← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 129

Sashe 122

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

polourn Amma Basu fito kallon asmy tayi ta Ce "Jifa Dan girman Allah yanzu mintinmu nawa anan Wama yasan dadewar yaran a palour ga kofa ba rufe da key ba Dan Allah want mugun ma basai a sache yaran suna chan ba wlh saina fadawa ammy "Ta fada Tana lalubar number ammy "Asmy Ce ta Ce "Karki kirata Dan Allah "Allah saina fada Mata ba iya rainonsu zasuyi ba "Ammy na dauka chuchu ta Ce "Kinganmu Nan ammy munzo gidan muka iske Yaran a palour kofa a bude ba key sai kuka suke har yanzu Kuma Basu waiwayesu ba "Subhanallah irin ta'asar da zasu tafka kenan Daman Ina Shirin kawo masu aiki su taimaka.mata da aiki da Kuma nanny din yaran Bari yanzu yanzu nakira Mai samamun y'an aiki ta samo wacce xata dinga kula da Yaran"Ajiyar zuciya chuchu ta sauke ta ce "To Ammy"Saida su chuchu suka kwashe awa guda kafin suga fitowarsu hannunsu sartse cikin na juna MD yasha bak'ar shadda da tayi mugun amsar farar fatarsa har wani shining shaddar take tana walkiya Zahra ko sanye take cikin atamfa super Holland Wanda duk a cikin kayan data gani a wardrobe ne duka size dinta ne tasan aikin Ammy ne Dan Bayan dawowarsu ta taba amsar size dinta Zahra na Ganin su chuchu ta saki hannunshi wajensu ta nufa cikin farinciki ta na murmushi ta Ce"Yanzu kuka zo"Harararta asmy tayi ta Ce "a a a Nan muka kwana"y'ar dariya Zahra tayi ta ce"Sorry maida wukar sauke lillte a bayanta da tayi bacci Asmy tayi ta kwantar da ita chuchu Daman tunda Amar yayi bacci ta saukesa kallon MD sukayi suka gaisheshi ya amsa musu cikin sakin fuska "Kallon Zahra chuchu tayi ta Ce "Ina kwana auntynah"Harararta zarah tayi "y'ar Dariya chuchu tayi "MD dai kallon matar tasa kawai yake Wajen Yaran yaje kowanne ya Basu peck a kumatu kafin ya juya ya kalli chuchu ya ce "Kuyi Mata gyaran komai please Karki Bari tayi aikin komai na baki amanarta"Insha Allah Yaya"Chuchu ta amsa Tana dariya kasa kasa"Zahra ko Kallonshi kawai tayi Ganin ya kashe Mata ido daya ya sanyata kasa da kanta Tana murmushi Saida MD ya fita su chuchu suka samu damar zolayar Zahra Asmy ta ce"Kuntafi Kuna love kunbar Yara sai kuka suke "Dariya chuchu tayi ta Ce "Antafi sama musu kanne dai Dan matar Yaya twins da triple zata dinga Haifa Mana kafin 5 years gidan ya cika da Yara tako Ina "shegantaka sosai suka dinga Mata wani ta biyesu wani ta kyalesu yanda MD ya fada su chuchu sukayi aikin komai Banda Zahra da ta kula da Yaran Bayan sungama Mata sauran gyare gyare sun karaa gyara Mata kitchen dinta da jeren da bai musu ba suka sake Wajen ukku sukaji knoking chuchu ta je ta bude Ganin aunty zey Ce sosai tayi murna Bayan ta shigo parlourn Gaisheta Zahra tai ta amsa cikin girmamawa a Tare da cewa "ya bakunta "Alhmdllh"Ta fada kasa kasa "Masha Allah Ubangiji ya bada zaman lfy Mai dorewata fadad'a Tana daukar Zahra ta Ce "Nayi kewarki Ammynmu"Saida ta danyiwa little wasa kafin ta Ce "ki yafa gyale maza ne zasu shigo da Kaya"to "Zahra ta fada gyale Zahra taje ta dauko ta yafa Fita zey tayi ganinta sukayi da kawai Maza na shigowa da jibga jibgan akwatina na gani na fad'a Saida aka jere akwati hamsin reras a palourn Sosai su kansu su asmy sukayi mamakin kayan lefen zey na murmushi ta Ce "To Amaryarmu ga lefe dai munkawo na Bangaren Ango sai Kuma na Bangaren Ammy da chuchu munji dai su shiru"dariya chuchu tayi ta Ce"Naku wasa ne Aunty Zey kikaga namu saikun Raina Naku"Dariya zey tayi ta ce "Ah to muga nakun Mana"Sosai Zahra tayi mamaki Kamar tayi magana yanzu wanna uban kayan duka lefantane ikon Allah "Asmy Ce ta Ari bakinta