Sashe 26
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
idan ta dafa bango ta na iya tafiya da kanta ta koma kan gadon Kazar da fruits din da Jaber ya kawo a bata Dr Halima ta shiga bata da kanta Wanda dak'yal da lallashi ta samu ta d'anci . Dr Halima ce da murmushi a fuskarta ta ce"sorry ko amarya ki saki ran mana tunda da sauki Ki daure kici kazar Zata taimaka maki"cikin sanyi murya ta ce "Aunty na k'oshi Inajin kamar zazzabi zai rufeni" Tab'a jikinta Dr tayi ta ce "Subhanallahi Ga zafi nan jikinki Bari na hada allura nayi miki zata taimaka maki nan Dr ta had'a tayiwa Zarah allura dukda ta na matsar k'walla akayi allurar yunkurawa tayi zata Mike Dr Halima ta ce " ina kuma zaki Keda baki lafiya"hawaye na bin k'umcinta ta ce"alwala zanyi na rama sallolin da banyiba"Okay Kibi a hankali kinji kanwata "Gyada mata kai Zarah tayi Dan ta lura Matar Nada sakin fuska kuma ga Alamun babbace Dan daga ganinta kasan bazata rasa yara ba Saida Zarah ta rama sallolin ta gabak'i d'aya a zaune kafin ta mik'e ta koma kan gadon blanket Ta rufa mata tare da cewa" ki kwanta yanzu bari zanje na duba patient kinji"Bayan fitar Dr Halima Zarah banda hawaye ba abunda take ta na jin shigowar Jaber tayi saurin maida idanuwanta ta rufe kamar mai bacci nanko ba bacci take ba banda tafarfasa zuciyarta ba abunda take Jaber ganin ta samu bacci Ajiyar zuciya ya sauke tare da Aje ledar kayan sawa da ya sayo mata da su brush da Maclean. Kwanan Zarah ukku a asibiti wanda Dr Halima ta dinga kula da ita tamkar k'anwarta cikin kwanakin nan harsun saba da Zarah Dan ta lura Matar na da kirki Kullum sai Asmy tazo amma Zarah bata bata ma kofar da zatayi mata magana tsananin fushi take da ita marar musaltuwa yanzu taji sauk'i harma ta fara takawa zazzabin ma yanzu yayi sauki Saidai damuwa da tayi mata yawa Dan duk ta rame Yau ma da Yamma suna zaune Dr Halima na bare mata ayaba Asmy ta shigo A sanyaye Zarah ta na Dagowa ta ganta lokaci guda ta b'ata rai tare da cewa "Ficemun da gani Asmy bana k'aunar ganinki kafin nayi maki abunda baki tunani" Asmy na hawaye ta ce "Ni kike kora Zarah me yasa bazaki tsaya ki fahimceni ba," bazan fahimcekiba bazan tab'a fahimtarki ba har a bada ki Ficemun da gani tunda burinki ya cika ai shikenan ki rabu da ni karki Kara takurawa rayuwata kuma ya isa haka"ta k'arasa fad'a ta na fashewa da kuka Itama Asmy tana kuka ta ce "zan tafi Zarah bazan k'ara takurawa rayuwarki ba kamar yanda kika fada " ta fad'a ta na kuka tare da Juyawa cikin Sauri tabar asibitin "Bayan fitar asmy Dr Ta kalli Zarah dake Kuka ta ce" na tambayeki mana kanwata"Goge hawayenta Zarah tayi Dan yanzu kuma ta rage kukan Saidai na zuci ta ce "Ina ji Aunty" Me ya sanya duk sanda Yarinyar nan tazo kike korarta ta damu dake sosai matuka sannan me yasa tsawon kwanakinki Ukku Asibiti banga mijinki ko wani nashi ba ko wani naki yazo duba ki in banda saurayin nan dake hidima dake kuma na tambayeki kince ba mijinki bane please karkice na yi maki shishigi abun ne ya bani mamaki" Kuka ne ya kubcewa Zarah Dan bata da Amsar tambayar da dr Halima ke mata saida ta tsagaita kukan Kamo hannunta Dr Halima tayi ta ce "Ki daukeni tamkar yaya ko uwa Zarah Bazan tab'a yada sirrinki ba ina son taimakonkine dukda bansan ko kina da buk'atar hakan ba Amma please ina son ki fad'amun Gaskiya akan Lamarin nan ko fyad'e akayi maki??Nanma shiru Zarah bata bata amsa ba jin bazata bata amsa ba ya sanya Dr Halima rabuwa da ita. Washegari dr ya shigo Tare da Jaber a bayanshi Zarah na ganin jaber ta kauda kai Dan Shima ji take ta tsaneshi saboda ta ganeshi sarai shine Wanda ya fito daga d'akin da Asmy ta wullata Yana murmushi ya ce " Sannu ko Zarah ya k'arfin jikin"wani banzan Kallo ta watsa masa tare da kauda kai tana Jan tsaki"Murmushi sukayi shida Dr ganin yanda ta masa dr Ne ya ce "ya jikin Zarah yanzu bakyajin komai ko" Gyada mishi kai tayi ta ce "Eh Dr inason komawa gida Dan Allah ka sallameni" Zaunawa kan chairs din dake d'akin sukayi tare da fuskartarta ya ce "Yau za'a sallameki Zarah amma kafin nan Dan Allah ina son ki nutsu zamuyi magana " Kamar bazata Yi magana ba sai kuma ta ce "inajinka..... <America> Zaune yayi a makeken Palourn shi bayan saukarsa k'asar ko hutawa baiyi ba Yayi awa guda amma baiji d'uriyar Amera ba hakan bai damesaba ba hayewa yayi stairs Bayan yayi wanka Kwance Yayi kan makeken gadonshi tare da lumshe ido Darensu na jiya ne shida Zarah ya shiga dawo mashi a kwalwa shekara Tara ya na mu'amula da Amera Amma baitab'ajin gamsuwa da ni'ima irin Ta wannan yarinyar ba mirginawa yayi yana tuno irin Zumarta da ya lasa jiya tunowa yayi da tsayayyun breast d'inta manya wanda suka fara firgitasa shi daman mutum ne mai tsananin son breast rumtse idonsa yayi ganin lokaci guda zai rikitama kansa. Lissafi tunani ya kumayi yanzu ko ta na wani hali Lokaci guda mood dinsa ya sauya Saikuma ya ce " Ai ba laifi na bane ita ta kawo kanta"ya fad'a ya na dage kafad'a ya k'ulla wannan ya since wancen a haka har wani bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi cike da gajiya..... <Zaria> D'ago da rinannun idanunta tayi da suka sauya kala tsabar bacin rai tayi Bayan ta gama sauraron bayanin da Dr yayi mata Wanda takejin maganganun tamkar almara cikin tsananin b'acin rai Ta ce.........✍🏿 *07026166536 domin magana da marubuciyar*