Sashe 16
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina wasa dake Chuchu ni kike fad'awa haka na k'arajin maganar nan bakinki zan zaneki"
D'an Kara Ta saki tare da cewa "Auch sorry Babban yaya bazan sake ba" Kafin ya sakar mata kunnen ya ce .
"Bazaki koma ba Yau sai jibi week end ya k'are badan Chuchu ba taso ta zauna Dan bazata musawa Yayan nata ba Amma gabak'i d'aya hankalinta ya tafi wajensu Zarah.
suna nan zaune a palour suna y'ar tab'a Hira Har aka k'are nuno Musabakar A television Knoking da suka jiyone ya sanya Chuchu saurin Mikewa tare da zuwa ta bude.
Wani wawan tsalle ta daka ganin Hajiya kaka tare da su Adil da Ruky " dakyal ta Bari suka karaso palourn saboda d'oki MD ko gabanshi ne ya fad'i ganin zuwan Hajiya kaka gidan yasan shikenan yanzu kuma zata addabeshi akan Maganar k'ara Aure.
Sosai Ammy tayi murnar ganinsu nan ta shiga musu lale marhaban Bayan sun gaisa an cika musu gabansu da abubuwan makuleshe Chuchu suna mak'ale ita da Ruky da bazata wuce sa anninta ba suna Hirar yaushe gamo.
MD ne ya kalli Hajiya fuska ba walwala ya ce "Sannu da zuwa Hajiya anzo lafiya".
tab'e baki tayi tare da k'are masa kallo ta ce "Lafiya salamamme ina ita gimbiyar taka ko har yanzu bata haihu ba "
"Ya na had'e fuska ya ce " Daga zuwanki ba ko gaisawar kirki Hajiya "
"eh ba gaisuwar ai wannan zuwan da kaga nayi zuwan Kane na kashin kanka tunda ita Fatima ta kasa tab'uka komai ta na tsoranka karka tsireta to ni bazanji tsoronka ba idan kaga na bar nan garin nan tofa sai naga haihuwar shegiyar yarinyar nan idan ba haka ba Da Rukayya zan hadaka Auren zumunci sai Inga ta tsiya.
" Ba MD ba hatta ruky saida ta d'ago jin maganar Hajiya kasa tayi da kanta Dan Ita kanta tasan karya take tace batason MD amma kuma tasan MD bazai tab'a sonta ba yafi karfinta kuma ma ita tana da Wanda takeso "
"Shiko gogan Mikewa yayi ba tare da ya nuna Alamun damuwa a fuskarsa ba ya haye stairs da Kallo Hajiya ta bishi ta na Jan tsaki" Chuchu ko Dariya tayi kasa kasa tare da tsunkunin Ruky ta ce "Kaji amarya a gidan yaya MD" .
harara ta maka mata Arif ko Tunda ya shigo ya ke kallon sahibar ta sa Chuchu ta message yayi mata magana da su kebe Dagowa tayi suka hada ido tare da sakarwa juna murmushi Ya Mike ya fita Ta na ganin haka itama ta bisa "tab'e baki Hajiya tayi ta ce.
" kuma Kunzo ku fad'amun abunda ke tsakaninku Dan na gaji duk Aurar da ku zanyi yara sun girma sun bunkasa a gida Suna gogayya da iyayensu"cewar Hajiya ta na Jan tsaki Ammy dai murmushi kawai take.
Washegari asubanci MD yayi yabar garin daga shi sai Jabir kamar koda yaushe tafiyar sirri sukayi har suka isa garin gombe.
Daga gombe ma nayi mamaki irin dajin da suka Yanka kafin Su isa wani k'aramun kauye karshen kauyen naga tafkeken gida flat da ya tsaru Inda suka kutsa motarsu cikin gidan
Zaune yake gaban wani dattijon mutum Wanda bazai haura shekaru 65 ba ko fi a kwance ya ke yayinda idanunsa suke a bud'e Babu abunda yake motsi a cikin jikinsa sai y'ar yatsarsa Gadon da yake MD ya hau tare da kamo hannun dattijon ya rike gam gam ya na murzawa Shima shi yake kallon dattijon ba abunda yake sakar masa sai Murmushi ".
