← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 129

Sashe 4

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan Malaman suka bawa Zarah kyaututtukan da ta samu duk a emblem ne wasu Ba yanda batayi ba akan malaman su rik'e sukace a a a nata ne Sosai Malaman sukeson Zarah saboda kwazo da kokarinta Tabbas Zarah tabar makarantar zasuyi Babban rashi Dan duk musabaqar da ta tashi da ita ake turawa kuma ita ke ciyo musu na daya.

Bayan sun taho daga Makaranta kai tsaye gidansu Asmy suka nufa a kofar gida Zarah ta tarda Baba Dan ya rigasu tahowa Wajenshi suka nufa Kallonsu yayi ya ce "Allah yayi muku albarka Zarah ked'in y'a ce ta gari da kowani uba zaiyi sha'awar kasancewar ki y'arshi ina matuk'ar alfahari dake Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari mai tausayi da jin k'ai".

murmushi Zarah tayi tanajin dad'in addu'ar Baba ta ce "Ameen Baba nagode mik'a masa kyaututtukan da ta samu tayi " nan ya shiga d'agawa emblem na farko kud'ine tsabarsu dubu Hamsin na biyu kuma turmin atamfa na Ukku alqur'an ne sai sallaya a ciki da charbi"Cikin fara a Baba ya ce........✍🏿

Ga masu buk'atar a tallata musu hajarsu su tuntub'eni akan number wayata kamar haka 07026166526
Ko masu buk'atar shiga grp sharhi ko tambaya hanya a bude take

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

💑 *AUREN WATA TARA* 👨‍❤️‍👨

MALLAKAR

*Hajara L Sadeq*

🅿️.........*5 & 6*

"Masha Allah natayaki murna y'ata Allah sanyawa karatunku albarka "

Ameen suka fad'a ita da asmy Mik'a mata kyaututtukan Baba yayi da niyar ta amsa.

"girgiza kai tayi ta ce " a a a Baba banason komai a ciki komai na sama na sameshine ta dalilin tarbiya da jajircewar da kayi a gareni ".

girgiza mata kai yayi ya ce " na sani Zarah ta amma Bazan amsar miki Komai ba nasan kina da buk'atar abubuwa da dama bakya tambayata Dan haka ki biya bukatunki dasu .

"Girgiza kai tayi ta ce " a a Baba wlh bana buk'atar komai kafini bukatarsu Dan Allah ka amsa ".

Duk yanda Zarah tayi Baba ya amsa kin amsa yayi saida Asmy tasa baki dak'yal ya Anshi Dubu ashirin Inda ya mik'awa Asma'u sauran kudin ya ce "

"Amshi ku tafi Sannan ya kalli Asmy ya ce "kiyiwa mamanki Godiya kice nagode Allah ya saka da alkhairi Tabbas Saratu ta cika y'ar mutunci kuma ta cika Alkawarin aminiyarta mariganyiya Kinga yarinyar nan saboda kawaici bata fad'amun akwai maganar Anko ba Allah sarki ashe har tayi muku saida safe take fad'amun angode Allah bada lada".

Murmushi Asmy tayi ta ce "To Baba " Barwa Baba sallayar sukayi tare da Qur'an din Inda suka koma gidan su Asmy sai tayasu murna ake nan y'an uwa da abokan arziki suka shiga shigowa tayasu murna da Yamma suma sukayi y'ar k'aramar walimar su Wanda mamansu Asmy ce ta shirya hakan.

Bayan magriba isha'i Asmy ta kalli Zarah ta ce "Wai kudinnan sis me za ayi miki dasu" ki bawa Mama kawai ni ba abunda zanyi dasu"Mama ce dake jinsu ta ce "Har ance babu abunda za a yi da kudi Zarah zandai Aje miki " .

Girgiza kai Zarah tayi ta ce "Mama Dan Allah ki rik'e wlh babu abunda zanyi dasu ke ai tamkar uwa kike a gareni Dan Allah Mama ki rike " .

girgiza kai Mama tayi ta ce "a a fa Zarah Aje miki kawai zanyi karki k'ara cewa wani Abu "

shiru Zarah tayi badan taso ba Dan a abunda maman asmy take mata ko jininta ce ita sai haka .

"Asmy ce ta ce " Mama babansu zarah yace nayi maki Godiya "girgiza kai tayi ta ce "

" Ai Tsakani na dasu ba Godiya Komai nayiwa Zarah Ban fad'i ba irin zaman mutuncin da mukayi da mariganyiya da amintar da mukayi a lokacin bamu da hali amma Matar nan bata ci banci ba akwai lokacin da saimun kwanta bacci haka zata buga mana gida na bud'e naga abinci ne ta kawomun a lokacin muna cikin wani hali da haka zamu kwana bamuci ba muna halin Rashin babu Amma Matar nan bata tab'a cin Abu Bancishi ba Munyi zama na amana da mutunci da mahaifiyar Yarinyar nan ".

Goge hawayenta tayi ta ce Har yau idan ina tuno da zahara'u bazan daina kukan rashinta ba mace mai kirki hakuri da juriya Allah dai ya jikanta yasa ta huta".

