Sashe 112
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
da dinkinta Tana shirin kurma ihu ya had'e bakinsu waje Daya ya d'auki lokaci sosai yana kissing d'inta Kamar zai cinyeta lokaci guda yaji ya fara fita daga hayyacinsa baisan lokacin d'aya sanya hannunsa cikin rigarta ba ya fara wasa da ...... kamar zai cinyeta zahra gabak'i d'aya bata yanda zata kwaci kanta ga ya had'e bakinsu waje Daya Sarautar Allah kawai tasawa ido Dan bata da damar kurma masa ihu gaba d'aya MD ya rikice har baiji kukan da Amar ya fara ba Alamun ya tashi zahra ko Naji ta fara kokarin ya saketa amma ta kasa chuchu daga palourn da take ta dinga jiyo kukan Amar shataf ta manta da MD.na d'akin da gudu ta Ruga d'akin abunda ta gani ne ya sanyata yin Sauri tayi baya ba shiri tana dafe k'irji tace"na shiga ukku ni maryam me.na ganoma.idona"Zaune tayi tana tagumin tunanin yanda zahra ta biyewa Yayan nata murmushi tayi Ita d'aya ta ce "Allah sarki babu yanda banso zahra da yaya na ba ashe Allah ya Riga da ya tsara itace matarsa hadda y'ay'a ita kanta ta tuna abun nan al'ajabi take sai ta tuna lokacin da take cewa su Asmy.kilama ita d'in rabon yaya ce Ashe dai rabonshi d'ince...saida Little itama ta tsala nata kukan kasancewar na yara biyu ya dawo da MD hankalinshi cikin Sauri ya tashi a kanta Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da sauke numfashi Cikin Sauri MD ya d'auki little ta dauki amar jijjigashi ta fara shima MD na jijjigashi ganin bata da shirin feeding dinsa ya sanya MD cewa " ki basa abincinsa bakijin irin kukan da yake"Kauda kai tayi tana turo baki gaba tayi ta ce "Dan Allah Malam ka fita Haba" murmushi yayi ya ce "Ko kunyata kike Bayan yanzu na gama liliy...batajira abunda zaice ba tayi Sauri ta bar dakin cike da jin kunya da haushin Rashin junyarsa palourn ta koma gefen Chuchu ta zauna tana turo baki Chuchu na kallon yanda ta fito a murtuke saida tasoyin Dariya ta Had'iye MD ko murmushi yayi tare da jijjigar y'arsa kafin ya d'auki akhbar dake bacci Duka ya sanyasu a kafada ya fito Chuchu ya mik'awa shi ya ce " ku daina barmun yara su kadai a d'aki ko nan da nan ne"Murmushi Chuchu tayi tace "Daman bama barinsu yaya " satar kallon Zahra yayi da ta wani had'e rai yayi murmushi ya wuce da little kasa...tundaga lokacin nan MD ya samu damar zuwa ya rage zafi da zahra Chuchu ko tuni ta ganesa Dan d'aya shigo d'akin yake cewa ta basu waje ganin haka ya sanya data gansa take ficewama ta basu waje Zahra ko Dan dole yake mata Dan ba irin yanda batayi dashi akan ya daina zuwa Wajenta ita bataso idan yaranshine Ya dinga kiran Chuchu tana Kai masa su A haka dai har zahra ta kusa yin arba'in Yau ma MD yazo Chuchu ta fice tana palour ita da Amar da Alkhbar da suke kan gadonsu na kwanciya tana yi musu wasa suna mata dariyar koda Ammy ta shigo d'akin rik'e da little dake Tsala kuka Chuchu na ganinta ta ce "Ammy kuka take" Eh kuka take ai tamayi hakuri rabonta da mamanta tun safe fa "bari na kai mata ita" ta fad'a tana nufar kofar chuhu na ganin haka tayi Sauri ta shige gaban Ammy Dukta rude ta ce "Am my bari na kai mata ita" Harararta Ammy tayi ta ce "Da Allah bani waje bansan shiririta D'akin naku bako na ne " ta fad'a tana tura kofar kusan daskarewa tayi ganin MD kan zahra sai kissing d'inta yake Saurin rumtse ido tayi kafin Ta daka masa wata irin Tsawa wadda ba shiri MD Ya tashi a kanta Sosai ya rud'e ganin Ammy baiyi tsammaniba zahra ko wace irin kunya ce ta lullubeta tasan Ammy bazata fahimceta Ba ason ranta yake mata haka ba Dan ba yanda zatayi"Cikin Tsawa Ammy ta ce "Wuce ka bar dakin nan munafiki" sim sim MD yabar dakin cike da jin kunya Zahra ko kunya ta isheta saita fashe da kuka "Cikin fad'a Ammy ta ce " Watau ni ina Chan ina kwata miki hakkinki ke.kina nan kinbiye masa Ina tibka kina warwarewa kin mayarmun da aiki baya zahra me.yasa kika saki jiki dashi haka bakison yasan darajarki da martabarki yagane matsayi da muhimmancinki zahra "Cikin kuka zahra ta ce " Dan Allah Ammy kiyi hakuri nima banason yana zuwa kuma ki tambayi Chuchu kiji "tab'a hannu Ammy tayi ta ce " kenanma wannan bashine karo na farko ba kafin ta dallawa Chuchu harara ta ce "Ke kuma Munafuka