← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 129

Sashe 104

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

din " Murmushi Zey tayi tace Alhmdllh Auta "ina su Mimi" Ta tambayeta"Suna gida Ana musu lesson shiyasa bantaho dasu ba dayake ba jimawa zanyi ba "ayya naso ganinsu Ina Tsarabata" Tana Chan kije ki amsa da kanki kinsan dai ba kawo maki zanyi ba y'ar rainin hankali ina yayarki a gari amma saikiyi watanni bakije Inda nake ba ni bama wajenki nazo ba wajen Auntynmu nazo"Dariya Chuchu tayi sai sannan ta kalli Chuchu da ta Aje qur'anin ta ce "momcy ga fa Aunty Zey yayatace daga yaya sai ita saini" Murmushi d'auke da fuskar zahra ta ce "Ina yini" Cikin fara'a zey ta ce "Lafiya qlau momcyn mu ya jiki" Alhmdllh "ta fad'a kasa_kasa" masha Allah Allah ya k'ara sauki bari na wuce saina dawo ina Sauri"Murmushi Zarah tayi ta ce "A gaida gida Kallon zahra Chuchu tayi ta ce " ina zuwa momcy bari na raka aunty"gyada mata kai tayi"Suna fitowa Zey ta kalli Chuchu ta ce "Wlh yarinyar tayimun ji nutsuwa da hankali gata da kyau masha Allah jifa duk yanda ciki kesa ayi muni Amma ita kyanta na nan " Dariya Chuchu tayi ta ce "Ai da tafima haka kyau wlh Aunty bari ta haihu kiga ta koma asalinta " Har suka Iso palour Zey na yaba zahra Zaunawa tayi gefen Ammy ta ce "Wlh Ammy Yaya ya rasa wannan ya yi Babban rashi da asara Dan wlh bazai samu kamarta ba Dan Allah Ammy karki yarda Su rabu Tunda gashi hada rabo tsakaninsu" Harararta Ammy tayi ta ce "Ke daman ai Chan bakinku d'aya babu ruwanki da duk hukuncin da zan yanke dole ya rabu da ita tunda ba kaunarta yake ba jira nake.kawai ta haihu na amayar da duk abunda ke cikina a kansa " Jan bakinta Zey tayi shiru ta ce "Amma Ammy sainakega kamar ba yaro d'ayane cikinta ba jifa girman cikin yakamata ayi scanning asan meye cikin Dan mufara sayayya kar wuri ya K'ure Dan daga gani ta kusa" Nasa Dr yayi mata scaning Nasan komeye ciki harma na sanya ayo order kayan daga Dubai jibi ma zasu iso "Ammy nawane?basaikinji ba ta haihu kingani" Marairaicewa Chuchu tayi ta ce "Dan Allah fad'a mana nima inason na fara sayayyar kayan baby" Jin haka ya sanya Ammy cewa "Triplet ne amma Karku fad'awa kowa koshi ko ita kada Wanda Naji kun fad'awa" Sosai suka Zarah ido a tare sukace y'an Ukku Ammy"Dariya Ammy tayi ganin yanda sukayi Chuchu ta buga tsalle ta ce "Wayyo Allah dadi wlh Ammy karkiji yanda na k'agara Momcy ta haihu naga jinin yaya wayyo Allah y'an Ukku a gidannan" Zey ko hamdala tayi ta ce "Allahsrk yaya Double Allah yayi masa Ammy Banmasan wani irin farinciki nake cikiba" murmushi d'auke da fuskar Ammy tace "baku kaini farinciki ba Zey ranar da aka fad'amun kwana nayi ina Godiya da Allah Dan al'amarin nan gaba d'aya ikon Allah ne Amma Karku fad'a musu Kuyi sayayyarku kawai" Insha Allah Ammy bazasuji ba "Tundaga ranar Zey tahau uwar sayayyya komai Ukku takanas ma kawarta takira dake Paris tatura mata kudi akan tayi mata sayayyar kayan jarirai na triplet yawan kudin ma data tura mata saida nayi mamaki yanda kasan ita ce Zata haihu cikin sati uban kayan suka iso akwai kusan goma banda abun goyon jarirai na ciki irin na turawan nan shima komai ukku Chuchu ma Sosai take jibgarta sayyya itadai zahra nata ido bata tab'a tanka mata akan sayayyar dataga tana lubgowa ba Ammy ko ba amagana Dan har kekunan wasa yara saida ta sayo daki guda ta ware ta cika kayan jarirai dashi da gadon kwanciyarsu keken koyon zama kai komai Wanda wani ma baka tab'a ganinshi ba saida Ammy ta had'o mai gayya kwa mai aiki kwata kwata hankalinshi baya jikinshi baimayi tunanin fara wata sayayya ba duk yanda yaso koda ganin Zahra Ammy ta kasa ta tsare bangaren zahra ba laifi zaman gidansu Chuchu yayi mata dadi saboda wata irin kulawa da suke bata a halin yanzu cikin zahra