← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 129

Sashe 111

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsine masa amma ke ta kayan Da aka lalata miki ma.kike Allah mai iko zaman gidannan ko kayan takaici Aiko zuwa zanyi na tattara kayana na bar garin haihuwa yau har tajamun Zagi" Hajiya ta fad'a tana goge hawayen takaici kafin tayi fuuuu itama tabar palour "Cikin b'acin rai MD.ya kalli Amira ya ce " Hakan da kikayi burgewa ce to hankalinki ya kwanta kin had'ani da iyayena sannan zakisan iyayena Suna da martaba da daraja sunfi k'arfin zagi a wajenki ki biyo ni"ya fad'a yana fita sai sannan tsoro da fargaba suka kama Amira ta tuno da abunda tayiwa Ammy da Hajiya kaka sai sannan hankalinta ya fara dawowa jikinta tasan karya take ta zagi mahaifiyarshi da kakarshi ta kwana Lafiya karfa ya saketa "Cikin tashin hankali ta bishi Inda ta sameshi cikin mota ya had'e kai da sitiyarin mota Cikin tashin hankali ta fashe da kuka ta ce " Dan Girman Allah MD.karka sakeni wlh tallahi bansan na zagesu ba zuciya ce kasan bata da kashi"Wani irin kallo ha dinga binta dashi cikin Tsawa ya ce "shigo nace" Cikin Sauri ta shiga da Sauri ya figi motar bai tsaya ko ina ba sai gidansu suna isa bakin get ya tsaya ya ce "Fita ki tafi gidanku " Kuka ta fashe dashi ta ce "Dan Allah honey karkace ka sakeni" Cikin Tsawa ya ce "Bakiji abunda nace ba " Ba shirin ta fita tana fita Ya rufe motarsa ya jata da gudu da gudu Amira ta shiga gidansu tana wani irin kuka ta fad'a jikin dad d'inta ta ce "Na shiga Ukku Dad shikenan md ya rabu dani daddy yayi Aure bansaniba Matar harta haihu naje gidansu na zagi mamansa da kakarsa yayi fushi ya maidoni gida shikenan dad nasan sakina zaiyi na shiga ukku wlh dad inason mijina ina kaunarsa bazan iya rabuwa dashi ba wata bata isa ta rabani dashi ba Dady zuciyata ji nake kamar zata tarwatse dad tana cikin wannan sai ganinta sukayi ta sulale a wajen summammiya hankalin iyayenta idan yayi dubu ya tashi a guje aka wuce Asibiti da ita hankali tashi Kafin likitoci su fara kokarin ceto rayuwarta.....MD ya rasa yanda zaiyi da ransa yasan Ammy ba k'aramun fushi ta k'ara dashi ba nakin sakin Amera Jabir ya kira a waya ya sanar masa halin da ake cikin hankali tashe Jabir ya ce " Innalillahi Abu dai baiyi dadi ba bloody me yasa kak'i sakinta Ammy fa da Hajiya ta zaga kishi hauka ne "Jabir bazaka gane bane ni kadai nasan yanda Naji zafin hakan a cikin raina Nafi su Ammy jin zafi naki sakinta ne saboda Duniya zata zageni babu Wanda zai duba abunda tayi za ace na saketa ne saboda Na auri wata harta haifamun yara nayiwa Matar data zauna dani tsawon shekaru goma ko shad'aya butulci" numfashi Jabir yaja yace "Tabbas hakane kayi tunani bloody amma dai abunda yafi kamata kaje kaba Ammy hakuri yanzu kayi mata bayanin nan zata fahimce ka" Kamar yanda Jabir ya fad'a masa haka yaje ya samu Ammy da dare ko gaisuwar da yayi mata kin amsawa tayi cike da damuwa ya ce "Dan Allah Ammy kiyi hakuri wlh bawai Dan banji ciwon abunda Amera tayi ba yasa ban saketa ba nayi hakan ne saboda gujewa surutun mutane za ace na saketa ne kawai saboda wata Matar ta haifamun yara na