Sashe 58
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwana biyu da komawar Zarah school MD ya rasa ta hanyar da zaije Zaria ga hankalinshi da ya tashi kiran da Hajiya tayi mishi tace ya saurari zuwanta karya zaci ta manta dukda Amera bata fiya damuwa da halin mijinta ke cikiba amma wannan Karin saida ta tambaya ta ce "Honey lafiya wai?Kallonta yayi ya ce " Me kika gani"Naga kamar akwai abunda ke damunka "Numfashi yaja ya ce " nothing kawai tafiya ce ta kamannine Germany to bana son na tafi na barki ne shiyasa saboda zanyi kewarki"murmushi Amera tayi cike da jin dadi ta ce "Kai honey saikace yau ka fara tafiye tafiye kayi tafiyarka wlh bakomai ni daman America nake son komawa na gaji da zaman Nigeria "da mamaki MD.yake kallonta a tunaninshi zatace Saidai su tafi tare ne ko ta kawo k'abli da ba Adi amma yaga cikin Sauk'i kamar ma.so take ya tafi girgiza kai kawai yayi ya ce " ko irin kewar nan tawa bakyajin zakiyi ko kamar ma.so kike na tafi'"Shigewa tayi jikinshi tace ba haka bane honey Kasan nafi kowa sonka da kaunarka da kuma kishinka kasan babu abunda zai hanani kewarka kawai dai Naji dad'in tafiyar taka ne saboda zaka bar k'asar nan ta sa ido y'an mata su daina kallemunkai shiyasa"Hmm Chan gemany din ba y'an mata kenan "Hade fuska tayi tamau tare da cewa " Aidai nasan yanda baka kula y'an mata anan ba Chan ma bazaka kuka su ba "zancen ki kenan Amera kullum magana d'aya yaci ace tsawon shekara goma kisan waye mijinki kinsan sarai babu macen da ta isa fa rud'e ni ke kad'aice tal daga ke ba k'ari to meye zaki dinga tada jijiyoyin wuya kullum magana d'aya kishiya kinsan da ina yi miki kishiya tsawon shekarun da mukayi dake da nayi ko kuma da kin taba samun labarin ina da y'an mata ko budurwa to why zaki dinga damun kanki " sosai Amera taji dad'in kalaman mijin nata da murmushi a fuskarta ta ce "Nasan da haka mijin da babu kamarsa ina son har kullum ka dinga rik'emun Amanata please MD wlh kasan bana son kishiya ina son kayimun alk'awarin bazaka tab'amun kishiya ba ko da Bayan rai nane please wlh Inajin da kayimun kishiya gwara ace ga ranar mutuwa ta tafiyumun sauki" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka Rungumeta jikinshi MD yayi dukda ba Yau Amera ta saba irin wannan maganganun ba Amma yau d'innan ta karyar masa da zuciya yasan duk maganar dake fitowa bakinta da gaske take yasan ba karamun so amera take yi mishi ba Lallashinta ya shiga yi sosai Cikin kwantar da murya da kalamai masu dadi harya samu tayi shiru da dare koda yaga tayi bacci tashi yayi zaune ya kasa zaune ya kasa tsaye a ranshi ya ce "why Hajiya zakiyi mana haka me yasa kikeson ki ruguzamun farincikin mata,ina ruwanki da rashin haihuwa ta tunda ke kina da yaran meye ruwanki da nau,me yasa kike kokarin tarwatsa farincikina da na matata iska ya fezar me zafi zirga zirga ta fara a tsakiyar d'akin Tabbas dole ne ya samu mafita cikin Sauk'i ga yarinyar ma da jaber ya bada shawarar mafita da ita ba mafitar saima Kara rikita abubuwa da hakan yayi tsaki yaja a ranshi ya ce Tabbas dole ne yarinyar nan tayi