Sashe 94
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da isarsu asibiti ma emergency aka wuce da ita idan hankalin MD yayi dubu a tashe yake zirga zirga kawai yake yana cikin wannan tashin hankalin wayarsa tayi ringing baima duba mai kiran ba ya daga daga dayan bangaren amera ta ce"Hello honey ykk daman zan fad'a maka ne gobe zanyi tafiya Dubai dan wlh jina nake kamar a k'aya k'asar nan dan karkaji na tafi"md ji yayi kamar ya shakota ta cikin wayar ya wanke ta da mari ba karamun haushi ta basa ba cikin bacin rai ya ce "Ba london ba kitafi bangon duniya stupid mahaukaciya kawai kije gaba da bangon duniya " baijira amsarta ba ya katse kiran yanajan tsaki shi yana cikin wannan babban tashin hankalin wanda duk silarta hakan ya faru ita tana ma masa zancen tafiya wata kasa baimasan ya zage ta ba ,babban Dr d'in mai asibitin kanshi kasancewar da kansa ya shiga duba ta tare da taimakon nurse saida yayi awa Ukku a ciki kafin ya fito yana shafce zufa da Sauri MD ya taresa ya ce "ya ake ciki dr tana lafiya Kardai kace mun abunda ke cikin ta ya zube" Calm down ranka ya dad'e Babu abunda ya samu abin cikin ta Gaskiya kayi Namijin kokari da kukazo da wuri asibiti Dan da aka kai wani lokaci Abinda ke cikin ta zai fita ita kanta zata wahala sosai Dan dak'yal da taimakon Allah yasa Muka ceci cikin daga zubewa Amma yanzu alhmdllh cikin iko na ubangiji Munyi aiki da kwarewa har muka tsaidar da jinin sannan muka yi control d'in matsalar dake shirin faruwa Amma Gaskiya next ka kula sosai Dan Abu Kad'an ba fata ba Zai iya Affecting cikin ayi asararsa sannan ta dinga cin abinci please "nauyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke Jin cikin bai zube ya ce " Thank you so much Dr itafa ya jikin nata"Alhmdllh da sauki amma zata kwana biyu kafin a sallameta saboda ta k'ara warwarewa yanzu munsanya mata Karin ruwa tana bacci ne "Okay Zan iya samu na ganta" ba matsala ranka ya dad'e "Dr din ya fad'a yana masa nuni Dan kallo d'aya yayi masa ya ganesa saboda suna cin karo da hotonsa a Internet sannan MD ba boyayyan mutum bane dukda yayi mamakin Kawo yarinyar da yayi Saiya d'auka matarsa ce tunda bakowa yasanta ba " Bayan shigar md d'akin da zahra take kan kujer dake gaban gadon ya zauna kallonta ya shigayi ba kakkautawa kwance take tana bacci hankali kwance Fuskarnan tata tayi fayau yanayin yanda take baccin sosai ya basa sha'awa a hankali ya kamo hannunta mai d'auke da bakin lalle da ratsin ja sosai lallen yayi masa.kyau Kallon lallen ya shigayi ba kakkautawa yana Dan shafa lallausan hannunta a hankali A rayuwar MD yanason yaga matarsa na masa lalle wayarsa ce tayi ringing ganin jaber ne yasanyashi saurin picking Daga bangaren jaber ya ce "Yadai najiki kamar baka cikin yanayi mai dadi"da sauki ya fad'a yana matsawa daga Inda take ya ce " ya ake ciki kaje asibitin?Eh naje komai ya tafi yanda akeso kuma sun bada Had'in kai Sunji dadi sosai da taimakon sannan munyi magana da Dr d'in a jiya ma ina Chan yace Zuciyarsa ke ke shirin kamuwa da ciwo amma idan aka tallabi abun da wuri bazai kamu ba "Innalillahi MD ya maimaita