← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 129

Sashe 75

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sati Ukku fa baba"ta fada idonta na cikowa da k'walla " eh sati Ukku muka tsaida saboda shekara hud'u ba wasa ba munriga munshirya komai na biki da kayan daki tuni na tanada komai Saidai jiran rana Kina da matsala ne da hakan"Goge hawayen tayi ta ce"a a a Baba naga yayi kusa ne"Murmushin dattaku Baba yayi ya ce "baiyi kusa ba Zarah Iyayen yaron sun nuna yana son ne ayi abun wurwuri shiyasanya muka barshi a haka din " kasa tayi da kanta saida Baba ya k'ara mata nasihohi sosai kafin ya bata umarnin fita Zarah kamar jira take yace ta fita tana zuwa d'akinta tayi rubda ciki ta fashe da kuka Cikin kuka take cewa "Na shiga ukku ya zanyi da rayuwata taya ina musulmai zan yarda A daura mun Aure Bayan akwai Auren wani a kaina sannan ba idda ba komai ka cuceni Musty tsakanina dakai Sai Allah ya isa mugu azzalumi" Sosai take kuka Daren ranar bacci sai barawo ne ya d'auke ta washegari koda ta tashi da ciwon kai ta tashi saboda kukan da tasha Bayan tayi wanka d'akinta ta koma Dan yanzu kwata kwata zaman gidansu baya mata dadi Khairat ce Daman Suke Dan Hira da ita gashi itama Bata gidan bare Safiya yunwa takeji Amma tashin hankalin da take ciki tasa ta manta da abinci sosai ta Lula duniyar tunani "tana cikin wannan tunanin Asmy ta shigo saida ta daddabata tasan da zuwanta Firgit tayi ta mik'e tare da kallonta da Itamadin ita take kallo a sanyaye Asmy ta ce " Kinji Sati ukku aka sanya Aurenki da Hafiz yanzu nakeji wajen Mama"Naji"zarah ta fad'a kamar zata fashe da kuka "Tagumi Asmy tayi tare da lulawa duniyar tunani Wanda itama Zarah tagumin tayi Sunkai minti goma ba Wanda yayi magana kafin Asmy ta ce " nayi Danasanin *Auren wata taran* wannan da Akayi Zarah Bacci da idona jiya ya gagareni nasan duk ni na ja maki wannan tashin hankalin ji nake inama akaina wannan Abun ya faru bake ba Zarah akwai babbar matsala Bazaiyu ayi Auren nan ba muddin bai sakeki ba sannan koya sakeki dole saikinyi idda "murmushin da yafi kuka ciwo Zarah tayi Dan yanzu idanunta sun fara k'afewa da kukan ta ce " Hmmmm"Hawaye na sauka daga idon Asmy ta kamo hannunta ta ce "Dan Allah Zarah ki yafemun da nazama silar shigarki wannan hatsarin wlh tallahi da nasan haka zata faru da ko makamanciyar haka bazaiyu ba A lokacin sonki da tsoron rasaki ya sanya harna amince da Auren nan bansan abun nan zai zama Haka ba Zarah na cuceki naci Amanar.....rufe mata baki Zarah itama hawayen take ta ce " Kidaina cewa haka Asmy wlh ban rik'e ki da komai a zuciya ba na d'auki hakan a matsayin kaddarata kidaina cewa haka Wannan din ya zama sirri a tsakanin nidake karmu sake wani yaji labarin nan Asmy mun tafka Babban kuskure duk laifi na ne "Ba laifinki bane Zarah laifi nane yanzu menene mafita kwana nayi ina tunanin mafitar da zamu samu Amma kaina ya kulle" Bamuda mafitar da ta wuce Addua Komai ya Riga ya lalace Mafitarmu d'aya Allah shi kadai zamuyi ta roka Dan ba abunda yafi karfinsa shine kawai zai kawo mana mafita"cewar Zarah "wayarta ce tayi ringing kamar bazata dauka ba saita d'auka tana ganin Hafiz ne saida gabanta ya fad'i saida ta kusa