← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 129

Sashe 73

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

rasa dalilin da yasa takejin kunyar Matar chuchu ce ta ce " Ammy amarya ce fa Bikinta za ayi Dasun koma gida nasandai zaki barni nayi sati a Chan"cikin fara a Ammy tace" Kai kai ashe amarya ce y'ar tawa to Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya insha Allahu ai ko nima zan halarci bikin da yardar Allah "cike da jin kunya Zarah tayi kasa da kanta gabanta na fad'uwa tuno mata da bikin da akayi " Dariya Chuchu tayi ta ce "Ammy kunyarki takeji fa" hararar wasa Zarah tayi mata Ammy ta ce "wai takwara ai ko da baki kyauta mun ba keda ya kamata ki saki jiki dani ai munriga munzama d'aya Kinga zoma ki mana hoto a wayarki" Ammy ta fad'a tana kamo hannun Chuchu"sosai Chuchu tayiwa Ammy da Zarah hotuna masu kyau kamar y'a da uwa mutane sai kallonsu suke suna gulmar ko me ya had'a Zarah da uwar MD Wanda suka San chuchu saisuce dayake kawarta ce shysa Bayan Chuchu ta gama musu hotunan wata kawarsu taba wayar ta d'aukesu su Ukku sosai aka musu hotuna masu kyau kafin Ammy tace ta gaji zata tafi "Bayan Angama duk abunda ya kamata Inda aka shiga karrama dalibai Wanda Zarah tana d'aya daga cikin daliban da aka karrama sosai bikin yaye daliban yayi kyau fiye da tunanin mai karatu Lokacin da Ammy zata tafi s s d'inta mace a bayanta tana take mata baya Chuchu da asmy da Zarah ko sosai suka Rungume juna suna kukan rabuwa Dan ba k'aramun sabo sukayi ba " Ammy ce tace "ikon Allah to ku ya haka saikace Wanda zasuyi nesa da juna to tunda bakusan rabuwa ni ku taho mutafi daman neman y'an mata nake Kunga saikuje Chan a cigaba da kawancen" Maman su asmy ce da tin dazu suka gaisa da ita ta ce "Gaskiya kam Hajiya Saisu runkuta su tafi" Dak'yal suka rabu sunajin ba dadi a ransu Danma sunyiwa juna Alk'awarin ziyartar juna a kai a kai a mota Chuchu ta lafe jikin Ammy tana turo baki ta ce "Ammy nayi fushi da yaya ranar graduation dina guda amma yak'i zuwa" Shafa kanta Ammy tayi ta ce "Kiyiwa Yayanki uzuri Maryam kwanakin nan ni kaina bana gane masa ya zama wani iri ina tsammanin tunanin Abunda Hajiya ta fad'a ne yasan tana gab da zuwa shiya sanyashi cikin damuwa in banda abun babana meye abun damuwa a Aure Kuma Aurenma zab'i aka baka na rasa abunda ke damunsa akan yarinyar nan Amera bana gane masa yanzu haka tafi wata biyu bata k'asar shi yana nan a haka wai zaman Aure ne fisabilillah dandai karkayi magana ace kaima kana da y'ay'a mata saita zauna ta dinga abunda take so "ai Ammy wlh laifinki ne tsorantafa yakeji idan kika tilasta kika nuna masa b'acin ranki ba dole yayi Auren ba karkiji irin yanda nakeji idan na tuna da yaya wlh Rashin mata ta gari babbar illa ne ta Riga ta lalata rayuwar Dan uwana ni kad'ai nasan irin zafin da nakeji a raina yaya baiyi dacen Aure ba ammy" murmushin da yafi kuka ciwo Ammy tayi ta ce "Ni kadai nasan irin yanda nakeji a cikin Raina Maryam nidin uwa ce Addu'a kawai zan Kara dagewa da masa Dukda kullum cikin masa nake kema ki raya Yayanki da addua".... A sanyaye Zarah ta shiga cikin gidansu Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba Mama Rabi tsakar gidan Sai Baba yanajin radio cikin farinciki da murna Baba ya tari y'ar tasa ba irin albarka da bai sanya mata ba. Sosai ya nuna mata jin dadinsa na