← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 129

Sashe 55

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari MD yana zaune yana hutawa a palour Amera na gefenshi suna zuba love Wayarshi tayi ringing dubawa yayi yaga Baba audu ne mai kula da tsohon nan na gombe cikin Sauri ya d'auka banji komai akace daga bangarenba saigani nayi ya Mike a matuk'ar firgice ya ce "Alhamdulilla Alhmdullillah Allah mungode maka gani nan zuwa yanzu " yana gama fad'ar haka ya katse kiran daka Kallesa kasan yana cikin farinciki Kallonshi Amera tayi ta ce "Honey ya naga ana kiranka duk kabi ka wani rude " Murmushi ya sakar mata ya ce "wani abun farinciki ne ya sameni " Da Fara a fuskarta ta ce"daga ina "Murmushi kawai ya sakar mata yace " zakiji idan na dawo "yana gama fad'ar haka ya fita da Kallo ta bishi kafin ta tab'e baki MD na fita jaber ya kira Inda Yayi mishi albishir kamar yanda Baba audu yayi masa a Airport suka had'u Ba bata lokaci jirginsu ya d'aga gombe kamar ko yaushe gidan suka isa sosai MD yayi farincikin samun lafiyar Baba a palour suka sameshi shida Baba audu da Matar shi tunda ya shigo Baba tsoho ya kafeshi da idanu sai Murmushi yake sakar masa Shima MD murmushin ya sakar masa Bayan sun zauna cike da girmamawa yace " ina yinin ku Baba"Lafiya qalau Yaron kirki anzo lafiya"Alhmdllh ya jikin Baba "ya fad'a yana kallon shi " Da murmushi a fuskarsa ya ce "Alhamdulilla yaron arziki hakika bani da bakin da zan gode muku a bisa ceton rayuwata da kukayi kunyimun abunda babu abunda zan iya cewa daku saidai fatan samun aljanna kuka ne yaci karfinsa cikin Sauri MD ya tashi ya koma kusa dashi tare da dafoshi ya ce " Dan Allah Baba kayi hakuri yau ranar da ya kamata kayi farinciki ne fiye da kowace rana tsawon shekaru Ashirin da wani abu kana kwance yau Allah ya tasheka ai farinciki ya kamata kayi Baba karka damu da abunda nayi maka ka daukeni tamkar jikanka Dan Allah kayi shiru bazanji dad'in ganinka kana kuka ba "Goge hawayen shi yayi ya ce " dole nayi kuka yaron nan tsawon shekara ashirin da wani Abu ina kwance kai kake kula dani sha na magani na da komai ai dole nayi kukan farinciki kafin ya damki hannunshi ya ce "Allah yayi maka albarka yaron nan yasa ka gama da duniya lafiya ya kareka daga sharrin makiya da mahassada ,Allah kareka daga sharrin makiya na jikinka da Wanda bana jikinka ba ,Allah raba ka da sharrin mahassada ,Allah ya biyaka da gidan Allah Nama rasa wace irin addua zanyi maka kayimun abunda Bazan tab'a mantawaba dashi ba a rayuwa kayimun abunda babu Wanda ya tab'amun a rayuwa Allah sa ka gama da duniya lafiya" Ameen kowa ya amsa nan yayita Jerawa MD adduo'i Bayan komai ya lafa an gaggaisa Jaber ya kalli tsohon ya ce "Baba ka tuna shekara ashirin da biyu da suka wuce abunda ya faru mun tsineka ne yashe a gefen titin a hanyar jigawa dajin Allah mukuma a lokacin ni da Amini na ya fad'a yana nuna MD da yayi k'asa da kansa ya ce mundawo daga garin kenan Wani bikin dangin mahaifi na da Abokina yayimun rakiya kasancewar tare muka taso tun yarinta a lokacin bamu da wasu shekarun kirki lokacin da muka tsinceka da farko mun tsorata Da ganinka Dan dajin