Sashe 95
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zataci da kanta ya kiya shi zaiyi feeding d'inta shi kanshi yayi mamakin akan yarinyar yakeyin abubuwan da bai tab'a yinsu ba a rayuwa wannan ne karo na farko daya tab'a feeding d'in mace sosai ya samu taci abincin Sai sannan hankalinsa ya kwanta magungunan da Nurse din ta kawo ya b'alla mata Tasha sai sannan ya iya Mikewa Dan yaje ya gabatar da salla da harara zahra ta bishi kafin taja tsaki ta ce "mugu macuci azzalumi wlh na tsaneka " Dak'yal ta yunkura tashiga toilet ta dauro alwala ta gabatar da salla dukda batasan tana da tsarkin yin sallarba Dan bataga komai ba yanzu sab'anin idan bata manta ba kafin hankalinta ya gushe...bangaren Jabir sosai yayi kokari akan Baba kamar yanda MD ya umarcesa haka akayi ya samu yarda sosai daga wajen dangin Baba bisa ga taimakon da yayi musu baisha wahala ba ya samu appointment da Najmat a ranar aka maida Baba asibitin dr Najmat Wanda d'aya daga cikin y'an uwanshi ne kad'ai zaiyi jinyarsa bisa ga Dokar asibitin ko dubiya ba a barin mutane shiga saboda masu irin ciwon basasan hayaniya....bangaren Mama Rabi saida akayi mata dinki.kwana tayi tana tsinewa zahra da kawayenta Asmy ko har gida taje ta samu mamanta Tayi mata tas Wanda Bata biye ta ba nanfa mutane aka shiga binciken ina Zahra tayi tsegumi saiya dawo sabo wasu na cewa guduwa tayi Mama Rabi ko itace uwar zazzakewa wajen bada labarin abunda ya faru dukda wasu daga cikin mutane basu yarda zahra ta aikata hakan ba Sosai Mama Rabi ta dinga mamaki lokacin da aka fara shigowa da libgin kayan abinci kamar za a bud'e wani store tsakar gidan saida ta kusa cika da kaya Bayan anyiwa Jabir Iso ya shigo Mama Rabi har kakkarwa take wajen shimfida masa tabarma a takaice suka gaisa kafinma ya fara mata bayani ta ce "yaron nan wannan kayan fa ko b'atan hanya kukayi" Murmushi d'auke da fuskar Jabir ya ce"a a a nan aka kawo Oga na ne ya sanya na kawo muku ga wannan anyi cefane ya fad'a yana mik'a mata y'an Rafar dubu"ai irin godiyar da Mama Rabi tayi kamar tayiwa Jabir sujjada kira take "Kinji Allah Mai iko tsuntsu daga sama gasashshe amma Allah ya sakawa ogan nan naka da alkhairi ya bashi abunda yake nema duniya da lafiya Allahsa ya gama da iyaye lafiya sai kuma kuka ta ce " Allahsrk wai yau nice Rabi da rik'e irin wannan kudin Wanda tunda nake bantab'a rik'e ko rabinsu ba ga kayan abinci Wanda ko buhun shinkafa ba a tab'a Aje mana ba Sosai Mama Rabi Tasha sabbatu daga baya kuma Bayan fitar Jabir tahau rawa da guda yanda.kasan anyi mata albishir da gidan Aljanna..bangaren Asmy kullum cikin kuka take ta rame Ba irin tambayar da Mamanta batayi mata ba akan ta fad'a mata abunda ke damunta ta ce "Bakomai" Dukda ta fahimci akwai abunda ke damunta Ganin ba fad'a ba zatayi yasanyata rabuwa da ita ta sanya mata ido....bangaren Chuchu ma tunda ta dawo bata da walwala sosai labarin da Asmy ta bata ya burkita mata kwalwa sosai takejin tausayin zahra har cikin ranta Dan Asmy ta bata labarin irin bak'ar wuyar da tasha wajen Mama Rabi itamadin wani time d'in kukan tausayin zahra take yanzu bata da burin