← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 129

Sashe 7

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

~Share please~

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

💑 *AUREN WATA TARA* 👨‍❤️‍👨

MALLAKAR

*Hajara L Sadeq*

*TEAM GAWURTATTU BIYAR*💃

🅿️.........*9 & 10*

"Baba ne ya ce Wai bazanci gaba da karatu ba Aure yakeson yayi mun"

Yanayin yanda tayi maganar ne ya bashi Dariya saida ya Dan dara tukwana ya ce "My Zarah kenan rigima to meye a ciki ba saimuyi Auren mu ba Kinga ni bazan hanaki karatu ba daga degree har masters.

Turo baki tayi gaba ta ce " nidai banason Auren karatu nake so"To kwantar da hankalinki gimbiyar mata anjima zanje na samu Baba da maganar insha Allahu zai amince.

Cikin Sauri ta d'ago ta ce "da gaske ya Hafiz" saboda haka take ce masa"murmushi ya sakar mata ya ce .

"Insha Allahu" zokuga murnar da Zarah tayi kamar ance Baba ya amince.Aiko ranar Duk miskilancinta ajeshi tayi itace hada Hira da Hafiz Wanda hakan ba karamun mamaki ya bashi ba.

Da daddare Hafiz yaje ya samu Baba da maganar karatun Zarah Inda ya nuna Rashin amincewarshi sosai Hafiz ya dinga yiwa Baba magiya akan dan Allah ya amince Zarah ta tafi karatun tunda ta na da hankali nutsuwa uwa uba Ilimi Sannan ya ce "Insha Allahu kuma Baba ni zan d'auki nauyin karatunta har ta gama".

Shiru Baba yayi kamar mai nazari kafin ya d'ago ya ce "

"bank'i taka ba yaro kozan iya Amincewa Zarah ta tafi karatu tofa Indai da gaske kake sonta ka turo magabatanka a tsaida maganar Aure duk lokacin da ta gama amma haka kawai sakaka bazanbar y'ata ta tafi karatu ba sannan Ko kana fara d'aukar nauyin ta tofa sainaji magana jinjina daga magabatanka"

"Alhmdllh Hafiz ya fad'a a ranshi daman wajen da yake jira akai kenan " Nan take ya ce "Baba na Amince insha Allahu gobe magabatana zasuzo wajenka yanzu zanje na samesu da maganar".

Ajiyar zuciya Baba ya sauke ya ce " ba laifi"Ranar Hafiz cikin farinciki ya koma gida Koda ya samu iyayenshi da maganar basu wani kin Amincewa ba saboda sunsan Malam Yusuf Babban limamine da garin d'aid'aine basu sanshiba kuma sunsan mutumin kirki ne duk y'ar data fito daga wannan gidan tofa za a sameta da tarbiya.

a washegari magabatan Hafiz sukaje wajen Baba Bayan an mutunta juna Inda suka tsaida magana akan Lokacin gama karatunta za ayi Auren shi ma lokacin sannan ya gama masters dinsa hakan yayiwa kowa dadi musamman baba.

Zarah da bata San wainar da ake toyawa ba "saida dare Baba ya fad'a mata yanda sukayi " Baka iya Tantance yanayin da ta shiga farinciki ko akasin haka Amma kuma idan ta tuno da makarantar da Baba ya amince saitaji dadi a ranta batasan ya akayi ba dai maganar Auren bata kwanta mata a rai ba.

Asmy ko koda ta samu labari hada tsallen murnar ta dan babanta dashi aka tsaida lokacin cikin farinciki ta je gidansu Zarah tare da Rungume juna suna murna ta ce.

"Gaskiya nayi farinciki wlh sis bantaba tunanin Baba zai sauko haka ba inye kaga amarya a gidan Hafiz d'inta" turo baki Zarah tayi tare da "Kai mata Bugu a baya ta ce ".

" kinsan bansan zolaya "Ranar kusa raba dare sukayi suna Hirar yanda Tafiyarsu makaranta zai kasance.