ciki ko tana so ko bata so Dan bazan tab'a jurar ganin Merah cikin wani hali ba kwata kwata kanshi ya kulle Ta ko ina ya hasaso saiyaji ba mafita dole dai yarinyar nan da jaber ya makala masa ita zai samu mafita ta hanyar ta Bai samu bacci ba sai Chan cikin dare Bayan ya gama nafilfilu da adduo'i akan Allah kawo masa mafita a cikin rayuwarsa washegari koda ya tashi asuba har lokacin da ya dawo daga masallaci Amera bacci take a hankali yahau tashinta taki tashi data tashi saita koma cikin y'ar daga murya ya ce " wai bazaki tashi kiyi sallah ba Amera kin sani sarai banason Sallar safen nan da kike "Cikin gigin bacci ta ce " Dan Allah ka rabu dani bana yi "Dukda yayi mamakin yaushe ta fara perioud saiyayi tunanin ko cikin dare yazo mata kyaleta yayi yashiga wanka Bayan ya fito ya shirya cikin shigarsa ta kasaitattun kayan da ya saba sai baza k'amshi yake Yana cikin duba wasu document akan makekekiyar kujerar dake d'akin yaga tashinta kallo d'aya yayi mata yaci gaba da abunda yake yana ganin sanda ta fito Bayan tayi wanka yana kallonta saida ta gama shirinta tsaf hada kwalliya sosai yayi mamakin Ganin ta d'auko hijab da darduma ta kabbara Salla yasan wannan ba shine karo na farko ba da take haka Amma ya rasa dalilin da yasa yanxu yake ganin dabi'un nata a wani kala tunowa yayi da Zarah yarinya k'arama amma bai tab'a ganin lokacin salla ya wuce ta ba shi har mamaki yake Yanda yarinya k'arama take da wannnan ibadar Dan wani time d'in yanajinta raba dare Take tana k'iyamul laili shi kanshi yasan duk kokarin shi na ibada yarinyar ta shanyesa ta damesa yana cikin wannan tunanin kuma sai ya tuno da kiriar d'ayar yarinyar da muryarta ta kasa barin kwalwarsa lumshe ido yayi Dan shi a rayuwar sa yana son yaga mace mai Ilimi musamman ta had'a biyun na addini da kuma na boko yasandai Amera bangare daya yayi sa a tana da ilimin boko da wayewar da duk taron da yaje da ita na manya da manya ko k'asashen k'etare bata basa ruwa tana fiddashi kunya Dan baya da shakkar ko ina yaje da ita Saidai Inda ta samu tangarda bangaren ilimin addini yana cikin wannan tunanin tajita gefenshi ta rungomasa ta ce "Sannu honey good morning" morning too dear how was your night "Fine " ta basa amsa "kamar bazai magana ba saikuma ya d'ago ya Kalleta ya ce " Amera me yasa kika raina addini haka ,sau nawa zanyi kokarin sauyaki daga kan wannan muguwar dabiar "tashi Amira tayi tare da Fara gunguni ta ce " wlh honey ka tarki y'ar cewa kwanannan Wanda da baka dashi abubuwan da baka magana akansu a da yanzu komai nayi saikace banyiba daidai bansan me zanyiba yayi daidai"ta fad'a tana ficewa daga d'akin da Kallo ya bita kafin ya maida idonsa ga aikin da yake yace "Allah shiryeki" (nikam nace Amen )ba ayi awa guda ba yaga shigowarta d'akin tare da akwati ya yafa beil din doguwar rigar aka Kallonshi tayi ta ce "Honey nafa shirya" ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Ina zuwa" America "ta basa amsa kai tsaye " Dukda mamakin abunda ta fad'a amma bai nuna mata ba "Allah ya kiyaye" ya bata amsa"Uhm to haka kawai zakace ba rakiya