Sashe 82
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Daman ita ce momcy din taki?Gyada masa kai tayi ta ce " Eh ita ce Yaya"ita ce mai muryar nan kenan?Nanma sake gyada masa kai tayi"Maida Kallonshi yayi ga hoton yana mamakin kenan k'awar Chuchu ce da takeji dinnan da ita yayiwa haka sosai Abun yazo mai a bazata yanda bai tab'a kawowa a ranshi ba "Kallon Chuchu ya kumayi ya ce " sunan ta na Gaskiya"Zarah Yusuf yaya ko ka Santa ne Wai"Zarah Yusuf ya maimaita a ransa Tabbas ita d'ince "Kafin ya kalli Chuchu ya ce " ta ina zan Santa Bayan ba tab'a ganinta nayi ba "Eh yaya Amma kagani ko ta had'u sosai ko?Ba Laifi ya fad'a yana Mikewa " binshi tayi ta ce "Yaya ina zaka kuma Bayan baka bani shawarar abunda zanyi mata ba bakace hoton yayi asashi ba "duk yanda yayi miki kiyi amma karkiyi mai hoto ?,binshi tayi ganin ya nufin hanyar stairs ta ce " Yaya Saboda me nafison nayi mata me hoto"Saboda bazaiyi kyau ba da hoto please ki barni na huta "ya fad'a yana hayewa sama Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta koma palour gefen Ammy ta zauna tana d'ora kanta kafadarta ta ce " Ammy wai kinji yaya kar ayi me hoto ko ayi me sunan kawai"Amsar hoton Ammy tayi ta ce "Masha Allah hoton yayi kyau amma kiyi mata mai sunan kawai zaifi watak'ila batason saka hotontane kinsan y'ar tawa ustaziya ce " Murmushi Chuchu tayi sosai takejin dad'in yanda Ammy ke son kawar tata ta ce "To shikenan Ammy wai Kinga da yaya yaga hotonta wlh saida yayi ta Kalla Kinga yanda lokaci guda ya sauya kamar daman ya santa" Murmushi Ammy tayi ta ce "Yanzu ba wannan ba kiyi Sauri ki kira mai jakar kar lokaci ya k'ure " Mikewa tayi ta ce "Barima kawai na tafi da kaina na masa bayani Dan gobe nakeson su iso guda D'ari biyar ai sunyi ko Ammy,?" Ta fad'a tana yafa beil"Eh sunyi please ki dawo da wuri banda gudu da mota a titi"......MD tunda ya shiga d'akin ya rumtiya duniyar tunanin Zarah Bai tab'a tunanin Zarah zata kasance itace kawar Chuchu kuma ita ce mai Qiri'ar wannan data ki barin kwalwarsa "sosai yaji zuciyarsa ta k'ara chunkushewa a halin yanzu baya da buri da yake dashi fiye da na ganin yarinyar tunda suka rabu Baccin kirki baya iyayi batare da tunaninta a ransa Wanda shi kanshi har mamakin hakan yake amma sai ya lakanta hakan da tausayinta ne da yake A ransa ya ce Tabbas wannan babbar dama ce ta sameni da zanyi amfani da ita wajen Gano Address d'inta Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " wannan Karin da Chuchu zanyi amfani"Wayarsa ce tayi ringing Ganin Amera ce Ke kiran ya sanyashi picking baiyi mamakin kin masa maganar kin kulata da yayi kwana biyu Dan yasan indai tana gidansu bata da matsala bataki ya barta tayi wata a gida ba Bayan sun gama waya baice yaushe zata dawo ba haka batace masa zata dawo ba dukda tana son ganinshi. Yau Tuesday Zarah ta tashi da zazzabi kin fad'awa kowa tayi ciki harda Asmy ranar mai lalle tazo dak'yal ta daure akayi mata danma a gidan su Asmy akayi mata ba Mutane sosai sai wasu cousin sisters d'inta na wajen Baba da sukazo Akayi musu tare sosai K'unshin Zarah yayi masifar kyau sai sannan ta fito a Amaryar Washegari