da ya wuce na Tasan Inda take Ammy itama tayi tambayar duniyar nan akan tafada mata abunda ke damunta Saidai ta ce Bakomai amma daka Kalleta kasan tana tare da damuwa....kwanan zahra hud'u a asbiti aka sallamesu Wanda MD shi yayi jinnyarta harta warke dukda wuyar da take basa na gardama da fad'a masa bakaken maganganu tun a mota zahra ta tubure ta ce "Wlh saiya kaita taga mahaifinta " ba irin yanda MD baiyi da ita ba akan ta Bari idan ta huta saitaje ganin tana shirin Tara masa mutane ya sanya bama su koma gida ba ya d'auki hanyar kd sai sannan hankalinta ya Dan kwanta suna isa kd ya kira Jabir ya turo masa address din asibitin da room d'in Suna isa asibitin MD ya sanya facemask Dan kar a ganesa cike da mamaki zahra ta ce "Yaya zaka kawo ni nan asibitin Bayan yana funtua" A takaice ya ce "ya na nan asibitin ki biyoni " binshi ta dingayi suna zuwa daidai Wani waje aka Hanasu shiga Dukda Dan basu gane MD bane da zasu iya mai alfarma dukda Dokar asibitin ce haka dak'yal fashewa da mai gadin wajen kuka zahra tayi ta ce "Dan Allah ka taimakeni ko ganinsa ne nayi" Hakan yasa ya tausaya mata ya ce "Zan iya muku wani taimako mu zagaya ta k'ofar baya akwai tagar da zaku hangesa ta nan amma karkuyi magana" Cikin Sauri zahra tace "bazanyi ba ngd" Kofar dake baya ya zagaya da su Tare da bude musu Kad'an nan zahra ta Hango Baba kwance Bisa makeken gadon da baiyi kama da na sauran asibitoci ba ga AC har biyu data sama data k'asa banda fanka ga k'atuwar plasma a d'akin kamar wani hotel batasan sanda wasu hawaye masu d'umi suka zubo mata ba ta ce "Dukni nayi sanadiyar shigar ka cikin wannan halin Baba na cuceka bansan da wani ido zan Kalleba ka yafemun Baba ...kuka ne yaci karfinta sosai Kamar daga sama tajiyo tarin Baba yana kokarin farkawa zara idanu tayi ta murza ganin yana bud'e ido Kasancewar ko ina na asibitin ctv camera ce ya sanya daga Chan office d'inta take gane wadanda ke buk'atar taimako ba ayi minti biyar ba saiga Najmat Ta shiga d'akin Sanye cikin farin glass dayayi mugun amsar kyakyawar fuskarta sosai naga ta k'ara kyau da wayewa fiye da wacce take da ita a baya tana sanye da labcoat kai tsaye Inda Baba yake ta nufa Fuskarta dauke da Fara a ta ce " Alhmdllh "Kujerar dake gefen Baba ta zauna Ganin ya farka nan ta fara aikinta Ta tambayesa me yakeji a jikinsa Girgiza mata kai kawai yayi kafin a hankali ya ce " Ina Zahra "Zahra najin da sunanta Baba ya farka batasan sanda kuka Ya Kubce nafa ba rufe mata baki MD yayi tare da girgiza mata kai sosai taji tausayinta da na mahaifinta Yasan akwai shakuwa da k'auna tsakaninsu cikin hikima irin ta kwarewar aiki Najmat Ta kwantar masa daa hankali dukda batasan dalilin shigarsa cikin wannan halin ba ta ce " y'arka ce Baba?gyada mata kai yayi"murmushi tayi masa ta ce "ta na nan jiyama tazo ganinka Yanzu haka tana gida na idan ka warke zatazo ganinka" Ajiyar zuciya Baba ya sauke yanajin damuwarsa ta ragu Saikuma yayi shiru tunowa da abunda Akace zahra ta aikata wanda har yanzu bai gama gaskata hakan ba Najmat na ganin ya fara tunani tayi saurin katsesa Ta fara masa labarai na sanya Dariya