← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 129

Sashe 8

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tari ne yaci karfinta Mik'awa Malam y'ar tayi tuni harta fara fita daga hayyacinta Tare da cewa " ga Amanar y'ata na a hannunka Malam ka kula mun da ita ka bata tarbiya ka zame mata uwa da uba ka bata duk kulawar da zan bata ka bata tarbiya harka Aurar da ita Malam ga Amanar yata nan "

a lokacin ne maman asmy ta shigo ita ma cikin kid'imewa ta nufi gadon tana hawaye ta ce "me kike cewa haka Zarah ai cuta ba mutuwa bace haka haihuwar take kowa haka yakeji"

Murmushin yake tayi tare da girgiza kai ta ce "bakisan irin abunda nakejiba shiyasa wannan ba zafin nakuda bane sannan ta kamo hannunta tana hawaye ta ce "Ga Amanar y'ata nan A hannunku ku rik'emun ita amana sannan ku bata tarbiya nasan zaku iya ".

" Malam ne da har zuciyarshi ta karye Ya fara hawaye ya ce "Bazaki mutu ba Zarah ta Insha Allah muna nan tare Harsaikinga auran Zarah da kanki zaki Riki y'arki" .

Kallon y'ar kawai take tana tari cikin k'arfin hali ta Ciro wata zoben gold dake hannunta Tare da awarwaron zinaren da dukansu tare aka tsinceta da su ta mik'awa Malam ta ce .

"idan y'ata ta girma har lokacin Aurenta ku bata wannan shine Babban abunda zai taimaka mata wajen gano Dangina lokacin da zan maku Bayani ya K'ure sannan ku sanya mata suna na Fatima Zarah sosai tarinta ya k'ara tsananta kafin kuma daga karshe suji ta fara Salati ta na Salati har ta cika.

Allahsrk mutuwa kenan mutuwar zarah ba Malam kadaiba hatta mutanen dake unguwar ta Girgiza su Malam ko Kullum kamar ba namiji ba haka zai zauna yayi ta kukan mutuwar zarah danma idan ya kalli y'arta sai yaji wani sanyi a ranshi tunda bata mutu ba har saida ta bar masa Jininta kuma photocopy d'inta Dan sak Zarah mahaifiyarta ce har dimple dinta sai kyau ma da tafi mahaifiyarta.

Kasancewar maman asmy itama ranar ta haihu saboda tashin hankalin mutuwar aminiyarta itama nakudar tazo mata Tasha kukan wannan Babban Rashin da sukayi ita ta Shayar da Zarah tare da y'arta da taci suna Asma'u ita kuma Zarah daman tun ranar da aka haifeta kamar yanda mahaifiyarta ta fad'a haka Baba ya sanya mata sunan mahaifiyarta Zarah ".

kulawa ta musamman maman asmy ta dinga bawa Zarah tare da Asma'u ta had'u ta dinga renonsu Malam ko yanzu baida wata jinjinar sana a saboda tundaga mutuwar zarah komai ya tsaya masa baya iya Zuwa ko ina koda akayi shekara biyu da mutuwan da zai koma harkar nomansa Ya samu Mai gonar har ya bawa wani haya nan ya dawo gida yaci gaba da tawakkali da Allah harya samu Aikin bakanikanci a wani garrage gyaran mashina da motoci Inda ya fara aikin A lokacin ne kuma danginshi suka fara korafin akan baiyi Aure ba yaci yayi Aure yanzu.

Inda ya hadu da Wata zawara rabi'atu da yaranta biyu a lokacin kamar mutuniyar kirki haka ya aureta tare da yaranta duk yanda zaiyi saiya ciyar dasu Inda Ya maido da Zarah gidan Wanda a lokacin ta nuna Duk d'aya ne a gaban idonshi zata nuna tafi kowa son Zarah Inda Bayan idonshi irin azabar da take gana mata kare baici Malam bai tab'a ganewa ba saboda Zarah ta tashi da wani irin hakuri kome za a mata bata tab'a fada masa ba.

ta haifi yaranta Biyu da Malam Safiya sai kuma khairat Azaba sosai take ganawa Zarah kasancewar ta sameta yarinya mai hakuri Wanda Malam baisan da hakan ba saidaga baya ya fahimta A unguwar ba Wanda baisan irin wahalar da rabi keba Zarah ba.