a ransa duk shi yayi sanadin shigar mahaifinta wannan halin kafin ya ce " Dan Allah Jabir kamun kokari duk yanda za ayi ayi kar wani Abu ya samu mahaifinta muddin wani Abu ya samesa bazan tab'a yafewa kaina ba duk yanda za ayi ayi chuku_chukun da za ayi kafin gobe a fitar dashi daga kasarnan na shirya kashe ko nawa ne wajen nema masa lafiya"insha Allahu babu abunda zai samesa amma ga shawara mezai hana a jaraba akwai wata Dr Najmat Kwararrar likitan zuciya ce har daga kasashe kawo masa patient ake Inma anfitar dashi wajen tofa abunda zatayi zai iyafin ma na Chan din saboda itama gwanace har Asibiti gareta a India a Gaskiya indai muka sameta tofa insha Allahu za a dace "cikin Sauri MD yace " To yaza ayi a sameta cikin Sauri kar wani Abu ya kuma samunsa sannan wani gari ne take "a nan kaduna itama take gidansu shima cikin GRA yake babu matsala insha Allahu saboda akwai abokin mijinta Habib to Abokina ne kuma matarsa Amera Y'ar uwar ita Dr najmat d'ince yanzu insha Allah zankira Habib din zanje har gidansa ta hanyar amerar zata hadamu da Najmat d'in Insha Allahu" (Only najmat abiy fans can related😝masu buk'atar cmplt book din *Najmat Abiy* su tuntub'eni akan wannan number 07026166536 Na Batin ne😝)Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce "Nagode Jabir komai Kenan ka sameni a waya zan maka transfer kudi kome ya kamata ayi sannan Dan Allah ka sayi kayan abinci da komai na Buk'ata ka kai gidansu ka d'ora musu da isassun kudi kayi abunda koda ina nan haka zanyi Dan Allah" Bayan sun gama wayar kujerar da yake ya koma ya kafeta da idanu kamar zai cinyeta yana jiran farkawarta da akayi Sallar Azahar yaje yayi salla d'aya daga cikin restaurant dinsa ya kira drivern sa akan yaje ya amso abinci Bayan ya fad'a masa asibitin d'akin da take ya koma kafin 1hour drivern ya kira number d'akin ya fad'a masa Akan idan yazo yayu knoking karya shigo haka ko akayi yana zuwa yayi knoking MD yafita ya amso warmers din yazo ya Aje sai wajen la'asr zahra ta farka dak'yal ta iya bud'e idanunta saboda wani irin nauyi da sukayi mata Ga jikinta da duk yayi tsami takejin ko tashi bazata iya ba MD yana lura da tashinta Ajiyar zuciya ya sauke suna hada ido hud'u zahra ji tayi kamar ta kashesa saboda a halin yanzu ba Wanda ta tsana sama da mutumin nan da yayi silar rugujewar farincikinta Dana mahaifinta "MD na shirin tab'ata cikin b'acin rai Ta ce " karka sake hannunka ya tabani"Kamar Wanda aka tsaida haka MD yayi dukda yaji ciwon abunda tayi masa Telephone din dake d'akin ya d'auka tare da kiran Dr din akan yazo ya duba ta ta tashi ba dau lokaci ba likitan yazo Nan yashiga tambayarta irin yanda takeji tana basa amsa a takaice Dan duk haushin kowa takeji "y'an rubuce rubuce dr yayi a paper tare da mik'awa MD ya ce " gashi a saya wannan magungunan ta fara sha daga yanzu amma kafin nan a tabbatar taci abinci "kin amsar paper MD yayi ya ce "a saya a pharmacy din asibitin bani acco no dinka zanmaka transfer kudin"take MD yayiwa dr din transfer kudi masu yawa dukda Dr baiyi mamakin hakan ba Dan MD zaiyi fiye da haka ba dukda asibitin