← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 129

Sashe 50

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

iya d'ora icloud " kin rik'e password dinne"gyada mishi kai tayi ta ce "Eh log out kawai za ayi kuma banga wajenba " Okay kawo "zuwa tayi zata mik'a mai ya zaunar da ita gefenshi kugunsu waje Daya amsar wayar yayi tare da cewa " ki Kalla yanda ake ",,Tana Kallonshi ya shiga ta karantomai password dandanan ya hau komai d'inta ya dawo hamdala tayi ta ce " Alhmdllh kaga ban rasa komai nau ba hatta hotuna na sundawo "Murmushi yayi mata ya ce " Ai daman bazasu bace ba sannan na bada a gyaro maki wayarki gobe za a gyara "girgiza kai tayi ta ce " a a bama sai angyara ba Tunda komai ya dawo"watau kinyi sabuwar taya kenan shysa zakice kar agyaru"Y'ar Dariya tayi batace kome ba "kwantota yayi jikinshi tare da cire Dan kwalin dake kanta bakin gashinta mai matsakaicin tsawo da yasha gyara ya bayyana ga k'amshin mai dake tashi a hankali ya fara wasa da gashin itadai Zarah shiru tayi bata iya hanashi ba daga nan ya fara mata wasu irin abubuwan da ya saba ganin zai zarce ne kuma zai tada mata feeling ya sanyata marairaicewa ta ce " ka bari Dan Allah perioud nake"Sassautawa yayi Dan har a ranshi yaso yau ya Dana ya ce "Yaushe kika fara" d'azu ta fad'a cike da jin kunya"Kwana nawa kike gamawa"4 zuwa 5" ta fad'a cike da kosawa da tambayar a hankali Zarah ta zame jikinta daga nashi tare da mik'ewa ta ce "Good night" Okay Have a nice dream"ya fad'a yana lumshe ido tana zuwa wayarta ta jona charge ta kwanta tana lumshe ido harga Allah taji dad'in wayar daya bata sosai a ranta ta ce "Allahsrk rayuwa wai Zarah nice zan rik'e wannan wayar mai tsada" saikuma tabar wannan tunanin ta koma tunanin irin wahalar da take sha lokacin period a baya amma yanxu wai itace yanzu hankali kwance take perioud harta gama bako wani ciwon ciki...satin md guda a Zaria sosai yaji dadin zaman nan saboda ko ba komai yana hutawa sannan ya kashe wayoyinshi bare ko harkar business a dameshi Amera ma ba samunshi take ba dukda yace mata daman zai kashe wayoyinsa hakan yasa bai damu da halin da zata shiga ba saboda ya sanar mata zaman nashi anan sosai ya samu Hutu biyu gana moruwa da yake da Zarah gana hutawa ba Aikin da yake sosai yayi kyau cikin shigar da ya saba watau ta K'ananan kaya banda k'amshi ba abunda ke tashi daga gareshi cikin murna Zarah ta fito daga bedroom d'in sanye cikin lafcececiyar Hijab d'inta har k'asa wayarta ce kawai a hannunta Tare suka shiga baya Inda driver yashiga gaba ya jasu Har suka isa A B U bamai magana Zarah sai doki take Suna isa har ciki suka kaita inta da zata fita Ya damk'a mata Rafar y'an dubu dubu a hannu yi tayi kamar zata amsa sai tayi Sauri ta fita tana Dariya ta ce "Sai anjima " Girgiza kai MD yayi tare da mayar da kud'in ma ajinsu kai tsaye KD driver ya wuce dashi koda yaje bai samu Amera gida ba Bayan ya bud'e wayarsa ya kirata yake shaida mata ya dawo cikin murna ta ce "Gani nan honey daman gida naje kafin ka dawo" Gidan Ammy yaje suka gaisa kafin da magriba ya koma gidanshi yana zuwa ya samu Amera da gudu Tayi hug dinsa tana murnar ganinsa Saidaifa duk murnar a baki ne Dan ko ruwan Tarbar miji yayi tafiya bata kawo masa Inda sabo MD ya saba Dan in zaiyi tafiyar wata nawa indai zai dawo ko ruwa bata tarar shi dashi bare akai ga abinci da ko dahuwar indomie bata iya ba Saidai idan yace ta d'auko masa ruwa take d'auko masa...Sosai Zarah suka maida hankalinsu ga jarabawar da suke Kasancewar sun fara exams hankalinta gaba d'aya ta maidashi ga karatu a haka har suka gama Exams dinsu ta first semester Level 4 Inda zasuyi hutun wata biyu da sun dawo wata hud'u ya rage musu suyi final Exams koda suka isa gida gidan su Asmy ta fara sauka Bayan sun gaisa tadan huta ta wuce nasu gidan Dan daman tasan Baba na wajen aikinshi hakan yasa ta fara zuwa gidan su Asmy tana shiga da Sallama a bakinta ta shiga Mama Rabi da ke kan Kujera tana jin radio ta mik'e ta ce "Iyye Andawo daga yawon katuwancin kenan Ai muna nan dai muna jiran uhum Dan wlh rana d'aya ta barawo rana d'aya tame kaya Waye bai sani iskancin da kuke a jami'ar ba za Adawo ana mana wani bagu waike ishashiya mai Ilimi kin shiga jami'a ko to dad'in abun ansan komai dai ehe karshen dai alawa kasa karshen iskanci dai a d'auko cutar Sida ko kuma cikin shege Dan allurorinma da kuke idan Allah ya tashi tona muku asiri ba aiki suke ba......✍🏿
Chapter 50 · 0% Book details