Malam ya tsayewa Zarah Karatun boko da na arabi Zarah yarinya ce mai baiwar kokari Dan kokarinta saidai a kirashi na baiwa saboda yanzu za a ayi yanzu za a kwashe duk karatun da tayi tare sukayi da Asmy Dan sun zama kamar y'an biyu kuma maman asmy ta rik'e Amanar da aminiyarta ta bata danma Mama Rabi dake azabtar da ita Yaran Mama Rabi duk sun lalace saboda Rashin tarbiya da bata basu ba khairat ce cikinsu kawai ta fita zakka zarah tunda ta taso ta fara perioud take shan wahala dan duk wata saidai akaita ayi mata allura irin fita daga hayyacinta da take har suma take sannan tana da larurar tsananin sha'awa mai karfi wanda wani lokacin abun ya taso mata saidai a bata maganin bacci wanda shawarar dr din da aka taba kaita wajenshi ne dan ya bata magani ya basu hakan .
wannan kenan.

*FCT ABUJA*

Manyan motoci ne na gani na fad'a Sunkai Sha biyar jere suke suna tafiya cikin gudu saboda bikin da za a gudanar na bud'e shahararren sabon shopping mall d'in da ya amsa sunansa.

Wajen shake yake da manyan mutane tun daga kan y'an kasuwa "shahararrun masu kudi da sauransu *MD SHOPPING MALL*naga an rubuta a saman ginin yanayin yanda akayi rubutunma kad'ai ya isa ya sanyaka Yin k'auyanci.

Waje ne da ya tsaru da kyau saika rantse ba k'asa Nigeria kake ba saboda yanda zakayi mamakin irin dukiyar da aka zuba a ginin ma b'ata lokaci ne.

Nan aka fara gudanar da bikin bud'e Wajen Bayan jawabai daga bakin manya da shahararrun y'an kasuwa Inda akazo ga jawabi wajen mai gayya mai aiki wato mamallakin wannan shahararren wajen watau Mustapha Dikko *MD* .

"hamshak'e ya ke a wajen banyi Tunanin yana jin hausa ba saboda kwata_kwata baiyi kama da hausawa ba Fari ne sosai kamar bature ko kuma ba indiye Sanye yake cikin bak'ar coated wacce ta amshesa ta kara fito masa da kyau da kuma hasken fatar sa kallo d'aya zakayi masa kaga asalin ba india

sanye ya ke cikin siririn farin glass sumar kan nan nasa lufluf gwanin sha'awa da burgewa ga kuma sajenshi Dake zagaye da kyakyawar fuskarsa daya kara kayatar da tsananin kyaun da Allah yayi mishi.

a gaskiya ni kaina saida na rude da ganin zubi da kyau irin na wannnan bawan Allah zan iya cewa tsawon rayuwa ta ko a film bantaba ga namiji da kyau irin haka ba duk inda karshe da baiwar kyau take tofa Yakai a kirasa da komai Dan guy din ya had'u karshen had'uwa (lol).

Daga zaunen da yake batare da ya mik'e ba ya amshi abun maganar tare da Fara jawabi cikin zazzak'ar muryarsa Yanayin yanda yake.maganar saika d'auka wani sautin wak'a ne mai ratsa zuciya ke tashi.

baiyi wata magana mai tsayi ba saboda shi daman Chan ba mutum bane mai fiya son magana da yawa ba Hasalima yanzu a k'agare yake A gama taron nan ya tafi dukda dalilinshi kowa yazo wajen amma ya k'agu saboda hayaniyar da ake a wajen dan shi ba mutum bane mai son hayaniya .

camera ce A kansa ta gidajen television da dama kowa so yake ya d'auka jawabin harya gama ana haskasa da camerori.

