Sashe 72
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"na shiga ukku na lalace Asmy shikenan na bani na lalace na shiga ukku na " ta k'arasa fad'a a matuk'ar rude tana d'ora hannu biyu aka "a d'imauce Asmy ta Dauki takardar ta ce " me akayi Zarah"Da hannu ta nuna mata da ta karanta "kafin ta k'ara rushewa da wani kukan Bud'e takardar Asmy tayi gabanta na fad'uwa Ta fara Duba good handwriting dinsa da bai wuce layi shida ba fara karantawa tayi kamar haka" Ko a addinin Christian ba a Aure kan Aure bare addininmu na musulunci da ya haramta hakan Har yanzu har gobe da Aure na akanki basaina yi doguwar magana Ba nasan kina da Ilimi kinsan abunda yake fari da baki Ki rik'e mutuncinki na Matar Aure ban Aureki Dan in sakeki yanxu ba har sai na samu cikar buri na nima kamar yanda kika samu naki zan waiwayeki nan bada jimawa ba ina Kara tuna maki karki sake ki yarda ki bari a daura miki Aure da wani Bayan da igiyar Aure na a kanki bye ki huta lafiya black beauty " "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" Asmy ta shiga maimaitawa tuni idanunta harsun cika da k'walla ta ce "Shikenan ya kashemu bake kika shiga ukku ba Nina shiga ukku Zarah Dana ja miki wannan Abun " ta fad'a itama tana fashewa da kukan sai ya zama.cikin su bamai Lallashin wani Asmy ce tayi dauriya ta mik'e cikin b'acin ran da tajima batayishi ba ta ce "Wlh basu isa ba Jirani naje gidan basu isa su maidamu y'an iska ba me suke nufi " ta fad'a tana wartar hijab d'inta ta fita Zarah ko sosai take kuka Tana Danasanin abunda suka aikata Tabbas sun tafka Babban kuskure da wauta yanzu yazatayi da rayuwarta?Bikinta da ya Hafiz fa ?Taya zai Aure ta Bayan da igiyar Auren wani a kanta?Taya zan iya yiwa Baba bayanin wannan Abun bak'inciki"da wani ido zan kalli mutane shikenan abunda nake gudun ya faru asirina zai tonu Baba banyi maka adalci ba naci amarka naci Amanar tarbiyar da yardar da ka ban....kuka ne yaci karfinta ta kasa k'arasa abunda take cewa a haka har Asmy ta dawo sai huci take "Kingansa?Zarah ta fad'a cikin muryar kuka" Ina fa gidan kulle da kwado ko get man babu "Innalillahi Mutumin nan ya cuceni ya gama da rayuwata Allah ya isa tsakani na dashi" Zarah ta fad'a tana kuka Wayarta Asmy ta dauka tare da dannawa jaber kira yana d'auka bama gaisuwa cikin jaraba ta fara cewa"Daman haka kuke ,K'ananan mutane ne ku daman bamu sani ba ,to wlh kunyi Gina kun tarda ruwa wlh baku isa ba wlh"Jaber da baisan wainar da ake toyawa ba cewa yayi"nutsu kiyimun bayani Dan Allah ma'u me yake faruwa wai"Ai kafi kowa sanin abunda ya faru tunda abokinka ne abunda nakeson ka sani wlh baku isa ba saiya saketa ya zaku mayar damu y'an iska"Wlh bansan abunda yake faruwa ba please Ki daure kimun bayani"a takaice Asmy ta basa labarin takardar da MD ya ba Zarah"Cike da damuwa Jaber ya ce "Subhanallahi ya bloody zaiyi haka Bayan ga Yarjejeniyar da mukayi Kuyi hakuri abun mai sauki ne bari na je gidansa zamuyi magana insha Allahu ko yau ban kiraki ba gobe zankiraki" tsaki Asmy taja tare da katse kiran tana huci Lallashin Zarah ta fara ta ce "Kiyi hakuri sis Wlh basu isa ba abunda bazaiyu ma bane ki