Sashe 125
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amera sukace tsafi Kuma Mudan kana nufin har tsafi make bamu sani ba innalillahi wa inna ilaihiraji'un"Banda kuka ba abunda Baban amera yake kukan nadama ya ce "na Fara tsafine tun kafin dawowata kaduna na hadu da wani abokina Wanda sanadiyarsa na fada harkar tsafi Ni mutum ne Mai tsananin son Abun duniya tun Ina yaro hakan yasa nake iya komai Akan Indai Zan samu kudi kisa a wajena ba wani abu bane ,na kashe mutane da Dama.....kasa karasa abunda yakeson fada yayi sakamakon kukan da yaci karfinsa salati kawai kowa yake Jin abunda Baban amera ke fadada bakinsa har Zahra da ta shigo Daga baya Saida ta tsorata you tayi Kamar zata ruga MD Dake kusa da ita ya ruko ta "dukta tsorata ,"tashin hankalinta da MD yake jiki baya musaltuwa dakyal ya iya Daga Baki ya kalli daya Daga cikin jami'an tsaron ya ce "Wan laifin ne yayi Wanda har aka zagaye Gidan. Da jami'an tsaro"Daya Daga cikin dpo din da MD yasa Akan binciken kisan babanshi da Kuma na Alh sammani aminin babanshi ya ce"Case din Akan aikin ka ne MD Kasan tun lokacin kisan mahaifinka Da na Alh sammani bamu bar bincike Akan wadanda sukayi Wannan aikin ba to a jiya ne bincike yagano Mana wasu Daga cikin manyan y'an fashin garin Nan Wanda muka gana musu azaba matuka Daga karshe sai yau da safe daya Daga cikinsu ya fada Mana da Shi aka kashe Alhaji dikko Da Kuma Alhaji Sammani bisa umarnin ogansu Alh Mudan Hakan yasa mukayi mazamuka zagaye unguwar sannan muka shigo muka kamasa Kuma Alhmdllh bamusha wata wahala ba ya amsa Mana laifinsa"innalillahi wa inna ilaihiraji'un kowa ke fada Ammy ji tayi mutuwar ta dawo Mata sabuwa a matukar rude ta fashe da kuka ta Ce "Daman Kaine Wanda ka kashemun miji tsawon shekaru me mukayi maka da muka chanchanci Wannan danyen hukuncin a gareka"MD ko shakesa yayi Cikin wata irin muryar bacin Rai idanunsa sun Rina sunyi jawur ya ce"Me mahaifina yayi maka dazaka kashe Shi me yayi maka me mukayi maka"MD ya fada cikin k'ara Wanda ke wurinma Saida suka tsorata dakyal jami'an tsaro suka kwace Mudan Daga shak'ar da MD yayi Masa wani irin huci MD yake Kamar Zai tashi sama Yanajin Kamar ya kashe Baban Amira Daman shine Wanda yayi silar kashe mahaifinsa"Mudan na kuka ya ce "Ban kashe Alhaji Sammani Dan komai ba sai Dan wata Rana muda abokan tsafinmu munje want kauye muka sato wata yarinya a take muka kwankwale Mata Ido mun dauki wani bangarruka na jikinta da muke bukata juyawar da zamuyi muka hangoshi tsaye ya fito daga mota Yana kallonmu Sosai hankalinmu ya tashi ganin shine saboda ya sanmu muma Kuma mun Sansa a harkar wani kasuwanci muka taba haduwa mun d'auko bindiga muna Shirin harbarsa ya maza ya koma mota tare da janta a guje hakan yasa muka Mara Masa baya har muka shigo garin kaduna Muna binsa Wanda a dabara muka dinga binsa Shi a daukarshi ya bace Mana baisan munaankare dashi ba Saida mukaje har kofar Gidansa ya fito Zai bude get muka harbesa a saitin zuciya kafinma ayi wata_wata mungudu Shi Kuma Alh Sammani aminin mahaifinka ne na kashesane saboda munyi sa'insa dashi akan wani Gidan gonarsa da nake son ya sayarmu ya kiya Wanda har nayi b'arin Baki na ce "sainayi ajalinsa Kamar yanda nayi ajalin abokina Alh dikko"Sosai hankalinshi ya tashi har Yana ikirarin saiya mikani ga hukuma lokacin Dana tuno baran baramar da nayi ya Sanya hankalinta tashi gashi cikin gari muke Indai nayi harbi kamani za ayi saboda duk inda nake Daman da bindiga ka nake yawo hakan yasa bankashesa a Nan ba har Saida ya juya zuwa Komawar Gidansa Wanda Shima irin kisan amininsa nayi masa saidai Shi bani da hannuna na kashesa ba sanyawa nayi aka kashemunshi'"ya karasa fada Yana wani irin kukan nadama"Tashin Hankali ba a gwada maka Rana tashin hankalinta da kowa Dake wajen ya shiga ya baci amira ko zuciyarta kasa daukar tension dinnan tayi ba Wanda ya Lura Da Ta sume ma Saida mudan ya gama tonon asirin kansa Yana kuka Yana yayi nadama Yana Durkusawa akan Kakan Zahra ya yafe Masa kasan Dan uwa da d"an uwa sai Allah Sosai tausayin Mudan ya tsargu a zuciyar baba har za a fita dashi Baba ya juya ya ce "Na yafe maka mudan hakkin kasheni din da kasoyi da hakkin kwantar Dani ko yanzu ka mutu kar a tambayeka hakkin Nan na yafe maka"cikin kuka mudan ya ce "Nagode Yaya Saiwataran sai mun hadu a darussalam Kai baka mutu ba Ashe Ni Zan rigaka mutuwa Yaya nayi tsantsar nadama"Daya Daga cikin sojojin da suka zo kamasa suka Tisa keyarsa akayi waje dashi MD ma ransa a matukar bace Yaja hannun matarsa sukayi waje baima waiwayi Amera da take a sume ba Ammy ma da su baba waje sukayi gabaki daya mD da ammy Jin mutuwar Suke ta dawo musu sabuwa har suka Isa gida ammy na tsine mass Tana ja Masa alkaba'i Zahra ko dukta firgice ga Bata Manta ba Jin MD da aka Kira mijinta dashi sunan da bazata Manta Dashi ba Gidan ammy suka sauka Koda chuchu taji labarin Nan itama Nan tashiga tsinenewa Baban Amira har amirar take hadawa Zahra dai batacewa komai hankalinta duk Yana kan mijinta da taga ya firgice fuskarsa ba fara'a ko Zama baiyi ba ya juya ya koma police station Dan hankalinshi bazai kwanta ba har saiya tsaye an yankewa mudan hukuncin kisa Kamar yanda ya kashe Masa mahaifi ranar da dare Zahra tayi Tagumi Akan bed kallon chuchu Dake waya tayi Ganin yanda take wayar ya tabbatar Mata da Adil ne saurayinta Kuma cousine dinta Saida chuchu ta Gama wayarta kafin Zahra ta kalleta ta ce "Dan Allah chuchu na tambayeki waye MD please",Tirkashi chuchu ta fada kafin ta gyara Zama ta ce "Mijinki shine MD momcy Yaya ne MD din ai"Fuskarsa Zahra dauke da mamaki ta ce "Wai kina nufin shine MD dinnan da yayi harbi a gabanmu Wanda na tsana"Kama hannunta chuchu tayi ta ce "Tun lokacin a school naso maki bayani kikak'i fahimta momcy wanna mutanen da kikaga Yaya ya harba Sune wadanda sukayi kisan abokin mahaifinmu da kikejin labari yanzu ranar sun dawo Daga kisan sun kubucewa Yan sanda yayana yakai wajen Wanda dpo ya kirasa ya fada Masa akan ya harbe su Dan Karsu gudu tofa kinji dalilin daya Sanya har Yaya yayi Harbin Nan Amma ba halin sa bane bai taba harbi ba "Allahsrk shiyasa ba ason saurin yanke hukunci akan abunda baka da masaniya Ashe ma Shi taimakone yayi harna rike hakan a Raina nake Masa mummunan zato ke Kuma kinaji Ina zagin yayanki kikayi shiru kikaki fadamun yayankine"Zahra ta fada Tana sauya fuska"Dan murmushi