"Tsaki yaja yana kauda kai Dan ba abunda ya tsana irin taron jama a "

jabir ne dake kusa dashi ya rad'a masa a kunne"Sorry bloody Dan Allah yau karkayi mana halin naga ka fara tsaki ka.daure har a gama bikin nan kasandai duk Wanda yazo wajen nan kai yazo tayawa farinciki".

Lumshe ido MD yayi tare da bud'esu a hankali batare da yace uffan ba kamarma ba dashi jabir yake magana ba hakan bai damesaba saboda idan da sabo ya saba da halin aminin nasa Shidai burinshi Indai bazai kwafsa musu ba ya jira har agama falilllahil hamdu".

Ba aja wani lokaci ba aka gama komai Inda MD ya Mike Security na take masa baya Sunkai su 30 yanda kasan wani president .

security gabansa haka bayansa ma sai kakkaresa ake nan fa y'an jaridu suka shiga d'aukar rahoto har ya isa motarsa Inda suma suka shiga motocinsu A motar ma tunda ya shiga Danna waya ya ke

"Jabir ne dake gaban motar da juyo tare da tambayarsa ya ce " Ranka ya dad'e ina muka nufa"Kamar baya da shirin magana Ya ce "Airport" Ya fad'a yana cigaba da latsa waya kamar bashi yayi maganar ba "Jin haka ya sanya jabir ganowa Kaduna Zasuje kenan ".

Ko a Airport d'inma saida nayi mamakin irin yanda mutane ke kallonsa y'an mata har Tuntube suke suna cewa.

" wlh shine MD ne "wata har tsuma take tare da Rungume y'ar uwarta ta ce " Alhmdllh Gaskiya yau rakiyar nan munzo a sa'a ganin mutumin Dan ban tab'a tunanin tab'a gani ba a rayuwa yau nagansa karkiga yanda nake da muradin ganin guy d'innan cikin Sauri ta d'auko wayarta tare da shiga snap daga nesa ta dinga daukoshi Dan tasan ko giyar wake ta sha bata isa ta tunkari wajenba yanda security d'inshi ke zagaye dashi.

Ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga Kaduna koda ya isa Kaduna Chan dinma haka ne Tsaki ya dinga ja shi d'aya saboda a Rayuwarshi ba abunda ya tsana sama da Kallo da kuma yanda y'an mata ke rudewa idan suka gansa Har suka isa Unguwarsu da ke G R A ya na Jan tsaki .

Horn biyu sukayi mai gadi ya Wangale musu Get d'in Aljannar duniya kenan gidane katoton gida mai girman gaske fad'ar kuma kyau da tsaruwar gidan ma b'ata baki ne Dan saimu cinye page Ukku zaku iya kwatanta gidan da gidan indimi.(lol)

Motoci biyar Duka suka danno gidan kai tsaye Ta tsakiyar ita ce tashi A hankali yake fitowa daga motar bayan ya fara ziro kafufuwanshi dake shanye da hadadden cover shoes koda ganin takalmin kasan ba na kananan mutane bane a haka harya karasa fitowa daga motar.

kamar Wanda baison taka k'asa ya fara tafiya securities d'insa ne suka biyo shi da hannu ya musu nuni da su dakata Kai tsaye hanyar Part d'in mahaifiyarsa Ya nufa Kafin ya k'arasa shiga Yaga fitowar Chuchu da gudu Tare da rugowa ta fad'a Jikinshi Sosai nayi mamakin yanda Ya sakar mata murmushi Wanda Ya Kara fito masa da baiwar kyawun da Allah yayi mishi ashe daman idan yayi fara'a yafi kyau yake tamke fuska.
Chapter 8 · 0% Book details