Laraba tunda Safe sukaje saloon dukda tana Kokarin nuna ba komai a fuskarta ana cikin yiwa Asmy Bayan Angama yiwa Zarah tana gefe wayarta ce tayi ringing dubawa tayi taga Chuchu ce "Bayan tayi picking daga bangaren Chuchu ta ce " yanzu zantaho sis ki turomun Address d'in gidan idan nazo Funtua wace unguwa zance"Sosai Zarah tayi kokari wajen daidaita Nutsuwarta ta ce "Jabiri Gidan Malam Yusuf Zakice " okay to gani nan insha Allah "Murmushin k'arfin hali Zarah tayi ta ce " Allah ya kawoku lafiya"Bayan sungama wayar angamawa Asmy gida suka wuce tare. <KD> K'aramar akwati chuchu ta zuba kayanta sai murna take yau zata hadu da su Zarah 50k Ammy Ta bata ta kai gudummawarta Dan tace bazata samu halarta ba Bayan ta fito Harabar parking space d'in gidan Driver ya saka mata akwatinta a boot MD ya fito fuska ba walwala "Karasawa Inda yataho tayi tana kamo hannunshi ta ce " yaya yanzu zan tafi daman kai nake nema "yana Kallon motar da zata tafi ya ce" Wani gari ne zaki?Funtua ne Yaya ka manta bikin momcy da na fad'a maka"yaushe ne d'aurin Auran Asabar ne " shine zaki tafi tun yau Dan azarbabi "kamar zatayi kuka ta ce " Dan Allah yaya karkace zaka hana wlh mune manyan kawaye idan banjeba tun yanzu sai yaushe"Dan tasan halinshi sarai sai yace zai hanata "Jim yayi kafin ya kalli driver ya ce " fito da kayanta Daga motar nan zankira Wanda zai kaita "Jaber ya dannawa kira Bayan ya d'auka ya ce " Bloody Dan Allah ba abunda kake yanzu"Daga bangaren jaber yace "bakomai ya akayi" Inba damuwa kazo gidanmu ina son ganinka"Okay gani nan zuwa kana gidan "Eh" Kallon Chuchu yayi ya ce "Koma ciki kafin yazo ya kaiki" To yaya "ta fad'a tare da Juyawa Dan ta lallab'ashi karyace bazata ba ba ayi 30 minutse ba Jaber ya Iso gidan a palourn sa na part dinsa dake gidan suka yada zango..shiru jaber yayi Bayan ya gama sauraren MD Dagowa yayi ya Kallesa ya ce " Allah ne ya kawo mana mafita cikin Sauk'i amma nayi mamakin yarinyar da iliminta da komai zata yarda a d'aura mata Aure kan Aure "Numfashi MD ya fesar ya ce " Ni kaina nayi mamakin ta dalilin sanin ilimin nata bazata yarda a d'aura auren ba Alhalin da igiyar Aure na akanta ya sanya harna rabu da ita kafin Allah ya kawo mana mafita amma kana gani komai na shirin jagulewa"Ai bazaiyu a daura Auren nan ba Tunda muka samu address d'inta ai mungama samun dama Dole ne za a fasa Auren nan "Cewar Jabir "nasan da hakan bazan tab'a yarda A tabka wannan Babban kuskuren ba Amma tayaya kake ganin zamu magance matsalar" Ka barmun komai a hannu na bloody yanzu ba zankai Chuchu garin ba Kuma zangano gidansu ai magana ta k'are"Numfashi mai zafi MD ya fesar ya ce "Allah fitar damu" Ameen bari naje na sauketa kawai kome kenan saina dawo "Gyada masa kai MD yayi yana lumshe ido kan Kujera Bayan tafiyar su Chuchu ya jima yana sake_sake a ransa gabak'i d'aya kanshi ma ya kulle akan Lamarin yarinyar nan lumshe ido yayi kafin ya bud'e ya ce " Allah yasa ta tabbata ciki ne da ita Ya rabbissamawati"ya fad'a yana daga hannu yana rokon Allah ji yayi duk duniya yanzu kuma ba abunda ayake da buk'ata irin yara sosai yaji soyayyar cikin dukda bai tabbarba