rabu da ita tsawon shekararmu goma ban rabu da ita ba sai yanzu za aga Rashin kyautawata Wanda kome tayi baza a ga nata ba Amma Ammy kiyi hakuri indai zaki janye fushin nan naki wlh zan saketa yanzu daman na Turata gidansu Saina aika mata takardarta indai hakan zaisa hankalinki ya kwanta" Tunani Ammy tayi tace tabbas hakane dagowa tayi ta Kallesa har saida yaso bata tausayi ta ce "Bance ka saki Matarka ba Inama umartarka da kaje ka D'auketa ku koma gidanku Kamar yanda bazanso a saki nawa y'ay'an ba haka bazanso a saki nawasu ba ka mayar da Matarka gidanku sannan Ka lallasheta harka samu ka shawo kanta Tabbas kishiya da ciwo musamman baka San da ita ba har sai da y'ay'a dukda dai batasan dalilin Auren ba saboda soyayyarta ne ni na yafe maka ba abunda kayimun amma dai ka sani ina kan bakana saika saki zahra "cikin wani sabon tashin hankalin ya d'ago ya ce " Dan Allah Ammy kidaina maganar sakin Mamy na yarda zan saki Amira amma Bazan iya sakin Mamy ba please ammy ki barmun mata ta"nazarinshi Ammy ta dingayi kenan yayarda zai iya sakin Amera Amma Bazai iya sakin zahra ba Tunaninta takeso tabbatarwa na gane irin son da MD yakeyiwa zahra da matsayinta a zuciyarsa Dan tun ba yanzu ba ta Riga da gano irin son da yakeyiwa zahra kenan yanzu zahra harta samu matsayin da yafi na Amira a cikin zuciyarsa a zuciyarta ta ce "Alhmdllh" a fili kuwa murtukewa tayi ta ce "Bazan barmaka ita ba Bazatayi zaman y'ay'a ba sannan na baka daga nan zuwa awa 24 ka kawomun takardar zahra kaji na fad'a maka" Mikewa yayi cike da damuwa ya ce "Gaskiya ni bazan saki matata ba Ammy saboda ina sonta kuma ina muradin zama da ita Dan haka ni bazan sake ta ba " Yana gama fad'ar haka yabar palourn kamar zai tashi sama"Saboda ina sonta "Ammy ta maimaita kafin ta saki wani kasaitaccen murmushi ta ce " Alhmdllh Allah na gode Maka Addu'a ta ta tsawon shekaru ta amsu"Daren ranar MD bai iya bacci ba idan ya tuno da yanda Mamy take tilastashi akan saiya saki Zahra bai tab'a fahimtar irin tsananin so da k'aunar da yakeyiwa Zahra ba sai ranar da Ammy ta rabota dashi shi kadai yasan irin halin d'aya shiga na rashinta ba Tunanin irin rayuwar da sukayi tun a Zaria ya dingayi Tabbas baisani ba ya jima da Fad'awa kogin soyayyar yarinyar sani ne kawai baiyi ba Amma yasan ba k'aramun so yakeyiwa Zahra ba tunba yanzu ba Wanda yakejin duk ruwa duk iska bazai tab'a yarda ya rabu da ita ba ....Bangaren zahra sosai ta tsorata da ganin yanda Amira taso halaka mata ya dak'yal suka samu little zahra tabar kuka Bayan Chuchu ta goyata tana jijjigata ta samu tayi bacci sai sannan hankalinsu ya d'an kwanta...bangaren Amera ko itace bata farka ba sai washegari Kamar mahaukaciya haka ta tashi dak'yal iyayenta suka dinga Lallashinta harsuka samu tadan sauko amma har lokacin kuka take kamar ranta zai fita idan ta tuno da wai MD yayi Aure harda yara ji take kamar zuciyarta zata tarwatse babanta ko shi kadai yasan tashin hankalin daya shiga watau duk harin dukiyar MD da yake na Amira ta Haifa masa y'a y'a Wanda ko ya mutu ko ya kashesa Amera da yaranta Kadai sai mahaifiyarsa zasuyi gadonshi Duka plane d'inshi ya tafi a banza wata