Muryarshi na rawa Alamun damuwa k'arara a fuskarsa ya ce" Allah ya baka lafiya Insha Allahu Inajin a jikina wahalar nan taka ta kusa zuwa karshe da izinin ubangiji "
"Lumshe ido yayi tare da budesu Alamun yaji dadin abunda ya fada " wani Dattijon ne ya shigo Shima da bazai wuce sa'annin na kwancen ba .
"Kallonshi MD yayi ya ce " Sannu Baba A Gaskiya ba abunda zance da ku sai Godiya Allah ya saka da alkhairi jikin nashi na ga ya fara sauki masha Allah".
Da Fara a tsohon ya ce "muke da Godiya a wajenka ranka ya dad'e kai ka gama yi mana komai Allah dai ya basa lfy yanzu kam ana samun cigaba sosai Dan jiya har hannunshi saida ya motsa "
"Nauyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce " Baba inason a ninka akan saukar da ake masa Ya tashi daga duk sati ya koma duk kwana biyu "sannan ya mik'a masa mak'udan kudi ya ce " gashi a k'ara rabawa malamai da kuma makarantu a ninka sadakokin da ake ".
***
Tsaye yake sai safa da marwa yake waya na K'are a kunnashi cikin tsananin tashin hankali ya ke cewa " garinya har aka bari aka kama su baushe Aiko muddin suna hannun hukuma akwai babbar matsala sannan shi MD din zanyi maganinsa ina zuwa karka damu bazasu tab'a Tuna Wanda ya sanyasu aikinba ko za a kashesu".
Ya na Gama wayar cikin Sauri ya bar gidan tare da wucewa wajen tsafinsu Dan a rufewa su baushe baki.
Da dare aka kirasa akace aiki ya gama ranka ya dad'e sunkasa fad'a "Dariyar mugunta ya kwashe da ita ya ce " suna wasa dani basu San waye Alhaji mudan ba manya ma mun gagara baresu kanana kanana sannan shi MD zaisan ya shiga gonata ubanshi ma na gama dashi bare shi darajar soyayyar da y'ata kawai take masa yake ci nasan muddin na kashesa zata shiga mugun hali wanda bazan juri hakan ba saboda soyayyar da nakeyiwa Amera y'a daya tilo amma badan haka ba Da na jima da shafe Tarihinsa a cikin rayuwa k'aramun kwari"ya k'arasa fad'a ya na kecewa da wata dariyar irin ta su ta mugaye.
<Zaria>
Ran Monday Chuchu ta koma school koda ta je a lokacin Zarah taji sauk'i da damuwa ta ce " wlh hankali na duk a tashe yake me ya ke faruwa?
"Haba daughter Ai zuwanmu kadunar nan munga tashin hankali nan suka bata labarin abunda suka gani sannan Zarah ta d'ora da cewa .
" wlh Chuchu bantaba Jin tsanar wani mahaluki ba sama da MD d'innan na tsanesa na tsani duk Wanda ya shafesa zubar da jinin mumuni guda d'aya wasane Chuchu yaza ayi k'asarmu ta zauna lafiya ana zubar da jinin musulmai a gabanmufa mugun mutumin nan ya harbe bayin Allah suna Tafiyarsu basuji ba basu gani ba "
.rumtse idonta Chuchu tayi Jin Yanda Zarah ke aibanta Yayan nata mafi soyuwa a gareta Cike da damuwa ta ce "Amma bai kamata ace kin yanke hukunci batare da kin bincika ba kika sani ko masu laifi ne "
Wani banzan kallo Zarah ta watsa mata tare da cewa "Ai daman haka za ace tunda Mai kud'ine komai yayi daidaine Ta haka aka karesa kenan to ai idan duniya ta karesa zaiyi bayani a lahira mugu azzalumi macuci makashin mutane ko kema kina goyon bayansa ne"
Kara rumtse idonta Chuchu tayi Jin bazata iya d'aukar wannan mugayen kalaman ga yayantaba ya sanya ta tashi tashi tare da komawa gadonta ta kwanta tare da rumtse ido Tanajin zafin maganganun da Zara ke yi akan Yayan nata .