mai mugun tsadane dan kwana daya ma kudin gado kaji kudin saikayi mamaki amma saida ya ninka kudin sau hud'u dr din na shirin taba hannun zahra dan ya cire mata karin ruwan da ya kare md ya daga masa hannu yace " kaje zancire mata"okay dr din ya fada tare da yin hanyar fita zahra ta ce " Dan Allah Dr cikin ya fita"Murmushi yayi mata ya ce "Ki kwantar da hankalinki madam ba abunda ya samu cikinki ya na nan Saidai ki k'ara kula wajen rainonsa " Wani irin bak'inciki ne ya tokare zuciyar Zahra batasan sanda ta fashe da kuka ba Ta ce "wannan wani irin jarababben makwawacin ciki ne Ba irin bugun da banmasa ba Dan ya zube Amma ya like to duk jarabarsa wlh saiya fita Dan Allah dr ka fitarmun da Cikin...bata k'arasa fad'ar abunda take son fadaba sakamakon kwabe mata baki da karfi MD yayi Kallon Dr yayi yace " ka wuce kawai"Dr na fita cikin b'acin rai MD ya Kalleta ya ce "Wlh kika kara aibantamun ko yunkurin yimun asarar ciki zakiyi mugun mamaki na waike wace iri ce da bakisan lallashi ba ba irin Lallashin da ban maki ba cikin nan ko shege ne iya wulakancin da zaki masa bare cikin halak mai matsayi da gata kamar kowani d'an sunna " wani irin banzan kallo zahra ta bishi dashi kafin ta ce "kai harka samu bakin magana an aibanta cikin kayimun abunda zakamun macuci kawai" Kafin ta hade kai da gwuiwa ta fara rera kuka "Tsaki MD yaja yana dafe ka kansa yace matsala " Mikewa yayi Tare da kama hannunta yana kokarin cire mata Karin ruwan Ta fusge a murtuke ya ce "Ki tsaya na cire maki karya ja miki jini" a hankali ya samu ya cire mata Wanda har lokacin jin kukan nata yake na dakar masa zuciya komawa yayi kujerar da yake tare da bude warmers din d'aya Lafiyayyan sakwarace da tasha Miyar ja sai d'ayar kuma pepper chicken ne sakwarar ya zuba a plate tare da d'ora naman a kai sama yayi da plate din tare da Ajewa gabanta yace tashi kici "Cikin kuka ta ce " Bazanci ba Ka maidani gidanmu naga halin da mahaifina yake ciki "Ba irin Lallashin da MD bai mata ba Wanda shi kanshi baisan ya iya lallashi haka ba akan taci amma taki " Omg ya fad'a yana buga kansa da hannu ya ce "Ya kike so dani ne Wai Mamy kwana nawa bakici komai ba Zai iya shafar abunda ke cikin ki?Tsaki taja cikin Masifa ta ce " ina ruwanka Yama shafi kome zai shafa cine bazanyi ba saika kaini naga halin da mahaifina ke ciki"kwantar da murya yayi ya ce "Indai kikaci zan kaiki wajen mahaifin naki" lokaci guda ta d'ago ta ce "Ka rantse " Yanda ta fad'ar ne yaso bashi dariya ya fusge ya ce "saina rantse zaki yarda " Eh saboda kaid'in ba abun yarda bane"dukda MD yaji zafin abunda ta fad'a Hakanan ya sasa daurewa Dan yanzu ya zama dole ya lallab'ata kodan cikinsa dake jikinta da take shirin yi masa asara "kwantar da murya yayi ya ce " indai kina cin abinci da magunguna har aka sallameki wlh zan kaiki ki gansa"Sai lokacin zahra ta d'an yarda amma da sharadin yau a sallameta cemata yayi ba yanzu ba saikinji sauki sosai kafin ya d'auko sakwarar a spoon ya fara kokarin bata da farko kin amsa tayi saida ya k'ara rantse mata akan Zaikaita data warke taga Baba tukwana ta yarda dukda tace