nan babu alamar mutum a ciki Sai kukan tsintsayi da namun daji dak'yal dai mukayi shahada muka tsinceka kai tsaye wani local government da muke kusa da garin muka nufa dakai mai suna kazaure Inda muka kaika Asibiti da farko d'aukar mu baka da rai saida likitoci suka fara aiki akanka kafin Su fara ceto rayuwarka Satinmu guda a asibitin kazaure ganin ba wani cigaba sosai ya sanya muka wuce Asibitin kano dakai kasancewar munsanar da iyayenmu kuma suka kara mana karfin gwuiwa akan taimakon da mukayi yasa bamu samu wata matsala ba dukda kasancewar mu ba wasu manya ba watanka guda bakasan Inda kanka yake ba saboda saida akayi maka aikin Harbin da aka maka kafin Allah ya taimaka ka farfado koda ka farfado Kalmar farko daka furta shine a " Karku kasheni me nayi maka kake son hallaka rayuwata da ta iyalina"Dak'yal muka samu kabar sabbatun dak'yal ka yarda damu a lokacin Dan mun fad'a maka taimakonka zamuyi ka tambayemu a ina kake "Muka fad'a maka kano" Cikin tsananin rud'u ka ce "Ku fiddani daga garin nan indai taimakona kukeso Kuyi zai iya zowa har nan dinma ya kashe ni ina ina " Mamy Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Allah kasa bai kashe mun Mamy ba "Abunda kake maimaitawa kenan duk ka firgice akan Sai an fitar dakai daga kano saboda zasu iya biyoka nan yayi kusa da garinku " Ganin hakan duk hankalinmu ya tashi kuma muka lura kamar akwai wadanda ke harin rayuwarka rasa Inda zamu kaika mukayi gashi dukka firgice gombe shine garin da ya fadowa MD a rai a haka muka nufo gombe dakai Inda ya saya wannan gidan sannan ya samu wasu miskinai dashi da matarsa suna buk'atar wajen zama ya d'aukesu akan zasu kula dakai saboda tun sanda muka shigo garin kayi loosing memory a fahimtar mu ka manta komai sannan kuma ka daina magana wadannan mutanen su Suka dinga kula dakai da taimakon MD da adduo sa sadakokin da saukar qurr ani da aka dage Dan saidaga baya muka lura abun kamar akwai sihiri "Tofa kaji Baba a yanda muka sameka fatan kaima zakayi mana bayanin musan asalin waye kai" Tunda aka fara maganar yake Hawaye Kallonshi kawai su MD suke saida yakai karshe kafin ya d'ago ya ce"Na tuna lokacin nan yaron nan Wanda daga lokacin ban Kara sanin Inda kaina yake ba sai shekarun baya hud'u zuwa biyar Saidai bana iya komai sannan Ko nayi kokarin magana bana iyawa Bazan iya fada maku Tarihin rayuwata ba saboda tuno abun tamkar fama tsohon raunin da ke cikin zuciya ta Wanda bazai tab'a gogewa ba har abada Zadai ku iya sanin suna na "Abdussalam"Kuma haifaffan garin jigawa Wanda a halin yanzu babu garin da na tsana bana fatan ko wuce hanyarshi sama da garin nagode da taimakon da kukamun Saidai bazan iya fada muku takaicin labari na ba " Duk numfashi sukaja Inda MD ya ce "Karka damu Baba basaimunji komai ba yanzu ina kake son zama mu koma garinmu tare da Kai watau kaduna" girgiza masa kai yayi ya ce "A a yaro ka barni a nan hankali na yafi kwanciya a nan din " Ajiyar zuciya MD ya sauke yace shikenan Baba ba matsala saika zauna tare da su Baba audu koko a saya maka sabon gida idan kafison zaman kai d'aya "hawaye a fuskar sa ya ce " A a a nan dinma yayi indai ba takura su ba"Cikin