ba komai"Sai sannan ya d'ago ya Kalleta ya ce "Nida bansan da tafiyar taki yanzu ba Kuma bakiji addua nayi ba me kikeson nace " batare da ta k'ara cewa komai ba taje tayi hug dinsa tare bashi peck a kumatu ta ce "Bye honey sai munyi waya" tana gama fad'ar hakan tabar d'akin tana Sauri "Sai Bayan fitarta da awa Ukku sannan MD ya fita Escord dinsa suka biyo sa daga musu hannu yayi " Motarshi da ba kowa ya sansa da ita ba mai tinted ya hau Kafinma yayi horn security sun bud'e masa get yayiwa motarsa key sai Zaria koda ya isa gidansa ya nufa dukda. Yaga gidan yana buk'atar shara da mopping Dan ya fara kura tunani ya dingayi yanda zai hadu da yarinyar Dan yana tsananin buk'atarta wani tunani ne ya fad'o masa me zai hana yayi irin waccen dabarar da yayi na kiran Malam Umar ya ce a kira masa Zarah Yusuf Dan ya rik'e sunanta radam cikin ikon Allah yasan ta saikuma ya tuna kar Mlm din yayi zargin akwai abunda ke tsakaninsa da yarinyar Dan ya lura da irin kallon da yake masa tsaki yaja ya ce laifinane da ban Anshi number ta ba wani tunani ne ya fad'o masa kiran driver da ya d'aukar mata Wanda zai dinga kaita sch yayi Bayan ya d'auka ya amsa gaisuwarta a takaice ya ce "Da Allah ka rik'e yarinyar nan da kake daukowa daga makaranta" daga bangaren driver d'in ya ce "Eh ranka ya dad'e " okay gobe ina son kaje sch din lokacin tashinsu daga lectures kace ni na aikoka ka daukota"To shikenan ranka ya dad'e a Angama"daman Dan Zaria ne kuma baisan MD ba a fuska amma yasansa a baki washegari Zarah fitowarsu daga lectures kenan sun fito harabar da zasu wuce hostel taji ance "Hajiya " Bata amsa ba saboda batayi tunanin da ita ake ba cigaba da tafiya sukayi Ganin hakan ya sanya driver d'in binsu ya ce "Ranki ya dad'e ina yini" Yusuf ne ya Kalleta ya ce "da ke fa yake Daugher" Kallonsa tayi saita kalli driver dukda da farko bata Ganesa sosai ba Ta ce "Lafiya " Cikin girmamawa ya ce "Lafiya qlau Hajiya daman Alhaji ne ya turoni ya ce na daukoki nace maki shi ya Aiko ni" Numfashi Zarah taja tare da sauke ajiyar zuciya irin andameta ta ce "Ka ce masa nace bazanzo ba" Cikin girmamawa ya ce "Umarnine ya bani Hajiya Dan Allah ki daure kishigo "nima sako na baka ka kai masa ta fad'a tana yin gaba Hango su Chuchu da tayi Yusuf dai tsaye yayi yana mamakin me hakan ke nufi Kallon driver da yayi tsaye yayi ya ce " lafiya dai ko Malam "Lafiya " ya basa amsa daidai lokacin da wayarsa tayi ringing "dubawa yayi yaga oga ne Sosai hankalinsa ya tashi a sanyaye ga d'aga Daga bangaren MD ya ce " basu tashi ba ne"a sanyaye driver ya labartawa md yanda sukayi da ita"tsaki daga bangaren MD yaja ya ce "Ka bata wayar" ranka ya dad'e tabar wajen fa"ba ta yanda za ayi a bita da wayar"Kallon Yusuf yayi ya ce "Eh to ga wani nan Wanda na gansu tare kilan shi zai iya sanin yanda yayi ya kai mata wayar " saida MD yaja numfashi kafin ya ce "zankira nan da 5 minutse ka tabbatar an kai Mata wayar" yana fad'ar haka ya katse kiran kallon Yusuf yayi dake shirin barin Wajen ya ce "dan Allah Abokina ko zakayimun wani taimako ka mik'awa yarinyar da