← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 129

Sashe 84

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bari na rakaku Mama"Kallon Chuchu tayi ta ce "Ita kuma bakuwar ki barta ita kadai ki bari mu dawo A tare suka fita da Zarah hankalinta duk a tashe koda suka isa Asibiti Mama Habi cewa likitan yayi " Yi mata awon ciki"Gaban Zarah Ya bada daram Kallon Mama habi tayi tana so tayi magana taga yanda ta had'e fuska ya sanyata shiru Fitsarinta Dr ya d'auka Bayan yasa tayo a wata k'aramar kwalba ya tafi awo tagumi Zarah tayi Gabanta na tsananta fad'uwa ba ayi 20 minutes ba dr ya dawo Y'an rubuce rubuce yayi kafin ya d'ago ya kalli Mama Rabi ya mik'a mata takardar"Amsa tayi tace "Ba gane rubututtukan nan naku nake ba Dr fad'amun abunda ke damunta" Murmushi yayi ya ce "To shikenan Mama " Tana D'auke Da ciki ne Na wata Ukku da sati Ukku"Cikin tsananin tashin hankali Zarah ta d'ago ta kalli Dr Ta ce "Ciki kuma Dr" eh idan baki Yarda da result d'inmu ba zaki iya zuwa wani asibitin a aunaki amma Tabbas ciki ne dake na Wata hud'u ba Sati d'aya "Tashin hankali ne ya ziyarci zuciyar Zarah Wanda Bata tabajin irinshi ba a iya Rayuwarta ba " Batasan sanda Ta d'ora hannu aka ba Tana shirin kurma ihu cikin b'acin rai Mama Habi ta kwabe mata baki ta ce "Yiwa mutane shiru tashi muje" ta fad'a tana wartar hannunta "Sukayi waje kuka Zarah takeson tayi Amma tashin hankali yasa ta nemu kukan ta rasa Suna fita harabar asibitin Mama Habi ta ce " Tonon asiri ne zakiyi mana a Asibiti kowa ya fahimci halin da ake ciki ai ba yanzu ya kamata kiyi kuka ba yana nan gaba "Kuka Zarah ta fashe dashi Sosai ta ce " Wlh Mama karya yake bani da wani ciki sharri ne kawai zaiyi mini"d'auketa da Mari Mama Habi tayi cikin b'acin rai Ta ce "Yi mana tonon Asiri a titi Zakiyi bayani idan mukaje gida gaban mahaifinki bani ba " Tsaida mai napep sukayi suka shiga hade kai da gwuiwa Zarah tayi ta shiga rera kukan tausayin kanta Tabbas indai da gaske ciki ne da ita Musty ya cuceta ya gama da ita ya cuci rayuwarta "batasan sun isa gida ba Saiji tayi Mama Habi ta Ja hannunta bata dire ta ko ina ba sai d'akin Baba Kujerar Dake d'akin ta wullar da Ita tana huci ta ce " Kin cuce mu Zarah kin b'ata mana sunan zuri'a ana tunanin wuta a makera ashe a masak'a za'a sameta Kinban mamaki ko a mafarki ban tab'a tunanin zakiyi mana haka ba kin cuce mu kin cuci mahaifinki kin cuci mahaifiyarki dake k'asa sannan kin cuci kanki.........✍🏿
Chapter 84 · 0% Book details