Tabbas inko hakane dole ta boyewa Zarah cewar ita kanwar MD ce Dan yanda taga tsanarsa k'arara a idonta tasan Kanwarsa ce Zata iya rabuwa da ita Wanda bazata juri hakan ba Dan a tarenta da Zarah ta koyi abubuwa da dama na karuwa
A halin yanzu su Zara sun gama Exams Inda sukayi hutun second semester da sun dawo level3 zasu shiga.
Koda ta koma gida a kofar gida ta tarar da Baba cikin farinciki ta je ta gaishe da mahaifin nata ya amsa mata ya na sanya mata Albarka sun tab'a Hira sosai ta y’a da uba kafin ta wuce cikin gidan
Ta na shiga khairat ta rugo da gudu tare da Rungume ta ta ce "oyoyoy Aunty Zarah Sannu da zuwa" itama Rungume y'ar uwar tata tayi ta ce "Sannu my khairat ykk ya makarantar kina dai zuwa ko" gyada mata kai tayi tare da Amsar akwatinta ta shigar mata dashi ciki.
Mama rabi ce ta lek'o daga daki jiyo Zarah da tayi da Fara a Zarah ta ce "Mama ina yini" tsaki taja tare da cewa "da baki ganni lfy ba andawo daga yawon katuwancin ko Har wani kiba da kyau aka k'ara hmm muna nan dai muna jiran kishin dan abun nan ba banza ba akwai lauje cikin nad'i".
Girgiza kai kawai Zarah tayi Dan tasaba da kalaman nan ta na shiga daki Nan ta fitowa da khairat tsarabarta Godiya tayi mata jin bataji Safiya ba a gidan ya sanyata cewa " waini ina Safiya tunda na shigo banjitaba"tab'e baki khairat tayi ta ce .
"Baba ya maida ita Batsari gidan Bappa samari ke zuwa Wajenta har a soro suke zance rannan Baba ya kamata wani na rungumarta ranar Tasha Duka a ranar ya kaita Batsari ya barota ya ce bazata k'ara dawowa garin nan ba ".
Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce " Allah ya kyauta kedai Dan Allah khairat ki nutsu karki Shiga rayuwar nan marar kyau"murmushi tayi ta ce "Insha Allahu Aunty itama safiyar ai su Aunty Habiba ta ke biyawa"
Bayan ta huta Corn flask ta jika tare da madara ta sha ta kwanta ba b'ata lokaci baccin gajiya ya kwasheta saboda akwai tsananin gajiya tattare da ita.
<Kaduna>
Duka zazzaune suke a palourn hajiya,Ammy ,Adil,Chuchu,sai Ruky MD dake Danna waya Hajiya ta Kalla ta ce.
"Wannan karin maganar da nazo da ita ba wasa Mustapha wlh wlh kaji na rantse shekara guda na baka idan Matar ka bata haihu ba ko bata samu ciki ba ko a kauye ne sai na nemo maka mata na aura maka ko ka fito mun da wacce kakeso amma Bazan juri cigaba da ganin wannan kayan takaicin ba Mace d'aya ta zauna ta na Juyaka macen ma ba y'ar arziki ba to wlh baka isa ba ni ba tsohuwar banza ba ce Na baka shekara guda idan ba haka ba zakaga irin hukuncin da zan yanke maka salamamme a haka kamar zai tab'uka abun kirki a ido kamar mai jarumta nanko solo ne fanko kawai Me Auren ya amfaneka dashi aikin banza aikin hofi "