Sauri Baba audu yace"ai muma bazamuso ka tafi ka barmu ba munriga ansaba "matarsama dattijuwa tace " Gaskiya kam an saba "MD bai bar garin ba saida ya bar musu mak'udan kudin da zasu buk'ata nan gaba sannan ya sanya aka sayowa Baba waya da sim Dan sun dinga gaisawa a hanya sai Farinciki yake yana mamakin wani irin Abu ne akayiwa tsohon nan da har yake gudun garinsu na haihuwa shi kanshi saboda tsaron tsohon ya sanya yake tahowa a sirrance koda suka isa kd har dare ya fara gidansu ya fara zuwa yayima Ammy albishir da samun lafiyar Baba Inda ya bata labarin abunda ya basu a takaice sosai Ammy tayi farinciki kuma tayi adduar Allah ya k'ara masa lafiya ta ce Insha Allahu Zata samu lokaci taje ta ga jikin nasa daga gidan ammy gidansa ya wuce lokacin Amera hartayi bacci saida ya shiga d'akin ta gane yadawo cikin hammar bacci ta mik'e ta ce " yaushe ka dawo honey"yanzu harkinyi bacci kenan"wlhko na gaji da jiranka na kwanta wai ina kaje haka "Wani waje ina tsohon nan da nake baki labarin mun tsinceshi da dad'ewa tun kafinma muyi Aure " Eh nagane"Shine ya warke ya samu lafiya"Tab'e baki Amera tayi ta ce "Kaidai honey baka gajiya da kwashekwashe wlh a tunanina tuni ka wurgar da talakan tsohon nan saikaje ka kwaso mana alkakai daga tsintar mutum a titi kawai ka daukeshi ka dinga hidima dashi Haba wannan Abu Dame yayi kama sai wahalshe da kanka da kayi ba dangin iya bana baba Nifa banason harka da talakkawa wlh Haba su goga maka karnin talauci " ta fad'a tana yamutsa fuska"girgiza kai kawai MD yayi Dan baiyi mamakin abunda ya fito daga bakin Amera ba Tun fil azal ita daman ta tsani talakka Wanda hakan d'abi'ar da ta taso da ita daga gidansu ne duk yanda yaso ya sauya ta amma hakan ya gagara "Baice mata uffan ba sai rage kayan jikinshi da yayi yanajinta tana gunguni a haka har yaji ta koma bacci girgiza kai kawai yayi yana mamakin yanda Amera ta tsani talaka take wulakanta mutane da batasan darajarsu ba " Bayan ya watsa ruwa gefenta ya kwanta baccin gajiya ya daukesa..washegari around 11 dare MD na kwance Amera na gefenshi tana chat da kawayenta Sai dariya take shiko ya lumshe ido babu wacce ke fad'o masa a rai sai Zarah a Gaskiya yana da buk'atar ta koba komai tana bashi abunda baya tab'a samunshi a wajen Amera koda kuwa zai shekara suna Abu d'aya "Lumshe ido yayi ya bud'e sai yaji Yana son jin muryarta tsaki yaja a ranshi , "Tunani yayi yanzu ai ko yaje zaria suna Hutu tunda ba sanin garin da take yayi ba Yasan dai tunda take zaman hostel to ba yar garin bace Kallon Amera yayi dake gefenshi tana chat ya ce " My Merah chat d'in ya isa kizo mu kwanta"Sorry honey ka kwanta wani labari ne luzy take bani ba yanzu zan kwanta ba "Shiru yayi bai kuma ce mata komai ba " Duk yanda yaso bacci ya d'auke sa kasa daukarsa yayi saboda a matuk'ar bukace yake sai wajen 12:00 yaji kwanciyar Amera janyota yayi jikinshi koya rage zafi Amera najin haka ta ce "Haba honey Dan Allah ka barni na gaji Wlh bacci nakeji" Kyaleta MD yayi badan komai ba saidan bayason takurata a ranshi yana mamakin saita dinga cewa ta gaji saikace wace ke wani aikin wahala na farko
Chapter 55 · 0% Book details