Sashe 128
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
aka had'e Dana Asmy da Jabir wata hudu masu zuwa Yau Zahra na kwance Baba ya kirata bayan sun gaisa yake cewa ta Mika Masa sakon godiya wajen MD Sosai tayi mamakin yanda baba yake kwaraawa me addua tare da gode Masa ita dai Zahra murmushi tayi Bata tambayi baba abunda yayi musu ba baba na katsewa maman Asmy ta kirata itama godiyarce take ta surfawa hada kukan farinciki ta ce 'Allah yayi Miki albarka Zahra sanadinki Zan take kasar da bantaba tunanin zuwa ba sanadinki Zan sauke farali Allah yayi Miki albarka Zahra Yasa a gama lafiya ya Raya muku zuriarku godiya Sosai mama ta dingayi sai sannan Zahra ta fahimta kenan aikin hajji MD ya biyawa su baba Sosai taji Dadi Kuma tayi farinciki Koda ya dawo Tana Fara Masa gdy ya Girgiza Mata Kai ta Ce "Sun chanchanci fiye da haka Mamy kome.nayi akanki ban fad'i ba ke Kika Fara bani farincikin da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwa kingako dole wani ma Wanda ya shafeki na basa farinciki kafin ya ce Abunda yasa Baza a tafi Dake ba saboda su Akhbar Dole.saidai next year sannan kin yayesu kin Kuma haifamun wasu triple din"murmushi Zahra tayi tare da rufe fuska "Bayan su baba sundawo daga aikin hajji Wanda hada maman Asmy da babanta da bappa aka biyawa Zahra ta shirya domin taje tayi musu sannu da zuwa Sosai tayi mamakin Ganin yanda aka gyara gidansu da na su Asmy dakyal ta iya gane gidansu Dan har bene aka Dora musu Koda ta shiga ciki ma Saida tayi mamakin irin kayana alatun da aka zuba Baba ko hada kukan farinciki yake Yana godewa Allah na mallaka Masa Zahra a matsayin y'a itadai Zahra saidai tayi murmushi inda yayi Mata addu'a ta amsa da amen MD ko yasha ruwan addua Bayan ta huta gidansu dukda tayi mamakin rashin Ganin mama rabi a Gidan ta wuce gidansu Asmy nanma Tasha godiya da sa albarka Kukan farinciki ko maman su Asmy ta Shashi Bayan sun gama gaisawa Zahra tayi musu sannu da zuwa sai sannan ta samu Daman tambayar maman su Asmy ta ce mama Wai Ina mama rabi tunda nazo banganta ba "Girgiza Kai Mamansu Asmy tayi ta Ce "Ina ko zakiga rabi Ai tuni Malam ya saketa yaran Nan biyun dukansu sukayi ciki lokacin Yana batsari baisan wainar da ake toyawa ba Saida ya dawo Shima saidaga baya Anje cirewa Salamatu Cikin Rai yayi halin sa to kinsan dai maganar garin Nan magana ba boyuwa take ba asirinta ya tonu Wanda Malam ya saketa yace bazai iya Zama da ita ba "Salati Zahra tayi ta Ce "Wayyo Allah Salamatu ta mutu kenan bantaba sani ba Allah ya jikanta to Ina habibar ita ta haihu ne"Eh ta haihu d'an Wai ya mutu waya sani ma ko kashe shege sukayi"Sosai Zahra taji wani iri a ranta ta Ce "yanzu mama Suna wani Gida"Wama ya sane Mata Kullum Tana zarya Tana kuka Tana rokon Malam akan ya yafemata tayi nadama ya mayar da ita ya kiya yo me zaiyi da rabi matar da ta wulakantaki taso taga kin tozarta sai gashi kaikayi ya koma kan mashekiya Abu ya koma kan y'ay'anta shiyasa ba ason bin mutum da mugun nufi Shi shairi kwikuiyo ne Mai Shi yake dawowa"Sosai Zahra tayi sanyi ta ce "Mama Dan Allah tunda tayi nadama kusa Baki baba ya maida ita Dan Allah tunda tayi nadama kodan saboda su khairat Dan Allah mama "wani banzan kallo mama tayi Mata ta Ce "Amma bantaba sanin Baki da hankali ba Zahra sai yau matar da ta wulakantaki itace kike maganar ta dawo taci arzikinki ke wata irin zuciya ce Dake maimaikon kiyi farinciki mahaifin ki ya rabu da muguwar Mata shine kike kokarin ki Kara lakaba Masa"Ba Haka bane mama saboda su khairat za a duba"Barmun maganar Nan Zahra a Kama wata"da dare Zahra tajewa baba da maganar Akan ya mayar da mama rabi furtumarta yayi ya dinga Mata fada Akan Bata da hankali Sosai Zahra ta kafe hada kukanta Tana bawa baba hakuri akan Dan Allah ya dubi su khairat ya maidota idan ta sake