Hafiz ko koda yazo Zarah kin fita tayi Dan kunyarshi take ji shiko sai fara a da farinciki ya ke ji yake kamar anmasa Albishir da gidan Aljanna bai tab'a tunanin zai samu Zarah ba cikin Sauk'i haka ba.

Ranar Monday su Zarah suka shirya tafiya Zaria domin zana jarabawarsu ta FUMB Hafiz shi ya kaisu Har Zaria Inda ya jira saida suka gama tukwana Ya juyo dasu A hanya sai kallon Zarah yake yanda take sisinna kai a gaba "

murmushi yayi tare da Kallon Asmy ya ce "Bestynmu yau fa mutuniyar Naga sarautar takeji "

murmushi Asmy tayi ta ce "Naga alama kam inaga kunyarka takejifa "

Harara Zarah ta watso mata daga gaban da take Wanda hakan ya sanya Asmy da Hafiz yi mata Dariya "Turo baki gaba tayi tare da Kallon hanya "

har suka isa funtua suna Hira jefi jefi kasancewar ba wani nisa ke akwai ba tsakanin funtua da Zaria gidan su Asmy suka sauka Dan huce gajiya kafin ta wuce gidansu Ta na isa ta samu Mama Rabi na Surfa bala i ta na cewa.

"Aikin banza aikin hofi ko anzata bamusan iskanci da karuwancin.da ake a jami'ar ba To ayi mugani idan tusa zata hura wuta Aikin banza aikin hofi " Sosai take jifar Zarah da mugayen kalamai Inda ita ko a kanta Dan itadai burinta bai wuce tabar gidan nan ta huta ba.

Cikin ikon Allah jarabawar su ta fito Kuma duka sunci sun samu admission Inda Zarah mass com suka bata saboda daman shi ta cike ita kuma Asmy suka bata Biology education .

zokuga farincikin da suka shiga Daga ranar suka fara sayayyar Tafiyarsu makaranta sun amshi kudin da Zarah ta samu a wajen sauka Inda suka sassayi kayan sawa dasu Komai iri daya suka saya da Asmy kala biyar biyar sukayi atamfofi suka saya Zane bibbiyu suka Kai d'inki ita kuma Mama ta d'inka musu manyan hijabai hurhudu saboda su Kara da nasu.

baban su Asmy shi yayi musu registration ba yanda Baba baiyi dashi ba akan ya bari zai sayar da tumakishi a kauye ya rage masa ya ce

"a.a daman shi yayi niyyar ni musu ai anzama daya " Sosai Baba yaji dadi kuma yayiwa babansu asmy Godiya sosai Zarah ma tayi mashi Godiya kwarai da gaske yanzu zaman gidansu ma gagararta yake saboda koda yaushe suna gidan su Asmy suna shirye_shiryen tafiya saboda Abun na tunkarowa Dan yanzu wata Guda ya rage musu su fara lectures Wanda ji suke kamar su jawo ranakun"
*Wacece zarah*
*Zarah Yusuf* shine cikakken sunanta mahaifinta Malam Yusuf haifaffen garin Batsari ne Noma da kasuwanci shi ya kawoshi garin funtua kasancewarshi malamin addini .

ya samu karbuwa sosai a garin kasancewar lokacin Su ilimin addini bai wadatu ba Sosai sai ya kasance yana koyar da wasu manya magidanta karatu a masallaci Bayan kammala Sallar isha i kasancewar shine limamin masallacin Unguwar da masallacin juma'ar yankin"

wannan dalilin ya k'ara sanyawa mutane da dama suka sanshi a lokacin sosai Malam Yusuf yake da rufin asiri saboda gona guda ya ke amsar haya yayi shukar masara da wake Wanda alkhairi da yake samu ba Kad'an bane .