ya shiga watan haihuwa sosai Ammy da Chuchu suka ninka kulawar da suke bata kaffa kaffa suke da ita sosai dan sosai Ammy ke tausaya mata nauyin cikin yara Ukku ba wasa yau zahra tunda ta tashi takejin sauyi tattare da ita Hakanan dai ta daure batare da ta nuna komaiba tun safe tun tanajin Abu Kad'an har yazo yayi yawa Sosai take zufa a d'akin tana yarfe hannu tuni ta fara fita hayyacinta sunan Allah kawai take Ambata a haka Chuchu ta shigo ta sameta tana ganin haka a d'imauce ta ruga wajen Ammy ta ce "Ammy kizo kiga yanda momcy take zai zufa take kamar ta mutu" ba shiri Ammy ta mik'e ta sanya hijab d'inta ta ce"inaga haihuwarce tare suka koma d'akin Inda suka tarar da Zarah na murkashi Sannu Ammy tayi mata tare da kamata ta kalli Chuchu tace "yi Sauri D'auko hijab d'inta Da Sauri Chuchu tasa mata hijab tare da takalmi su biyu suka kamota har wajen motoci Inda Chuchu ta kwalawa driver kira ba shiri yatado mota Tare suka shiga su Ukku Chuchu dukta rude asibitin mafi kusa dasu suka nufa da ita Inda suna isa aka wuce labour room da ita zirga zirga kawai Ammy take da Chuchu Sosai zahra take karb'ar wuta tayi awa guda tana wahaltuwa sosai takejin wata irin azaba da tunda uwar da ta haifeta bata tabajin irinta ba D'aya Daga cikin likitan d'aya duba ta ya fito ya kalli Ammy ya ce " A Gaskiya Hajiya Kuyi hakuri Ayi mata cs bazata iya haihuwa da kanta ba sakamakon Rashin bud'ewa da batayi ba na Auna bata Inda zata iya haihuwa Inma akace dole saita haihu da kanta Gaskiya zata wahala over sannan abunda ke cikinta Shima zai wahala"Innalillahi Ammy ta fad'a ji take kamar ta fashe da kuka ta ce "Dr Kuyi mata Cs din kawai Kar wani abun ya sameta" Chuchu ko kuka ta fashe dashi Okay "Zamu shirya yi mata yanzu amma ana buk'atar ganin mijinta da mahaifinta da Susa hannu" Ba matsala dr ku shiryata yanzu mijin nata zaizo saiya wakilci nbaban nata tunda emergency ne cikin Sauri Ammy ta kira MD Cikin tashin hankali ta ce "Ka sameni a asibiti" Bayan ta fad'a masa sunan asibitin ta kashe ba ayi 20 minutes ba saiga MD yazo afutatan wajen Ammy ya nufa ya ce "Lafiya ammy" Da sauki Zahra ce Zata haihu muka kawota sunce bazata iya haihuwa ba sai anyi mata cs shine muke buk'atar sa hannunka"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Ammy yanzu tana ina Ina ne za a sa hannun"Sosai MD ya rikice ya rude Shi ya sanya hannu kuma shi ya bada jininsa kasancewar group o garesa suna gani aka shiga Theater room da zahra sosai Chuchu ta fashe da kuka Ganin kamar zata rasa kawartata Ammy ma hawaye take tana addu'ar Allah sa ayi aikin lafiya MD ma addua kawai yake hankalinshi a matuk'ar tashe yake "Ba ayi 30 mminutes ba sukaga fitowar dr D'auke da jariri a hannu fuskarshi d'auke da Fara'a suna ganin haka suka Kallesa Ammy ta ce " An sauka"Alhmdllh Dr ya fad'a yana mik'a mata jaririn"Amsar jaririn Ammy tayi "Allahu akhbar Allahu akhbar" kawai Ammy ke fad'a ganin yau ita ce rik'e da jinin MD a hannunta shiko gogon har yanzu gaba d'aya hankalinshi yana kan ga wani hali zahra ke ciki Nurse biyu suka ga sun Kara fitowa rik'e da wasu jariran a hannu"sai sannan MD ya kusa daskarewa ganin sun nufo su da Yaran Daya daga cikin nurse ta mik'awa MD.jaririyar ta ce "Congratulation Sir Allah ya raya" d'ayar kuma ta mik'awa Chuchu da itama ta daskare a wajen Kallon y'ar MD Yayi ya kalli sauran yaran dake hannun Chuchu da Ammy kamar Wanda bakinshi yayi masa nauyi ya ce "Kuna nufin Duka yaran nan aka ciro kuma Duka nawa ne" Murmushi nurse din tayi ta ce "Triple ta haifa gasunan Allah raya "farincikin da MD ya shiga fadarsa bata baki ne ji yake tamkar a mafarki wai yau shine Allah yaba yara har Ukku baisan lokacin da wasu hawayen farinciki suka zubo masa ba ya goge ya ce " Alhmdll.......✍
Chapter 104 · 0% Book details