kammaluwar karatun nata lafiya sannan ya bata hakuri akan Rashin halartarsa wajen " Murmushi tayi ta ce "Bakomai Baba wannan Karin Mama Rabi batayi alkaba'in da take yiwa Zarah ba saboda ganin Baba a takaice ta amsa gaisuwar da tayi mata Bayan Fitowarta daga d'akin Bayan Zarah ta huta Tayi wanka da dare Baba ya sanya aka kirawota Bayan ta zauna kallonta yayi ya ce " Zarah yau zan baki wasiyar da mahaifiyarki ta bani dukda na fad'a maki na adana maki ne har zuwa lokacin da ta wa'adanta watau lokacin Aurenki Alhmdllh yanzu ne lokacin da ya kamata na baki"Ya fad'a yana mik'a mata Awarwaron da zobanyar da ya sanya cikin k'aramun box hawaye ne suka zubowa Zarah tare da amsa sosai taji k'aunar awarwaron da zoben kuma tayiwa kanta alk'awarin kula dasu kamar ranta "Allah ya jikan mahaifiyarki yasa tana cikin Rahama " Ameen Baba"Zarah ta fad'a kafin ta ce"D'an Allah Baba kana da hoton Mamana ko d'aya ne?Yanajin tausayinta a ransa ya ce"Banda hoton mahaifiyarki Zarah ni kaina Inajin Haushi Rashin hotonta da bani dashi a lokacin bamu damu da hoto ba Tunda muka hadu da ita batayi wani hoto ba Saidai nakanji dadi idan na kalleki ked'in hoton ta ce Zarah idan kinason Kallon fuskar mahaifiyarki to ki kalli kanki ita zaki gani wani gamin idan ina kallonki sainaji kamar mahaifiyarki nake kallo saboda har zubin jikinki ba banbanci da nata sannan a lokacin ma da ta rasu Bazata wuce shekarunki ba kamar yanda kike d'innan har abun nan na gefen bakinki da suka lotsa (Dimples) ita ma haka suke banbanci nata d'aya ne ke kuma Duka biyun ni kaina nakanyi mamakin tsananin kamarki da mahaifiyarki ta baci zarah "Dan murmushi Zarah tayi sosai takanji dadi idan akace tana kama da mahaifiyarta sosai takejin dadi idan Baba na bata labarin mamanta cewa tayi " Baba Itama tana da hakuri ko?Murmushi Baba yayi ya ce "Hakurinta ya ninka naki Zarah kinsan dai rayuwa Ana cewa zomu zauna zomu saba ko ?To bantaba samun sabani da mahaifiyarki ba b'ata tab'a fushi dani ba ,bata tab'a yimun gardama ko musu ko kuma na fad'a magana ta mayar ba bamu tab'a fada ko na dak'ik'a d'aya da mahaifiyarki harta rasu shiyasa har kullum bazan tab'a mantawaba da mahaifiyarki ba Bantaba salla biyar ba ban roka mata Rahama wajen ubangiji ba Zarah y'ar aljanna ce ,tayi mutuwar shahada sannan ta rabu da mijinta lafiya ta rabu da mak'wafta da duk Wanda tayi mu'amula dasu lafiya Wanda nake da tabbacin iyayenta ma lafiya ta rabu dasu mutuwar mahaifiyarki ba mata ba hatta maza da idanunsu suka dinga kuka unguwar nan babu Wanda baiji mutuwar mahaifiyarki ba Allahsa ta huta"" Ameeen Baba "Ina son kiyi hakuri a gidan mijinki kamar yanda mahaifiyarki tayi zakici ribar zaman duniya Zarah har ko yaushe na kanyi alfahari dake matsayin kyautar da Allah yayi mun Na mallakamun ke a matsayin y'a ked'in y'a ce da kowani uba zaiyi alfaharin da kasancewarki y'a a gareshi Allah yayi miki albarka,Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki Albarka Sannan ina son na sanar dake mun tsaida Ranar Aurenki da yaron nan d'an mutunci Hafiz Sati Ukku masu zuwa" Wata irin faduwa gaban Zarah yayi Jin an tsaida Aurenta Da Hafiz sati Ukku Bayan da Auren wani a kanta"kanta yayi wata irin sarawa Wanda ta kasa control d'in kanta a matuk'ar rude ta d'ago ta kalli Baba dake mata kallon mamaki ta ce.........✍🏿
Chapter 73 · 0% Book details