Sosai sukayi sanyi Cikin k'asa da murya Zarah ta ce Ameen ganin ta na shirin yin kuka ne ya sanya Mama barin maganar tare da kama musu hirar duniya Har ta samu ta d'an warware

Bayan sunci abinci Cire kayanta Zarah tayi tare da sanya rigar baccin Asmy Dan daman nan gidan take Aje sabbin kayanta saboda su Habiba suke lalata mata su sanye mata kuma bata isa tayi magana ba hakan yasa take ajewa gidansu Asmy .

nan gidan kawai take samun walwala da farinciki Sai wajen 10pm ta wuce gidansu har bakin kofar gidan Asmy ta rakata tukwana ta Koma Zarah koda ta shiga Zaune ta tarar da Mama Rabi na girgiza k'afa tana ganinta ta taso tare da Wanke da Mari Dan da bakincikin kyaututtukan da akace Zarah ta samu ta yini hakan ya sanyata huce haushinta na dalili marar ma ana da tushe nan tahau dukanta tana bala i tana cewa .

"Y'ar iska tun safe rabonki da gidan nan Sanadin mutane su dinga zagina suna kin lalace a hannu na Bayan duk yanda zanyi inayi iya kokari na Amma kullum baki da aiki sai jamun Zagi cikin unguwa Itakuma saratun in gidanta zaki koma saitazo ta daukeki Dan kazar kazarta kuma daga yau bazaki kara fita ba daga gidan bare ki fake da islamiya na kara ganinki gidan saratu wlh duk tsiyar da na shuka maki ke kikaja shine kikayi zaune gidanta yau babu aikin da kikamun uban wani kike tunanin zai maki aikin gidan Dan matacciyar uwarki " .

Zarah kuka take sosai ta durkushe tana bawa Mama hakuri anma bata Rabu da itaba da hannu take jibgarta Baba ne ya shigo tun a soro yaji kukan y'ar lelen nashi .

cikin b'acin rai Baba ya shigo Tare da wanke Mama Rabi da Mari cikin b'acin ran da idan kaga yayishi tofa rai ya b'aci ya ce "Duk iskancin da kike kikaga ina kyaleki ba tsoronki nake ba Rabi gudun tashin hankali ne me marainiyar Allah tayi miki da Zaki hauta da duka daman an fad'amun irin zalincin da kikewa yarinyar nan idan ba Dan kin sameta mai hakuri bata fad'amun shiyasa kika maida ita jakar ki to hakuri na ya fara kaiwa Bango daga yau Zahra'u bazata sake Wani aiki a gidan nan ba su d'iyanki aikinme suke idan bazasuyi aikin ba gidan ya rube karewar kazanta kumasannan daga yau Kika Kara d'aga hannu kika daki yarinyar nan kin daki igiyar auranki a bakin aurenki"

Nuna kanta Rabi tayi ta ce "Ni kake fad'awa haka Malam " Amfad'a maki ko akwai abunda zaki iya"jinjina kai tayi ta na girgiza k'afa na borin kunya Dan Malam bai tab'a mata haka ba tasan yakai bango Har ya iya d'aga baki ya furta mata a igiyar Aurenta tofa ya fara gajiya da ita hakan yasanya ta yin lakwas Dan Tasan ta rabu da Malam asirinta ya gama tonuwa Dan duk cikin mazajenta biyar da ta aura babu mai hakurin Malam bazata tab'a yarda Auransu ya lalaceba

wucewa ciki tayi kamar zata tashi sama Baba ko Kallon Zarah yayi ya ce "Tashi ki shiga kici gaba da hakuri kinji wataran sai labari " Mikewa Zarah tayi ta ce "Toh Baba nagode " tare da shiga d'akinta tana hawaye har bacci ya d'auketa.

Washegari koda ta tashi bata sa ran Bata abinci ba Ta na nan zaune wajen 10 koda ta lek'a ta tambaya ina abincinta Da masifa Mama Rabi ta korota ta ce Daga yau bazata k'ara cida ta ba Tunda ubanta ya hanata ta girka to itama bazataci shi ba ta nan zaune ta na hawaye taga shigowar Asmy dakin maza tayi ta goge hawayenta Murmushi suka sakarwa juna "Zarah ta ce

" yanzu nake tunaninki Besty"wlhko nima tunaninki ya sanya na taho ta fad'a tana zaunawa gefen katifar da take kallonta tayi ganin yanda fuskarta ta kumbura Alamun Tasha kuka kamata tayi ta ce "Mai ya faru Besty " kirkira murmushi tayi ta ce "Bakomai me kika gani"?hmmm karkiyimun karya Zarah ina gane halin da kike ciki ko baki fad'amun ba nakanji a jikina fad'amun meyake faruwa "

nan Zarah ta fad'a mata abunda ke faruwa Mikewa asmy tayi tare da dura ashar ta ce "Wlh iskancin Matar nan yayi yawa bari zan gwada mata ni y'ar zamani ce “

" ta fad'a tana niyyar fita kamota Zarah tayi cikin Sauri ta ce 'ki Rufamun asiri sis Dan Allah karkije ki k'ara jamun ni komai tayimun na barta da Allah .

dak'yal Zarah ta samu Asmy ta hakura Kama hannunta tayi ta ce "Taho muje gida ki karya " tare suka fito " Mama Rabi ta bisu da harara da tsaki suna isa gidan su asmy nan Zarah ta karya Dan tare suka shiga kitchen suka dafa indomie Bayan sun karya gadon d'akin asmy suka kwanta Dan su huta daman Zarah da gajiyar jiya bata saketa ba Aiko kafin kace me bacci yayi awon gaba da ita itace bata tashi ba sai wajen Azahar
Chapter 4 · 0% Book details