Bayan nan kuma daman yana kiwo a kauye ganin irin cigabar da yake samu a garin ya sanyashi sayan fili a unguwar jabiri Inda a hankali a hankali ya fara gininsa cikin ikon ubangiji har ya gama .

ana haka ne wata rana yaje Noma Ya hadu da wata matashiyar budurwa sai gudu take ta na hak'i sosai hankalinshi ya tashi kuma yayi mamakin daga dajin da ta b'ullo ga Saran maciji jikinta cikin Sauri ya taimaka mata Inda anan take ta sume kai tsaye Asibiti ya nufa da ita bayan an duba Saran da macijin yayi mata nan akayi mata allura aka bata magani.

Gidanshi ya koma da ita nan ya cigaba da kula da ita ganin har lokacin Bata farka ba gudun zargin mutane ya sanyashi daukarta ya tafi da ita garinsu Batsari Inda ya ajeta gidan baffanshi dan mahaifanshi sunjima da rasuwa a hannun kanin mahaifinshi ya taso nan aka cigaba da kula da ita harta farka Saidai me koda ta farka.

bata iya magana Saidai ta kalli mutane Cikin ikon Allah da addua da komai aka samu harta fara magana Saidai me duk tambayar da akayi mata game da Iyayenta ko y'an uwanta bata iya tuna komai duk yanda taso tunawa sai ta kasa.

hakan yana damun Malam sosai kuma yana tausaya mata gata dai ba wata babba ba Dan a lokacin bazata wuce 18 years ba Saidai abunda ya basu mamaki ta rik'e sunanta Zarah.

Saida Zarah ta shekara guda gidansu Malam batare da ta tuna kowa nata ba ga kuma karfaffar soyayyar da ta shiga tsakanin ta da Malam sosai suke San junansu Wanda lura da hakan ya sanya Baffa jin dad'i kanin mahaifinshi kenan Wanda shi ya tsaye musu har aka daura musu Aure.

ranar wannan masoyan sun shiga farincikin marar musaltuwa A funtua suka tare sabon gidan Malam da ke jabiri zamansu yaci gaba da wakana cikin soyayya da k'aunar juna saboda Zarah macece mai biyayya hakuri uwa uba Kirki Dan a zamanta da mutanen unguwar sai dai Sam barka Dan kowa Santa yake da kaunarta

aminiyarta d'aya a unguwar Saratu watau maman su Asmy a lokacin yarinyarsu d'aya Hauwa'u a lokacin suna cikin halin talauci Wanda hakan sosai ke damun Zarah hakan yasa bata iyacin Abu bata bata ba sunyi zama cikin mutunci da amintaka dukda Saratu ta girmi Zarah amma haka take girmamata kuma suke girmama juna.

"ana haka ne Zarah ta samu ciki Wanda tunda ta samu cikin takeshan wahala ta ke jin a jikinta cikin kamar shine ajalinta A tattare suka samu ciki da Saratu Inda lokacin mijinta ya samu warwara saboda daman yayi karatu Inda ya samu aiki a Bangaren agric saboda daman karatun malamin gona yayi .

kwana a tashi ba wuya wajen Allah a yanzu cikin Zarah ya shiga wata Tara Inda ranar wata Juma a ta tashi da nakuda kai tsaye Asibiti aka wuce da ita sosai take shan wahala tasan rayuwarta tazo karshe a lokacin ne kuma ta tuno da rayuwarta Ta baya Tana cikin halin nakuda ta ce " .

a kira mata Malam "haka ko akayi shigowarshi d'akin tayi daidai da haifo santaleliyar y'arta sak mai kama da Ita kamar an tsaga Kara an karya.

Ajiyar zuciya Ta sauke Kallon nurse tayi dake shirin Tafiya don a shirya d'iyar tayi cikin k'arfin ta ce " mik'omun naga kyautar da Allah yayi mun"

mik'a mata y'ar akayi Inda ta tsaya tana kallonta hawayen tausayin y'ar na zubo mata shafa kanta Tayi Tare da kissing din goshinta ta ce "Allah yayi maki Albarka Zarah ya sa mai taimakon Addini ce Ina sonki Sosai y'ata saidai Allah bai nufa Ba zamu rayu tare Allah ya shirya munke yayi miki albarka Albarkata taci gaba da bibiyarki har k'arshen rayuwarki "
Chapter 7 · 0% Book details