gama ringing tukwana ta d'auka tana daidaita muryarta karya gane tana kuka " A sanyaye ta gaishesa ya amsa cikin so kauda tare da shaida mata yana k'ofar gidansu"ina zuwa"ta basa amsa tare da katse kiran kallon Asmy tayi ta ce "Hafiz ne yazo" Okay gyara fuskarki mu fita tare daman Mama tace mutaho tare saina wuce gida idan kin sallamesa kije gida Mama na nemanki"To"Zarah ta fad'a tare da mik'ewa saida ta wanko fuskarta kafin ta dawo ta sanya k'atuwar hijab d'inta Tare suka fita da Asmy Bayan Asmy ta gaishe da Hafiz tana shirin barin wajen ya ce "a a dawo babbar kawar Amarya ai wannan zuwan Naku ne ku biyu Naga Amaryar tawa bata shirya ba har yanzu gwara mu mu fara shirin karmu biya tata" murmushi Asmy tayi ta ce "Hakane kam" Zarah ko bata tanka ba saboda wani iri da take ji"Mota Hafiz ya shiga Ya d'auko invitation masu yawa mik'awa Asmy yayi ya ce "gashi Dan ku fara rabo da wuri" Saida Asmy ta wara idanu kafin tayi Dariya ta Ce"lallai ango wannan zumudi haka invitation da wuri to shikenan"murmushi yayi ya ce "Ai dole nayi zumudi kam Abun shekara hud'u ya rage sati Ukku ina zama ya ganni" hakane kam to Allah ga kaimu "Ameeen Sai Maganar event ko walima da kukeso Kuyi duk abunda kuke buk'ata ki rubuta gobe idan nazo saina amsa" To shikenan ranka ya dad'e"Asmy ta fad'a"Bayan barinta wajen sai sannan ya maida Kallonshi ga Zarah da tayi kasa da kanta cike da kulawa ya ce "Yadai my wife lfy?lafiya qlau ya Hafiz Ina kwana" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Alhamdulilla an kammala sch lafiya ko to Allah ya taimaka jiya din naso zuwa wlh Wani kiran gaggawa ne akamun katsina shi ya hanani zuwa am sorry Kyautarki tana gida na mance da ita " murmushi ta kirkira ta ce "Ba komai Ai " Duk yanda Hafiz yake yiwa Zarah Hira kin sakin jiki tayi dashi Ganin hakan yasa ya tafi saita d'auka ko kunyarsa ce takeji Dan ya Santa akwai kunya Koda ta shiga gidansu Asmy Bayan ta gaishe da mamansu nan ta zaunar da ita ta fara bata magunguna Wanda tunda ta bata Zarah ta fahimci na meye ba ason ranta ba ta fara sha sai Dan batason yi mata musu Bayan nan ta d'ora tayi mata dilka ta amare sosai ita kanta tayi mamakin karuwar sanyin na Zarah Saita lak'anta hakan da Bikinta dake karasowa tundaga ranar kullum Zarah tana gidan su Asmy mamansu tana yi mata Dilka da magungunan gyara bangaren Mama Rabi ko Sosai Zarah tayi mamakin yanzu wani mutunci da take mata ba zagi ba komai har tana mata maganar shirye shiryen biki itama ta bata invitation tayi tata gayyatar ranar Zarah sossai mamaki ya cika ta Nan ta d'auko invitation din da chungum din da ya kawo mata daga baya ta bata tana mamakin wannan saukowar mutuncin na Mama Rabi na lokaci guda bangaren Baba ma sosai yayi mamakin yanda take nan nan da bikin kamar za ayi bikin diyarta a tunaninshi Zatayi bakin cikin kayan d'akin da akayiwa Zarah saiyaga itace mai cewa ma a k'ara wani abun ayi Abu na fita kunya sosai a ransa yaji dadin sauyawar tata har yana murnar kila yanxu ta sauya hali. <Abuja> Kallo d'aya zakayi masa ka lura yana cikin tsananin damuwa har wata rama yayi idonshi lumshe kamar mai bacci nanko tunani ne chunkushe a ransa Ya Lula duniyar tunani yaji wayarsa tayi