shi kanshi da akwaishi ko babu Amma zuciyarsa tafi rinjaya masa Akan akwai cikin wayarsa ya lalubo daidai numberta da yayi save da "Mamy" ya dinga kallo kamar kullum sai yayi kamar zai Danna mata kira wata zuciyar ta hanesa Dan yasan har yanzu fushi take dashi lumshe ido yayi a hankali ya furta "Simple babe baki da hayaniya " Kara lumshe ido yayi tunowa da zazzak'ar qiri'arta Da har yanzu idan ya tuno yakanjita a tsakiyar kansa ya ce "Ashe kece mai zazzak'ar muryar nan" Juyar da kansa yayi gefe saikuma ya saki murmushi ya ce "Koya taji.lokacin da ta ga takardar nan" Samun kanshi yayi da tsananin Bukatarta a kusa dashi koba komai irin zaman da sukayi dukda na d'an lokaci ne yana yi masa dadi sosai dabi'un yarinyar da hallayarta yake burgeshi Kara juyi yayi kan kujerar ya bud'e idonsa ya ce "Ashe kece kika k'ara inganta rayuwar kanwata Tabbas baki chanchanci Rashin Kyautatawa daga gareni ba ,dole ne na gyara kuskuren da nayi a baya wata zuciyar tace masa " To idan fa Chuchu suka gane kayi mata haka ya zasuji"tsaki yaja ya ce "Ai ba Laifi na bane Laifin Jaber ne tun Farko daya kawo wannan muguwar shawarar " To me yasa ban Sake ta ba "Wata zuciyar ta basa amsa da " saboda kana tausayinta" "tausayi kamar ya " ya k'ara tambayar kansa "Tausayi irin na musulunci " idan kana tausayinta me yasa da yarjejeniyar auren ku ta kare kak'i sakinta ta auri wanda take sonsa yake sonta "Saboda ina son inganta rayuwarta" Shi wancen sani kayi da har bazai inganta rayuwarta ba "Suk shi daya yake maganganun nan da zuciyarsa "tsaki yaja tare da buga kansa da hannu da karfi ya ce "OH MY GOD" na zauna ina ta tunanin k'aramar yarinya zata chazamun kai ". Jaber yana sauke chuhu ya karema gidan kallo daga mata boot yayi ta fito da kayanta da kuma gudummawar jakunkunan da suke a wata k'atuwar leda zagayowa tayi Inda yake gaban mota bai fito ba ta ce " yaya Jaber Please ka fito ka taimakamun d'aukar akwatin nan wlh tayi nauyi "Harararta yayi ya ce " wannan Dan Abun ne bazaki iya d'auka ba Kice zasu kwana anan"Turo baki gaba tayi ta ce "Shiyasa banso Yaya yace kai zaka kaini ba wlh dan nasan kaima duk kusan halinku d'aya" Dariya yayi ya ce "Kome zakice kice " Tana shirin sake magana ta Hango Asmy ta fito daga gidansu ta nufo Inda take jaber na ganin asmy gabansa ya tsananta fad'uwa karta zo ta ganesa asirinsu ya tonu wajen Chuchu Dan yasan Sarai Asmy ba control gareta ba cikin Sauri bai saurari Chuchu ba yaja motar da karfi tare da saurin barin arear da Kallo Chuchu tabi motar Kafin ta tab'e baki Rungume juna sukayi da Asmy suna murnar ganin juna kafin Su wuce gidansu Inda Zarah take da gudu Suka Rungume juna suna Daukin ganin Juna Sosai Zarah ta d'an wartsake Dan tayi murnar ganin kawar tata sosai aka karrama Chuchu a gidansu Asmy fiye da tunanin mai karatu da dare yayi ma anan suka kwana Dan Zarah batason zuwa gidan su taro ya fara yawa washegari gidansu Zarah suka wuce sakamakon yawan nemanta da dangin babanta suke d'akin Zarah suka yada zango sosai Zarah ta nunawa Chuchu taji dad'in gudummawar jakunkunan da akayi gudummawar Ammy kuwa kin amsa tayi ba yanda Chuchu batayi da