ta Ce "Kai Masha Allah Aunty gaskiya Kaya sunyi Allah Ubangiji ya saka da alkhairi ya Kara bud'i"chuchu ma ta Ce "To mungode Dai Allah ya saka da alkhairi Bari mu bude muga ko kunyi Abun kirki"ta fada suna Fara bubbude kayan na gani na fad'a mikewa zey tayi ya Ce "Bari na wuce naji Ammy nayimun waya zantafi da little anjima ya taho da ita saina dawo"TO aunty angode Allah saka da alkhairi"ta fada tare da mikewa tarakata har bakin kofa kafin da dawo ciki sai sannan aka Fara bude kayan da ita dariya chuchu tayi ta Ce "Waida Aunty Zey kikejin kunya shiyasa duk Kika wani daddare Naga Baki sake da ita ba kodan hakane Tana da wuyar sabo miskilancin tsiya gareta Anna ke ai Naga Tana sake Miki Sosai ki saki jiki da ita Bata da matsala wlh sannan ko wasu shawarori kike da bukatar irin Naku na masu aure zata taimaka Miki ba ruwanta "chuchu ta fada Tana dariya "Girgiza Kai kawai Zahra tayi ta ce"Insha Allah Abun bamu Saba Sosai ba shysa Saida suka daddaga kayan kowace akwati shake take da Kaya Banda akwatin zinare ma guda na sarkoki da awarwaro da zobuna Masha Allah anyi Kaya na kece rainin sai magriba su chuchu sukayi mata bankwana suka wuce Ganin dawowar MD Da dare suna manne dajuna ya ce"My princess Kinga kayasunyu maki ko"Murmushi tayi ta Ce "Eh Ya musty Nagode Allah saka da alkhairi ya Kara bud'i "Ameeeenmmn matar aljanna "ya fada Yana juyar da ita washegari Nanny din su Yaran biyu sukazo Wanda Ammy ta daukesu suka Fara kula dasu inda iyayen sure zuba love dinsu ba Kama hannun yaro Dan MD fitama gagararsa takeyi yini yake a gida Sai da suka kwana biyar kafin su fito ya zagaya da ita gidan taga ko ina Wanda wani wajenma a mota yakaita saboda Nisan musamman katoton lambun Gidan Masha Allah gsky Gidan yayi matukar kyau cikin gidanko ko palour ne guda takwaas kowanne shake da kayan waje Banda biyu da suke dauke da irin namu na Nan nja saidai Suma Masha Allah Anan Zahra ta gane sune Wanda su baba sukayi Mata kenan Sosai ta Yaba da irin kokarin da baba yayi bedroom din dakinko 12 kowanne Shima shake da Kaya nasu tiple ma cike da kayansu Banda dakin wasansu Wanda aka Sanya kekuna da abubuwa a compound gidanma had a Bangaren wasan Yara an zuba uban Kaya shakatawa baby banbanci da park ranar Ammy ta turo da nata Lefen akwati Sha biyar mamaki duk ya Gama cika Zahra to su wanna wani irin kudine garesu Kamar basusan darajar kudi ba Cikar Zahra sati a Gidan Tana kallon palour MD ya shigo Tana Ganin yanda take fara'ar tasan akwai magana wajenta ya nufa tare da rungumota ta gefe ya Ce "rufe idonki"Murmushi tayi tare da rufewa "Ba ayi two second ba ya Ce "open your eyes"budewa tayi taga ya Sanya mata kwalin waya kirar iPhone14 a hannu wara idanu Zahra tayi ta Ce "Wow"murmushi yayi ya Ce "Surprised na farko kenan tukuicin budurcinki "Wow Zahra ta Kara fada cikin doki ta Ce "Thanks thank you so much my Love Allah ya saka da alkhairi ya Kara bud'i "ameeen princess"Kafin yamikar da ita yaja hannunta sukayi waje daidai Wajen dalleliyar jar motar da Zahra Saida ta tsorata da Ganin kyau irin na motar ya jata daidai mota ya tsaya Yana murmushi ya Zaro"Key"Din Motar Ya Mika Mata ya ce"Ga motarki my love Tukuicin bani farinciki da bawanda ya bani saike na Haifamun triple da kikayi"sannan Ya k'ara d'auko wani Key d'in ya mik'a Mata ya Ce "Wannan Kuma makullin gidanki ne Dake abuja na sanyani kuka da kikayi na rubuta da shaidu da komai ya Zama naki halak_Malak "Ai Zahra daskarewa a Wajen tayi ta rasa want irin farinciki zatayi kawai sai fad'awa jikinshi tayi batasan sanda ta fashe da wani kukan farinciki ba cikin kuka ta ce............ ✍️
Chapter 122 · 0% Book details