watau duk hudubar da nayi maki akan karki sake ki barsa yana zuwa Wajenta bakiji ba to ai shikenan gaba d'aya yau zata koma part Dina sai Inga in d'akin nau zai dinga binta " Dariya Chuchu tayi ta ce "Ammy ni karkiga Laifina Miji da matarsa kuma saina hanasa shigowa" Dundu a baya Ammy takai mata ta ce "ja'ira" Dariya Chuchu tayi tana kaucewa ..tundaga ranar Ammy ta mayar da zahra part d'inta ta kasa ta tsare sosai akan MD ko Yaransa Saidai taba Chuchu takai masa sosai MD ya damu da hakan hankalinshi ya k'ara tashi Dan koba komai yana da buk'atar ganin matarshi sosai Ammy ta burkuta masa lissafi gabak'i d'aya ...yana kwance a makeken Royal bed dinsa kamar koyaushe indai ya kwanta shi d'aya to ba tunanin da yake idan ba nata ba yaji wayarsa tayi ringing kamar bazai daga ba saikuma ya d'auka ganin Baba na gombe ne Cikin girmamawa MD ya gaishesa ya amsa masa ya ce "jikana ashe haihuwa akayi maka baka fadamunba Abun farinciki ya samu ashe har anyi wata guda bani da labari sai dazu Jabir Daya kirani muka gaisa yake fad'amun gsky banji dadi da baka fadamunba kasan ai nazo naga y'ay'an nawa amma dukda haka insha Allah na shirya gobe gani nan zuwa kadunar zanzo nayi maka barka naga yaran kaga harmun gaisa da Hajiya sannan nayi mata Godiya"Cikin girmamawa MD ya ce " ba haka bane Baba lokacin wani uzurine ya mantar dani fad'a maka ai Baba dama ka barsa karka wahalar da jikinka idan sukayi kwari a kawoma maka su kaga jikin naka bai gama warwarewa ba"murmushi yayi ya ce "a a jikana jiki kuma ai ya warware gobe insha Allah Zanzo naga y'ay'an tunda tafadamun haihuwar Naji ina son ganin Yaran " cike da murmushi MD.ya ce "To shikenan Baba gobe da safe driver zaizo ya tafi dakai saika biyoshi zai kawoka har gida " haka ko akayi washegari tunda safe driver yaje ya taho da Baba na gombe da Yakejin gabanshi na fad'uwa tunda suka taho suna isowa garin Kaduna Baba ya dinga bin garin da Kallo yana murmushi Har suka isa tafkeken gidan su MD Daman tun jiyan MD.ya sanar da Ammy da zuwan Baba anshirya masa komai na tarba a Babban palourn bak'i aka saukesa Bayan an cika masa gabansa da abubuwan makuleshe sosai MD ya nuna jin dadinsa na zuwan Baba Bayan Ammy ta shigo tana rik'e da Amar Hannunta da fara'a tayi welcoming din Baba cikin girmamawa tamkar mahaifinta haka ta dinga girmamasa Bayan sun gaisa Baba ya k'ara yiwa Ammy Godiya akan irin taimakon da MD yayi masa murmushi Ammy tayi ta ce "Bakomai Baba Ai anzama daya kaid'in ai tamkar uba kake a gareni shiko jika ne a gareka" fara'a cike da fuskar Baba ya ce "na jima banga mutanen kirki mutane na kwarai ba irinku ba Allah dai yasa a gama da duniya lafiya ya kareku daga sharrin makiya ya raya zuri'a Ameen Ammy ta fad'a tana mik'awa Baba Amar ta ce " Ga d'iyan naka Baba Biyun yanzu za a kawo maka ana shiryasu"Murmushi Baba yayi yana amsar yaron Ya ce "kai kai masha Allah Tubarakalla Allah ubangiji ya raya ya karesu daga sharrin makiya " shidai MD yana mamakin Baba tsoho da duk addu'ar da zaiyi ko waya suke saiya ambaci makiya da mahassada "Kallon yaron kawai Baba yake yanajin k'aunar yaron haka kawai yakeganin yaron tamkar ya rik'e jininsa Chuchu ce tare da zahra suka shigo tana sanye cikin zullubebiyar hijab har kasa ita na rik'e da Akhbar Chuchu kuma little gefen Ammy Zahra ta zauna Hakanan yau ta tashi a sanyaye kallon ta kawai MD yake tunda ta shigo sosai yaga ta k'ara yi masa kyau da kwarjini baisan lokacin d'aya saki kasaitaccen murmushi ba tare da sauke ajiyar zuciya Dagowar da Baba zaiyi daga Kallon Amar idonsa ya sauka akan zahra dake mik'awa Ammy akhbar Ammy ta ce " To Baba ga sauran an kawo maka kaga maman yaran"ta fad'a tana nuna masa Zahra"A matuk'ar firgice Baba ya Mike Hankali tashe yake kallon zahra yana rik'e da Amar ya fara nunata da yatsa kasa magana yayi sai nuna ta da yatsa da yadingayi muryarsa gaba d'aya ta sartsa ya kasa furta abunda yakeson fad'a duk Kallon mamaki suke binshi dashi har zahra da ita yauma ta fara ganinsa Rumtse idonsa yayi da karfi kafin ya bud'e yana nunata da yatsa a rarrabe ya ce "Ma my y'a ta Zahra'u da man kina raye ba ki mutu ba Zahra'u kece nake gani ko ko mafarki ne nake........✍🏽