kwantar da hankalinki" taya zan kwantar da hankali na Asmy?in kwantar da hankali na fa kikace ?Dan ba ke kika shiga chakwakiyar da na shiga ba shine zakice na kwantar da hankalina ina ni ina kwanciyar hankali Bayan Ban sansa ba "Kuka ne ya k'ara cin karfinta hawayen Dana sani ne suka shiga zuboma Asmy Tabbas duk halin da Zarah ta shiga ita ce sila,Rashin hankali da wautar ta ne ya sanya ta jefa y'ar uwarta aminiya a cikin halin da ta sosai takejin rad'ad'i sa zafi a cikin zuciyarta. Kwance yake ya lumshe kamar mai bacci " Me yasa na kasa sakinta?Ya tambayi kansa "Saboda Baka samu cikar burinka ba na dalilin Aurenta da kayi?wata zuciyar ta basa amsa " Amma kana ganin kayi mata adalci kuwa?wata zuciyar ta k'ara tambayarsa "rumtse ido yayi yanajin zafi da rad'ad'i a cikin zuciyarsa dukda sanyin AC bai hanashi zufa ba zafi yake ji sosai a cikin zuciyarsa na tausayin yarinyar Tabbas na cutar da ita ?To ka saketa mana Indai kana Tausayin halin da zata shiga?Girgiza kai ya fara da karfi ya furta 'I can't bazan iya ba bazan iya sakin ta ba ?saboda me tunda ba sonta kake ba hasalima Auren Yarjejeniya ne kukayi da ita "buga kanshi yayi sosai da hannu idanunta tuni sun sauya kala ga wani irin ciwo da sarawa da kansa yake a rayuwarsa bayason ya cuci wani,baya k'aunar ganin wani cikin damuwa ko wani hali,bare shi ya zama silar shigar wata cikin wani hali yasan shi da kanshi ya zalinci yarinyar muddin bai saketa ba " biro ya d'auko da ta k'ara Yafi sau goma yana son rubutawa amma ya kasa wurgar da biro din yayi Daren ranar MD ya koma kamar wani Mahaukaci bacci ko barawo baiyi shi ba Bangaren su Zarah ma haka ta kasance Dan bacci ko barawo batayishi ba ita da asmy musamman Asmy da take ganin itace duka silar faruwar hakan Inda Allah ya taimakesu ma Chuchu ta tafi weekend Kd bare ta fahimci halin da suke ciki Zarah ko yini daya harta rame sosai ta shiga Jerawa MD Allah ya isa na yaudararta da sukayi "Kasancewar Sunday basa lectures yasa sukayi zaune a d'akin kamar Wad'anda akayiwa mutuwa sunyi jugum zarah na hawaye rungomo Zarah Asmy tayi tare da Fara Lallashinta ta ce " Dan Allah kiyi bacci zazzabi na neman rufeki?ta fad'a tana tab'a jikinta shiru Zarah tayi bata bata amsa ba haka hawaye basu bar zuba daga idanunta ba Dak'yal Asmy ta dinga Lallashin Zarah a jikinta ta samu har bacci ya d'auketa Ajiyar zuciya ta sauke tanajin ba dadi a ranta da ta zama silar shiga damuwar aminiyartata ita kanta idan ta tuna abunda suka aikata a baya saitaji abun kamar a mafarki ko a almara bata tabajin anyi abunda suka yi ba...Wajen 10 Jabir ya isa gidan MD Saida ya jirasa kafin yaga fitowarsa kallo d'aya yayi masa yasan akwai abunda ke samunsa kafinma.su gaisa jaber ya ce "Abunda kayi ka kyauta MD ,me yasa kak'i sakin yarinyar nan bakasan hakan babbar barazana bace a rayuwarta ,me yasa zakayi mana haka ," tsaki MD yaja duk haushin kowama yaji yanayi ya ce "sau nawa zance babu ruwanka a maganar nan?da ruwana waya hadaka da ita?Waye jadalin Auren shine yanzu zakace babu ruwana to da ruwa na wlh baka isa ba zuwan nan da nayi bazan fita ba saida takardar Zarah Ai abun ba hauka bane