harta haihu baki saniba ta Haifa masa Yara Ukku reras lokaci guda ko kina da abun cewa ne zakizo kiwa mutane hauka da ba abunda kika iya sai bakin kishin jaraba to alkadarinki dai ya karye Duka Asirin da kika masa ya sakesa yayi aurensa ya rabu dake saiki koma Chan k'asar tambadewar taki kici gaba da tambadewa a sararin samaniya "Hajiya kaka ta fad'a tana shigowa palour" a matuk'ar rude Amera ta juya ta Kalleta kafin ta saki Hannun MD tanajin zuciyarta tamkar zata tarwatse ta ce "What sai kuma ta fashe da kuka ta ce " wlh Allah karya ne bazaiyu ba ,bazaiyu ba MD yayi Aure ya haihu da wata,karyane ,ihu ta k'walla iya karfinta tana girgiza kai kamar zata hau bori "tab'a hannu Hajiya tayi ta ce " ikon Allah to ko aljanu zata tada kihau bori Kece bishiyar kuka karewar iskokai mahaukaciya y'ar mahaukata Kaikuma Solon hofi tsayawa ma kayi kana kallonta"MD Yama rasa Inda zai tsoma ransa fitowa Ammy tayi tare da little zahra a hannunta Chuchu na biye da ita tare da biyun tana hawaye ta ce "Dan Allah Ammy kiyi hakuri karki basa yaran nan Momcy zata shiga wani hali Kinga koda kika amsosu kuka take Dan Allah Ammy kar fushi yasa kiyi aikin Dana sani" Daidai shigowarsu palourn Duk Kallon Amera suka tsayayi dake kwala ihu kafin ta chukumi MD iya karfinta ta shakesa ta ce "Daman kai Bakin Munafuki ne bansaniba,Mayaudari ne kai daman ,ashe duk kalaman da kake fad'amun na bazaka iyamun kishiya ba na karya ne to wallahi tallahi ka sani Mustapha baka isa ba kayi Kad'an ka yaudareni kaci bulus wlh baka isa ba ka hada matsayi na Dana wata ba karya ne Wlh zan kasheka zan kasheta zan kashe kaina Bayan na kashe shaggun yaran Dan wlh badai aure ba Saidai in y'an zina ne kuka haifa.Marin da taji an wanka mata ne ya sanyata Had'iye maganar da ta fito daga bakinta Dagowa tayi da kalli wacce ta maretar Ammy ta gani tsaye kanta tana huci rike da baby cikin b'acin rai Ammy ta ce " Duk iskancin da zakiyi ki tsaya iya mijinki shine Wanda zakiwa kici bulus amma ba zahra da yaranta da sukafiki matsayi da daraja a wajena ba baki isa ki shegantar mata yara ba sannan anfada Yayi Aure matarsa ta Haifa masa Yara ba karya akayi ba ko haramun ne Dan yayi Aure tunda ke kin kasa basa farincikin da kowace mata take bawa mijinta hakan yasa yayi Aure kuma da masaniyarmu yayi kece baki sani ba yanzu kuma ai kinsani"Wani irin kallo Amera Kebin Ammy dashi tana rik'e da kumcinta ta ce "Ni kika mara " An mareki Dan Ubanki ko ramawa zakiyi" "Kutumar uban nan to Inma na rama din ke uwata ce ko haihuwa ta kikayi munafukai ke mijinki har ya mutu ya taba miki kishiya ne da zaki sanya nawa mijin yayimun kishiya daman Nasan ba kaunata kuke ba shine har Kuka sanya yayi mun kishiya to wlh kusani ni Amera nafi k'arfin kishiya nafi k'arfin hada miji....d'auke da Mari har sau Ukku da taji anyi ne ya sanya ta kasa fadar abunda tayi niyyar fad'a cikin huci MD ya ce" baki da hankali ne Amera mahaifiyar tawa kike fad'awa hakan Dan iskanci ko ubanki ya isa ya fad'awa mahaifiyata haka bareke kodan Kinga Duk abunda kike ina kyaleki kina cin Darajar Abu biyu ne Inbanda haka da baki isa kiyi wani abun na kyaleki ba"kuka sosai Amera ta fashe dashi tare da k'walla Ihu duk saida suka toshe kunnuwansu Kafin ta bud'e ido Jaririyar dake hannun Ammy idonta yakai kukan kura tayi tare da nufar Ammy ta amshe Jaririyar Tana shirin timata da K'asa Zahra ta rugo A guje batasan sanda wani k'arfi yazo mata ba ta amshe y'ar daga fad'uwar da Amira taso kadata Huci kawai zahra take tana kuka Dan yau ita kadai tasan tashin hankalin data shiga da Amera ta kada mata yarnan da batasan yanda zatayi ba jijjiga yarinyar ta fad'a data fara tsala wani irin kuka kowa Ajiyar zuciya ya sauke ganin irin kokarin da zahra tayi saboda ba k'aramar shammatarsu amira tayi ba Cikin Hargagi Hajiya ta ce "Ka fitar mana da mahaukaciya Matar nan gidan nan Dan ubanka tunda ta shanyeka Ibanda sakarai ta zagi uwarka Ka tsaya kana kallonta baka sauke mata saki Ukku ba " cikin ihu Amera ta ce " da Allah iwa mutane shiru ke asuwa Ke ki sakeni d'in tsohuwar banza kawai" Ai MD baisan sanda ya k'ara d'auke Amera da wani Marin ba ya ce "Dan baki da hankali iyayen nawa da kakata kika zaga?Anzagesu din kaima wuce a zageka kayi banza d'an iska Mayaudari tana kallon zahra dake jijjiga y'arta tana kuka ta ce " Daman Y'ar Iskar karuwarka ka aura Macuci Mayaudari"waige waige ta fara tana neman mabugi Chan ta Hango Fankar K'asa cikin Sauri ta nufi wajen iya karfinta ta Karya Fankar ta d'auko K'asar da gudu ta nufi wajen zahra zata maka mata MD yayi Sauri Yarike cikin tsananin b'acin rai ya ce "Wannan wani irin hauka ne kike Amira" Kallon Chuchu da zahra Ammy tayi ta ce "Ku wuce ciki" Zahra hada gudu_gudu suka wuce Dan sosai ta tsorata da Amira Dan bata mance karansu na farko ba Cikin b'acin rai Hajiya ta ce "Bazaka saketa ba Sai kallonmu ka tsayayi ta zageni ta zageka,ta zagi uwarka ta shirya kashe maka y'ar da ka shekara goma Kana fatan samu ka tsaya kana kallonta Dan Kana Asararre"MD rasa Inda zai tsoma ransa yayi cikin bacin rai Ammy ta ce " ku barmun gida daga kai har ita inba so kake na yi muku abunda bakuyi tsammani ba "Cikin tashin hankali ya ce " Dan Allah Ammy kiyi hakuri idan sakinta kike so nayi sainayi"Daga masa hannu Ammy tayi ta ce "Bance ka saki Matarka ba ya rage ruwanku amma Abunda nakeso ta barmun palour sannan a maida mun duk abunda ta lalatamun na palour " tana gama fad'ar haka ta haye sama da Kallo Hajiya ta bita kafin taja tsaki ta ce "Kaji d'ayar mahaukaciyar a tunani na zakice ya saketa ne ko ki
Chapter 110 · 0% Book details