← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 129

Sashe 30

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tunani tukun" ta na gama fad'ar haka tabar office d'in gabanta na fad'uwa "kawayenta ne hibba Da Jamcy da suka rakota suna ganinta sukayi kanta hibba ta ce " Lafiya me ya ce maki naga kin fito a rikice kinsan mutumin nan ba mutuncin kirki ya isheshi ba"Ajiyar zuciya Zarah ta sauke tare da cewa "Kudai kawai muje wlh abun yaban mamaki wai mutumin nan zaice ya na sona" wara idanu sukayi a tare suka ce "so " Sai Kuma hibba tayi Dariya ta ce "chab Wlh ki amince masa idan ba haka ba Zai Kadake a last paper baida mutunci wlh kuma d'an iskane na Bugawa a jarida haka sukayi Da wata budurwa yayata ta na bani labari daga tak'i amince masa wlh Ya kada ita a last paper kuma da gangan Dan Ance kokari gareta" wara idanu Zarah tayi ta ce "Na shiga ukku kuma shine kike cewa Na amince masa Bayan kinsan d'an iska ne " jamcy ce ta dafa ta ta ce "Karki damu ai ba kowa ake Kalla ayima zancen iskanci ba yanzu dai fad'a mana yanda kukayi dashi...nan ta basu labarin yanda sukayi hibba ta ce " To wlh tunda kikaji ya ce Aurenki zaiyi ki rabu dashi bazai maki zancen banza ba sannan kuma yana ganinki amerar makaranta kinsan ance d'an iska baya Auren y'ar uwarta y'ar iska Shima tagari yake nema wlh da gaske yake Dan tun sanda ake lecture na lura da irin kallon k'urullar da yake maki nasan sonki yake ki rabu dashi kawai kuyi soyayya "tab'e baki Zarah tayi ta ce"Bama sai Inda ya k'ara gani na ba.....Koda Tabawa su Asmy labari suma irin yanda Su hibba suka fad'a mata haka asmy ta bata shawara ita dai jinsu kawai take Amma batajin zata iya soyayya da wannan Bayan akwai baikon Aurenta da Hafiz (Nikam nace again kuma ga auran md akanki)Chuchu kuwa cewa tayi"Karki biyeshi momcy bazai kada ke ba Inma ya kada ke ai akwai Allah Duk mutumin da Akace Dan iska ne kaji tsoransa kinganninan bana k'aunar Dan iska shiyasa ko huld'a banayi dasu tunda nazo makarantar nan ba kowa nake abota dashi ba Saboda tsaro ku kadaine zance aminai na kuma Dan na yarda daku 100% na tabbatar kudin mutanen kirki ne kuma tare na daku na k'aru da abubuwa Dan haka Ina baki shawarar kawai kice masa an sanya miki Aure a wuce wajen"Zarah ta ce "Daman Chuchu duk jinsu nake wlh shawararki ita ce shawarar kirki sai sannan Asmy ta ce " Kuma fa hakane "a zuciyarta Asmy ta ce " Astagfurillah to ya matsayin Auren nan na Zarah yake a musulunce laifi ne tayi mu'amula da maza"wata zuciyar ta ce "Mata ai Aure duk Aure ne ko wayar da take Da hafiz haramun ne" Sosai taji gabanta ya bada daram Zarah ko bata tab'a kawo wani Aure a kanta ba harkar gabanta kawai take Dan mancewa ma take da wani Aure a kanta Dan bata d'auki Auren Aure ba dukda ta na da ilimi....Yau Zarah ta shirya tayi kyau sosai Cikin doguwar rigarta Abaya Black mai shegen kyau hijab ta d'auko zata sanya Chuchu ta rik'e hijab tare da cewa "Haba Momcy kici gayun nan ki sanya hijab Allah ban yarda ba gyale zakisa ai ba matsatsun kaya bane sannan Ko larabawa ai sanyawa suke har suyi salla ma dashi please ki yafa gyalen wlh sai kinfi kyau" Badan Zarah taso ba dole ta yafa gyalen nanko Chuchu ta shiga koda da tana cewa "Wow Momcy wlh kin hadu yanda kikasan wata first Lady taho muyi hoto ta fad'a tana shiga snap" Murmushi kawai Zarah tayi nan ta shiga kashe musu hotuna masu kyau chuchu ce ta ce "Wlh momcy karkiga yanda kikayi kyau aikedin Matar manya ce wlh ba yara ba da yaya na kika dace bada kowaba" Harararta Zarah tayi ta ce "ba nace ki daina had'ani da Yayan naki ba ni ta Hafiz ce ta fad'a tana mata far da ido" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ki dai bar cika baki kika sani ma