wani abun saiya saketa dakyal ta samu ta shawo kan baba ya yarda Zai maidota Amma da sharadin saidai habiba ta koma wajen dangin babanta dan bazata shafawa ya'ayanshi kashin kaji ba ajiyar zuciya Zahra ta sauke ta ce ta yarda Koda baba ya maido mama rabi Bayan yayi Mata kashe sannan ya Dora da cewa arzikin Zahra ne taci harya maidota mama rabi kukan nadama hada durkusawa kamar zatayiwa Zahra sujjada Tana Mata godiya ta ce 'Har kunyar had'a Ido nake Dake Zahra ki yafemun irin zalincin da nadinga maki Shiyasa akace duk yanda ya rike Allah shiya rike Babban bango na tsaneki na tsangwameki naso ki wulakanta ki kaskanta saigashi Allah ya d'aukakaki d'aukakawar da bakowa Zai samu irinta ba Zahra a yanzu kina daya Daga Cikin macen da za ayi alfahari da ita a duniya ki yafemun Zahra nayi nadama har kunyar had'a Ido nake Dake gashinan muna Cikin cin arzikinki Shiyasa akace kaji tsoron mutumin daka wulakanta"Murmushi kawai Zahra tayi ta Ce "Allah yafe Mana tare mama"Kwana biyu Zahra tayi Wanda Cikin kwana Biyun mama rabi kamar ta goyata abinci ma saita tambayeta irin Wanda takeso Dan tunda mama rabi tasan cewar Zahra MD take aure ta sadakas tasan Zahra tayi daukakar da babu mahalukin da ya Isa yayi kasa da ita gwarama tayi hakuri ta dangwali arziki Rayuwar su Zahra na tafiya yanda ya kamata a Haka har lokacin bikinsu Chuchu ya gabato anfara shiryen shirye ta ko Ina Bangaren Zahra da MD ma Sosai suke Shirin bikinnan a Haka har lokacin bikinsu yayi Zahra hankalinta duk ya kasu biyu ga Gidan ammy Bangaren chuchu ga chan funtua Bangaren Asmy tunda aka Fara bikin take Shan gayu da wankan gwala_gwalai Sosai suke Shan masifar kyau ita da yaranta da suka Fara tafiya gwanin sha'awa duk inda suka gitta sai anyi sha'awarsu ana gobe daurin aure ta samu damar zuwa funtuaa Wanda motoci takwas sukayi Mata rakiya tare da security yanda kasan matar shugaban kasa ita kanta Zahra ta kalli wanna daukakar da Allah yayi Mata har hawayen farinciki take Wai itace Zahra da da ba abakin komai take ba yanzu ta daukaku har Haka Koda ta Isa Unguwarsu duk manyan motocin sun cika wajen kowa sai daukin su gaisa da ita ake Saida ta gaishe da tsaffin layinsu Bayan tayi musu alkhairi kafin ta shiga gidansu Asmy dakyal ta samu ta shawo kan mutuniyar Tata Akan tayi fushi sai yanzu take zuwa dakyal ta fahimta bayaninta na cewar hidimar gidansu mijintace ta hanata sakat Yauma dakyal suka barta ta taho Nan aka cigaba da shagali da Zahra da dare gidansu taje Dan ta kwana zo kuga murna wajen mama rabi Kira ta ce "lale marhaban ga y'ar arzikin tazo Yar albarka sannu da zuwa jikokina sannunku ta fada Tana yin sama da little itadai Zahra murmushi kawai take Bayan ta Gaisheta Nan khairat ta ruga da gudu Tana murnar Ganin Yar uwartata Haka safiya da yanzu itama ta Zama budurwa Mama rabi kusan raba dare tayi tana goye da little dakyal Zahra ta samu ta saukota Tana mama zata gajiyar Dake Kira take ba komai Yar Nan barni in Goya abuna washegari aka daura Auren *Jabir & Asmy* tare da *Chuchu & Adil* na Asmy a funtua aka daura na chuchu Kuma a kd kasancewar an hade dinner ya Sanya aka Kai amarya da wuri Gidan ammy aka sauketa karfe goma na dare aka Tafi dinner Wanda Zahra da MD su suka shirya dinner Sosai wajen yayi masifar kyau da tsaruwa amarenma sunyi anko suma angwayen sunsha kyau iyayen gayya kuwa MD da Zahra ba a magana sunyi masifar kyau duk inda suke suna like da juna Excord dinsu na take musu baya tare da yaransu Dake tsalle tsallensu gwanin ban burgewa Sosai cemarori ke yawo Akan Zahra da MD yanda kasan sune amaren Zahra ko an kame girma ana zaune ita ta bada tarihin amaren MD Kuma ya nada na angwayen taro ya tashi Lafiya washegari aka wuce da kowacce gidanta chuchu Abuja Asmy Kuma Nan kd grab Dan gida daya ne tsakanin gidanta da Zahra..