ringing saida tagama ringing bai daga ba wani kiran ya k'ara shigowa kamar bazai duba ba saikuma ya janyo wayar a hankali tare da Kallon screen din wayar Ganin number Ammy ce ya sanyashi saurin picking a sanyaye ya gaishe ta ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da cewa "kana ina?Ina Abuja " Okay to kazo Hajiya na nemanka "yana kwance baisan lokacin ya Mike zaune ba a matuk'ar makance ya ce " Hajiya kuma Ammy tazo garin ne?Eh tazo tun jiya kuma tace kome kake karka wuce gobe bakazoba"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un "ya shiga maimaitawa a cikin zuciyarsa Ammy bata jira amsarsaba ta kashe wayarsa dafe kansa dake tsananin sara masa yayi ya ce " Oh my god"Ya Hajiya takeso nayi da rayuwata ne Wai,dalilinta na shiga halin da nake ciki yanzu kuma ta k'ara zuwa ta k'ara jagula lissafi cikin Sauri ya lalubo number Amera ringing biyu ta d'auka "bai saurari abunda take cewa ba ya ce " kome kike kiyi gaggawar dawowa gida kafin nan kafin 12:na ranar gobe "Daga bangaren Amera ta ce " Subhanalla honey lafiya"Lafiya nadai fad'a maki ki baro k'asar nan "Saboda me honey wlh gobe ake fara bikin Chichilayo" MD ji yayi kamar ya shak'eta da wayar baisan lokacin da yace "uwar bikin chichilayo Dan Iskanci ina Miki maganar Serious zaki sakomun maganar wata tsinanniyar arniya ki zauna karkizo ki saurari abunda zai faru kishiyar da bakiso ita zaki tarar"Daga bangaren Amera wani irin bugawar zuciya taji batasan lokacin da ta fashe da kuka ba Ta ce " nashiga Ukku ni Sadiya me kake nufi honey bangane yaren naka ba "Tsaki yaja ya ce " ki sameni a Abuja gidana Dake life camp buzu quarters Hajiya tazo kuma kinfi kowa sanin zuwanta"yana gama fad'ar haka ya katse kiran yana jan tsaki Sosai yakejin haushin kansa da na kowama yanzu ta ina zan nemo yarinyar nan?ya tambayi kansa "lumshe ido yana tuno da Dadin yarinyar lokaci guda mood dinsa ya sauya dak'yal ya iya hada ruwan tea tare da matsa lemon tsami kusan goma Dan tun Bayan rabuwarsa da ita kullum saiya sha sa yake iya samun bacci ga tunaninta da yaki barin kwalwarsa daidai da second guda washegari tun karfe shida na safe MD yaji bugawar part din da yake tundaga bedroom dinsa yajiyo saboda wani irin knoking da ake da karfi jallabiyarsa ya zura tare da fitowa palourn yana bud'ewa yaci karo da Amera kallo d'aya yayi mata yasan a matuk'ar firgice take ga idanunta da sukayi ja jawur Fadowa jikinshi tayi tare da fashewa da wani irin kuka mai tsananin gaske sosai take kuka kamar ranta zai fita Wanda MD Jin kuka nata yake har cikin ransa sosai ya tausaya mata wannan nadaga cikin abunda yasa ake ganin kamar Amera ta gama dashi Bayason ganinta cikin wannan halin hakan yasa ko maganar Karin Aure bayaso Daddab'a bayanta yafara cikin sigar lallashi Dak'yal ya samu har suka k'arasa palourn Inda ya zaunar da ita Cikin kuka ta ce " Honey karkaga tashin hankalin Dana shiga ban iya bacci ba Jiya da Daren da ka kirani na tafi Airport Sai 1am jirginmu ya tashi dak'yal na iya kawo kaina nan honey mutuwa zanyi a kanka "Numfashi mai zafi MD ya fesar kafin ya d'ago ya Kalleta ya ce " kibar kukan nan bashi da amfani kalleni muyi magana ta
Chapter 75 · 0% Book details