ked'in ko rabon Yayan nawa ce Saikiga Hafiz dinma ya mutu" Wara idanu Zarah tayi tare da Kai mata Dukan Wasa a baya ta ce "Ta Allah ba taki ba muguwa Ya Hafiz dina bazai mutuba sai yaga ma Auren jikokinmu" Dariya Chuchu tayi ta ce "Ah su jikoki manya sai mu gani Har na hangoki gidan yayana " Sanin Zarah ta biyewa Chuchu sai ta fasa fitar ya sanyata girgiza kai kawai ta fita ta ce "Dan yanzu Sauri nake ai zan dawo tare da fita daman Asmy ta fita yi musu chefane kai tsaye napep ta Tara Inda ta fad'a masa sunan unguwar da zai kaita kamar yanda Dr Halima ta turo mata sunan unguwa ta na isa Ta kirata ta ce " Aunty na iso nan tayi mata kwatancen Inda take"Dr Halima ta ce "okay ga yarinyata nan zata zo ta taho dake" Zarah na nan tsaye taga wata yarinya da bazata wuce sa'ar khairat din gidansu ba Ta na ganinta ta gane y'ar Dr Halima ce saboda kamar da suke Yarinyar ta gaishe da Zarah ta amsa mata da murmushi Tare da kama hannunta har suka Isa gidan Cikin mutuntawa Dr Halima ta tari Zarah tare da cewa"oyoyoyo Amarya Yau dai Allah yayi Gaki a gidana "Murmushi Zarah tayi tana zama ta ce " ina yini Aunty munsameku lfy"Alhmdllh Zarah ya kwana da yawa kin bace ko ya amarci"Murmushi kawai Zarah tayi ta na kasa da kanta kafin kace me an cika mata gabanta da abubuwa har mamaki tayi irin tarbar da aka mata Inda Dr Halima ta tsareta saida ta cicci wasu sosai Zarah ta yaba da kirkin Matar wajen magriba Zarah ta ce mata zata tafi sosai Dr Halima ta cikata Da abubuwan Arziki su turarruka masu kamshi sai Godiya take mata akan ziyarar da ta kawo mata ita dai murmushi take har waje ta rakota tare da cewa"A dai cigaba da hakuri Zarah zaman Aure d'an hakuri ne Sannan ki dinga yiwa mijinki biyayya Allah babu ruwansa da bakyason Auren zai kamaki da laifin hakkin mijinki muddin kina tauye masa"da mamaki Zarah ta d'ago ta na kallon Dr Halima gabanta na fad'uwa ta ce "Dr kina nufin kinsan komai " Ganin yanda ta rikice lokaci guda ya bawa Dr Dariya ta dafa ta ta ce "Baki d'auke ni y'ar uwa ba kenan ina son ki daukeni yar uwa a garin Nan kamar yanda dr aliyu ya fadamun bakisan kowa nan garin ba Aure ne ya kawoki sannan shima mijin aiki ne ya kawoshi garin Zarah Ai Dr ya fad'amun komai ya ce " Auren ne bakiso shysa ma ranar Har hakan ta faru kiyi hakuri ki zauna da mijinki lfy kinji kanwata "Boyayyar Ajiyar zuciya Zarah ta sauke a zuciyarta ta ce " Dr d'innan Allah ya hore masa iya tsara karya Munafiki da Aikin lawyer ko jarida ya dace bada Asibiti ba a fili kuwa murmushi tayi ta ce "Insha Allahu Aunty ki koma zan samu abun hawa" To nagode a gaida mai Gidan nima saina shigo gidan naki insha Allah"sannan ta mik'a mata 500 tace gashi kiyi abun hawa"Kin amsa Zarah tayi ba yanda batayi da itaba amma taki amsa Cikin unguwar taci gaba da tafiya Dan bataga Alamun samun abun hawa nan kusa ba ga kiraye kirayen magriba da Aka fara tana cikin tafiya Taji parking d'in mota bayanta bata waigaba saboda a matuk'ar firgice ta ke "keeeee" Ta ji anfada Wanda ya tabbatar mata da ita ake da wata zazzak'ar murya Saurin Juyawa tayi Ganin fuskar da bazata tab'a mantawaba da ita ba a rayuwarta ya sanya gabanta fad'uwa tare karawa saurinta volume Binta yayi yana kiran keeeee amma bata waigo ba Zarah batayi aune ba saiji tayi anyi charab an d'auketa wutsil wutsiltu ta fara tana yagushinshi tuni hawaye harsun wanke mata fuska ta ce "Meye haka Malam ka ajeni " Baimasan tanayiba bai direta ko ina ba sai Gaban mota tare da rufewa ya zagaya tashiga driver sit ya tada motar a guje yabar wajen.....✍🏿 _Ki saya da zuciya daya y'ar uwa Dan girman Allah kar a fitarmun da Littafi kud'in karantawa kuka biya ba na mallaka ba_ *07026166536*
Chapter 30 · 0% Book details