yarinyar da ka dinga cewa an lakaba ma dalilin me yasa bazaka saketa ba?Cikin daga murya ya ce " ya isa Haka jaber kai ba uba na bane da zakazo kanamun fad'a akan Abunda ya shafi rayuwata saki ne bazan sake ta ba shikenan final magana karka k'ara zomun da maganar nan Aure dai a kaina yake ba akan kowaba Dan haka bazan sake ba please Karka k'aramun Damuwa"mamaki cike da fuskar jaber ya ce "Ni kake fad'awa haka MD " tsaki yaja tare da kauda kai"Murmushi mai ciwo jaber yayi ya ce "Laifina ne duk wannan nagode" yana gama fad'ar hakan ya tashi fuuuu yabar gidan rai bace sai Bayan fitar Jaber MD yaji baiji dadin abunda yayi masa ba abunda basu tab'a samu da abokin nasa ba Kuma yasan fushi yayi "amma ai shi yaja " ya fad'a yana dage kafada "Koda Asmy ta kira Jaber rasa amsar da zai bata yayi Yasan ba k'aramun zalinci sukayiwa yarinyar nan ba da wani ido zai kallesu " Tabbas MD yayi masa bazata bai tab'a tunanin zaiyi haka ba "Amma ai laifinka ne daka bashi wannan shawarar marar tushe da ma'ana shi kanshi jaber ba k'aramun Dana sanin wannan gurbatacciyar shawarar da ya bawa MD yayi ba yana ganin kiran Asmy yake kin d'aukar wayar karshe ma kashe wayarsa yayi Dan baisan abunda zaice musu ba Tashin hankalin da su Zarah suka shiga b'ata bakine cikin kwana biyu harta rame bacci ko Saidai barawo ita da Asmy saina rasa wanene yafi wani shiga tashin hankali koda Chuchu ta dawo weekend ta samesu kallo d'aya tayi musu tasan suna cikin damuwa koda ta tambayesu meke damunsu cemata sukayi ba komai bata Kara tambayarsa ba saboda tasan da abunda Suke boye mata tun watanninan a ranta tace tunda basu d'auke ni d'aya ba Ai shikenan" Jarabawar su Zarah tazo Wanda Dak'yal ta maida hankalinta ta fara rubuta jarabawar Wanda Rabi damuwa tayi mata yawa ta rasa abunda ke mata dadi a haka dai Har suka gama jarabawa Hafiz ko tun a waya ya lura da bata cikin walwala koda ya tambayeta ce masa tayi ba komai a haka dai har suka kammala Jarabawarsu Ta final ranar da suka gama kowa na farinciki zai koma gida Angama school banda zarah da hankalinta baya jikinta yaune ranar graduation dinsu na gama makaranta bata cikin walwala ko Kad'an gidansu Asmy sunzo Inda akayi bikin gamawarsu sch ana ta hotuna ko hoto daya Zarah batayi ba ko kawayenta sun janyota Zamewa take tana zaune sanye da rigarsu ta graduation da ankon material din da sukayi tana tunanin data saba Chuchu tazo tare da kama hannunta tace taho muje tun d'azu nake nemanki zaku gaisa da Ammy a kujerar manyan baki da aka karrama suka iske Ammy sanye cikin shiga ta manya ta alfarma ta manyan mutane idanunta sanye da farin medical glass tana ganin Zarah ta sakar mata murmushi kujerar kusa da Ammy Chuchu ta zaunar da Zarah ta ce "Ammy ga takwarar taki" Kama hannun Zarah Ammy tayi ta ce "Sannu ko takwara " A sanyaye Zarah tayi kasa da kanta ta ce "Ina yini Ammy anzo lafiya" lafiya qalau daughter congratulations ko Angama karatu lafiya Allah ya sanya alkhairi yasa mai amfani ne "Ameen Ammy ngd" ta fad'a a hankali sosai Ammy takeson Zarah har cikin ranta saboda nutsuwarta "Sosai ta dinga janta da hira Wanda Zarah duk nonnokewa take saboda ta