da zai hanasa tunani kafin ta kunna masa kallo Na abunda zai basa nishad'i Likita guda takira akan ya zauna dashi pull time kar a sake A barsa yayi tunani ko na minti d'aya ne kafin tabar room d'in ta koma duba wasu Duk akan idonau MD hakan ya faru Ajiyar zuciya zahra ta sauke tana jin k'aunar Dr d'in ganin yanda ta kula da mahaifinta Sosai ta tsaya Kallon Baba ji take kamar ta fasa kofa tashiga taje ta Rungume mahaifin nata dukda tayi mamakin waya sauya masa asibitin daga wancen zuwa wannan Babban asibitin da daga gani za a chashi kudi masu yawa Wanda yayi musu jagora ne yace "Ya isa Haka su tafi kar wani ya gansu a ja masa ta aikinsa "hawaye d'auke da fuskar zahra ta ce " nagode "kudin da suka rage a aljihunsa MD ya basa masu yawa kafin Su koma mota sosai jikinsa ya mutu gaba d'aya kamar Wanda aka zarewa lakka Har suka isa motarsa nanfa zahra ta tubure tace batasan wannan ba ba Inda zata koma hankalin MD nanfa ya k'ara tashi yahau Lallashinta amma ta tubure ganin tana shirin guduwane baisan lokacin da karfi yazo masa ba ya fardota tare da sanyata mota yayi Sauri ya zagaya yayiwa motar lock kai tsaya ma bai tsaya saurarar komai ba ya juya Abuja sosai zahra ta dinga fasa masa kuka kamar ranta zai fita har suka isa Abuja tana kuka tana tsine masa Daren ranar sunsha dabu da ita Dan burkucewa tayi ya ce Wlh saiya maida ita gida kota jaza masa bala i dak'yal ya samu baccin gajiya ya kwasheta ....sosai Baba yake samun sauki a asibitin Dr Najmat kulawa.sosai Jabir yake basa bisa ga umarnin MD Bayan sati biyu jikin Baba ya warware Ranar da aka sallamesa y'an uwansa sukayi shawarar awuce dashi Batsari ya karajin sauki saboda sunsan halin Mama Rabi sarai zata Kara tayar masa da hankali ne akan zahra ta gudu Bayan sun boye masa sunce tana gida zuciyar Baba chunkushe da tunanin zahrarsa .....Cikin satin nan ba k'aramun dabi zahra da MD suke sha ba Sosai zahra ta birkitawa MD tunani ne yau inya tallabota nan gobe ya tallabota Chan sosai yake hakuri da jure irin abunda take masa shi kanshi baisan yana da hakuri har haka ba abinci ko Sai yayi kamar zai mata d'ure tukwana yake samu taci da bala'i da masifar saiya maida ita gida sannan ancire mata cikin nan har sukayi wata guda a gidan Wanda MD ko kd baisamu yaje ko gaishe da Ammy yayi ba Saidai ya kirata a waya ya ce uzuri ne yayi masa yawa .yauma yana zaune a palour around 9pm yana waya da Ammy tana masa complain Chuchu ta kasa gane kanta indai bashi ba yazo babu Wanda zata fad'awa damuwarsa"numfashi yaja Dan yasan damuwar Chuchu bata wuce ta abunda ya samu kawarta ba ya ce "Badamuwa Ammy Zankirata waya Naji meke damunta insha Allah zansamu nazo " Daga bangaren Ammy ta ce "Hmmm haka dai kake cewa Na rasa wani irin aiki ne wannan da zakayi wata guda kana k'asar bakaga ammynka ba " Shafa lallausan sumar gashin kansa yayi yana murmushi ya ce "Ba haka bane Ammy insha Allahu.muryarsa ce ta sartse ganin fitowar zahra daga ita sai rigar bacci cikin kayayyakin da ya sayo mata Wanda Hakanan take sanyawa d'an bata da wasu Cikinta ya fito yayi das a jikinta Cikin b'acin rai da hawaye ta ce " Waikai