chuchu tayi ta ce "To Taya zance Ni kanwarsa ce a lokacin tsanar da akayi Masa ta shafeni kintuna momcy yanda muke drama Dake a school Akan ki auri yayana Ashe dai tuni ma Yayan yayi wuf Dake nice bansaniba idan natuna abunnan al'ajabi nakeji"Dan murmushi Zahra tayi ce "Ni kaina wani gamin ina jinjina Abun"Ikon Allah ne kawai momcy wlh al'amarin Nan yakara wa'azantar Dani duk abunda yake rabonka ne Kota wace hanya sai Allah ya kawo dalilin samunsa sannan matar mutum kabarinsa Hafiz mutumin nawa ko ana Ina har yanzu mamaki nake fa dalilin da yasa yace yafasa Auren duk irin son Da ya nuna Yana maki"Sai lokacin Zahra ta tuno Hafiz kwantawa tayi tare da lumshe Ido a ranta ta na tunawa da ai Indai hakane soyayya to ba so takeyiwa Hafiz ba kawai dai zata auresa ne a saboda Halaccin da yayi Mata Amma so na so to MD takeyiwashi akanshi tasan meye so,a kanshi tasan zafi da radad'in so,a sanshiba tasan menene kishi ,taba ta din da chuchu tayi ne ya sanyyata bude Ido ta kalleta chuchu ce ta ce "muna Hira Kuma zakiyi bacci"Ba bacci nake ba fa ai nazata waya zakiyi da Habibyn naki"Murmushi chuchu tayi ta ce "Ai mungama na Manta ban fada maki ba kiyi Mana murna an maido Yaya Adil aiki Abuja kinji murnar da nakeji Dan banason Nesa daku wlh dafa ba ayi Masa transfer ba saidai a kaini maidurin Nan da ko da ziyara banason zuwanta wlh zafi da ranar garin tayi yawa ga Hajiya ta addabeka Amma yanzu Kinga gani gaku ga ammy musamman ma ke da Rabin rayuwar Yaya a Abuja yakeyinta Kinga naji dad'ina "Dariya Zahra tayi ta ce "gaskiya nayi murna wlh Nima da kikacemun an Fara maganar tsaida ranarku da naji maiduguri ce saida hankakina ya tashi Amma yanzu alhmdllh Tunda dai muna tare"Wlhko najima Ammy Tana maganar kafin wanna Case din ya bullo wait zamuje maiduguri Dake y'an uwan abbanmu su ganki Wanda Basu ganki ba sannan tace idan zata India Ganin gida ma tare zaku tafi itama Yan uwanta su ganki "wai kina nufin Ammy y'ar India ce kenan shiyasa Naga ita da abban su Zahra Basu Kama da hausawa najima Ina wannan tunanin Ina musu kallon Indiawa Ashe dai da gaske ne kune bakuyo Kama da y'an chan ba keda Aunty zey"Zahra ta fada "Gyada Mata Kai chuchu tayi ta ce "Eh Mu munyi Kamar Abba ne shiyasa"Allasarki "Bari na Miki wata gulma kinsan Yaya Jabir da Asmy sunjone soyayya suke kuwa to ko rannan da kikaga tazo Shi ya kawota ya maida ita Kinga yanda yake tarairaiyarta saboda dakyal ya samu ya shawo kan y'ar rigimar tasa Suna chan Suna zuba love yanzu Haka da Zaki Kira wayarta waya zakiji tanayi"Chuchu ta fada Tana Dariyar shakiyanci "wow Da gaske kike wai "Zahra ta fada "Wlh da gaske Baku zauna kunyi doguwar hira bane shiyasa Bata fada maki ba "Cike da farinciki Zahra ta ce "Alhmdllh Kai Allah na gode maka wlh karkiji irin dadin da naji Kinga Shikenan dukanmu mu ukkun bamuyi nesa da juna ba"Wlhko Nima karkiji yanda nakeji"a wayar chuchu suka Kira Haka ko akayi suka samu Tana ways Saida ta gama takira Sosai Zahra tayi Mata tsiya ta Rama irin yanda ita take Mata sunjima suna hira cike da kewar juna "Asmy ce to ce"Wai kinsan rad'e_Rad"in da nakeji a gari Wai Su Habiba da Salamatu sunyi cikin shege anje a fidda Abun yaki fita