banza tazo ta Haifa masa Har yara Ukku Tabbas dole ne Yaran su mutu Sannan dole ya kashe MD.....Kwana biyu Amira tayi a Asibiti aka sallamesu Lallashinta kawai dadynta yake akan tayi hakuri ta nuna musu ta hakura karta sake tayi haukan da MD zai saketa tabi komai a Sannu shi zai sama mata manufa dak'yal ya samu ta yarda da hakan amma ita kadai tasan yanda takeji a cikin zuciyarta wannan matsiyaciyar MD ya had'a matsayi d'aya da ita harta Haifa masa Yara intana Tuna abunnan ji take zuciyarta na shirin tarwatsewa saida tayi sati Tana jinya kafin a sallameta a cigaba da kula da ita a gida Dan yazama wata mahaukaciyar karfi da yaji...MD dakatawa yayi da zuwa gidan Ammy saboda kullum yaje zance d'aya ne akan saiya saki Zahra shi kuma ya kafe Akan bazai saki matarsa ba a haka dai Ammy na kula da Zahra da yaranta Bayan gyarata din da take Dan kayayyakin gyara na musamman ta sanya aka hadoma surukar tata gyarata take tsab a haka har sati biyu Wanda nanfa hankalin MD ya tashi akan son ganin zahrarsa Yau tunda ya shigo Ammy tayi banza ta kyalesa dukda ta k'asar ido ta Kallesa ganin ya rame saida ya bata tausayi amma Kuma Tabbas ko tana basa zahra saita gwalasa shiru yayi yana hangen Inda zai ga bullowar zahra ko Chuchu amma shiru Chan yaga tashin Ammy a wajen Ajiyar zuciya ya sauke kai tsaye stairs yahau ya nufi bangaren Chuchu Koda ya shiga tsaye ya samu Chuchu na goye da little zahra na zaune tana feeding d'in Akhbar daga kofar MD ya dinga mata wani irin mayen kallo ganin yanda take Shayar da d'an cikin nutsuwa suna Hira da Chuchu Gyaran muryar da yayi ya fargar dasu da Kallon mamaki suka bishi kafin Chuchu tayi Dariya ta ce "Yaushe ka shigo yaya daka tsoratani " banjima da shigowa ba Ganin yara na nazo""ya fad'a yana karasowa d'akin Tare da Zama gefen Gado Sosai gaban zahra ya tsananta fad'uwa kallo d'aya tayi masa bata sakeba saboda wani irin kwarjini da yayi mata rabonta dashi tun washegarin Suna gabanta na fad'uwa tayi Sauri ta cirewa Akhbar Mama dukda ba koshi tayi ba "Sauko little Chuchu tayi daga bayanta ta ce " Gata yaya yau saikayi mana raino tunda Allah ya kawoka"amsarta yayi yana murmushi ya ce "Oyoyo my Ammy" yana amsarta ta tashi daga bacci Da Hannu ya dinga mata wasa yana murmushi fita Chuchu tayi tabar d'akin zahra na ganin haka ta Aje Akhbar kusa da amar da duka sunyi bacci ta mike zata fita Tana yin hanyar fita Ya fardota da hannu d'aya Tare da matsota gefenshi"wara idanu tayi saikuma ta hade rai Ta ce "Meye haka wai malam " Har mommy's d'insu nazo gani ai Kuma ya zaki fita"ya fad'a yana kissing Little zahra Turo baki tayi ta ce"Ni Dan Allah ka sakeni bansan wannan Abun sanadin Ammy tazo tagani ko Chuchu su zargemu "murmushin gefen baki yayi ya ce " So what Dan sun gani ai kowa dai yasan da matata nake tare"Wani banzan kallo tayi masa tana shirin kwatar kanta daga matsar da yayi mata ta ce "Dan Allah ni ka sakeni kajedai Chan wajen Matarka ni ba matarka bace" ta fad'a tana Kokarin kwace kanta A hankali ya Aje little wajen y'an uwanta tare da juyar da zahra ya kwantar ta ita yabi ta kan kirjinta ya hayeta Dan yana sane
Chapter 111 · 0% Book details