Sashe 69
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nan chuchu"Jin haka ya sanya Chuchu Jan bakinta tayi shiru karsuce tana musu shishigi Zarah ko kallo d'aya MD yayi mata yasan tayi kuka Saboda yanda idanunta sukayi ja ga kuma Rashin walwalarta data shigo da ita a hankali ya kirata da sunan da yake kiranta watau Mamy "Cikin sanyi ta d'ago ta Kallesa saita maida idanunta kasa " Baki da lafiya ne?Girgiza masa kai tayi"wani Abu akayi miki?nan ma girgiza kai tayi ,"To me ya sameki "kukan da ta dinga Rikewa ne tun a hanya ya Kufce mata batasan sanda ta fashe da sabon kuka ba " subhanalla ya fad'a tare da komawa Inda take ya kama hannunta ya ce "Me akayi miki" Shiru nan ma saici gaba da kukan da tayi "Janyota jikinshi MD yayi saboda a rayuwa ba abunda ya tsana sama da sauraran kuka kukanma na mace wannan yana d'aya daga cikin abunda Yasa ake ganin kamar Amera ke juya sa nan ko haka rayuwarsa take bayason ganin wani cikin damuwa musamman Wanda yake tare da su bare kuma Amera matarsa da suka zauna tsawon shekaru goma " shafa bayanta ya fara cikin sigar lallashi kamar wata baby Yana cikin Lallashinta Har yaji saukar numfashinta alamar tayi bacci Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dinga kallonta yana nazarin meke damunta ya lura dai kamar akwai abunda ke damunta d'an karta tashi ya barta a jikinshi dukda yana buk'atar tashin Saida tayi baccinta ta gaji dukda a takure yake koda ta bud'e idanuwanta Kallon gefenta ta fara ya tabbatar mata da Cikin namiji take sai sannan tunaninta ya dawo mata cikin Sauri ta Zame jikinta a hankali daga nasa kallo d'aya tayi masa tayi kasa da kanta Tare da saurin Mikewa ta shige bedroom sallah kawai tayi danko yunwa bataji tarasa cikin kwanakin nan biyu abunda ke damunta ga tunanin mahaifiyarta da ya sanyata gaba sosai ta fara shiga kogin Dana sanin abunda ta aikata dukda tasan Asmy itace makasudin faruwar komai kwance tayi kan bed tare da lumshe ido kamar mai bacci Tana jin shigowarshi ta k'ara lumshe ido Zaunawa yayi gefen bed din tare da juye take away din d'aya sanya akayo musu a plate ya ce "taso kici abinci" Shiru tayi kamar mai bacci"Nasan kina jina kikamun banza ko Mamy"Kamar bazata tashi ba saikuma ta bud'e ido a hankali tare da mik'ewa ta tashi zaune tana jin kanta na ciwo kauda kai tayi bata bari sun had'a ido ba Plate din ya Aje gabanta tare da cewa"Ki juyo kici karya huce nasan ba abunda kikaci"a sanyaye ta ce "Na koshi?Baki isa ba sai kinci maza karki sake mun musu kinsan abunda bana so kenan"Sosai ta kwabe fuska kamar taga kashi haka ta fara cin abincin da ba dadinsa takeji ba Dak'yal tayi chokali shida ta Aje ta ce " na koshi"Kallonta ya dingayi yana Nazarinta a hankali "Ganin irin kallon da yake mata ya sanyata tsarguwa da kanta taki bari su hada ido" Kince kinyi perioud wannan watan? cike da kosawa ta gyad'a masa kai"shiru yayi kafin ya ce "Kishirya na kaiki Asibiti idanma Maleria ke damunki a baki magani" Kamar zatayi kuka ta ce "Ni wlh banason zuwa Asibitin lafiya ta qalau kaina ne kawai yake ciwo" Dage kafada MD yayi ya ce "Jikinki" yana gama fad'ar haka ya fita da harara ta bishi kafin taja tsaki kasa kasa tana tunanin tambayar da yayi mata sau biyu na perioud a ranta ta ce "Ko ina ruwansa da perioud dina "ba adau lokaci ba taga shigowarsa d'auke da ruwa a cup zaunawa yayi gefenta tare da b'allo parasitimol guda biyu ya ce " Anshi tana yamutsa fuska ta amsa Bayan ta amshi ruwan da ya mik'o mata saida ta rumtse ido kafin ta Had'iye saboda warin maganin da ya ke neman tayar mata da zuciya kakarin kamar zatayi amai yaga ta fara cikin Sauri ya d'aga pridge din d'akin ya fiddo fresh milk saurin budewa yayi tare da kafa mata a baki tana farasha taji ta dawo normal saida ta kusa Rabi kafin ta mai nuni da ta k'oshi janyewa yayi tare da kallonta ya ce"Ko bakiji dadi ba karki sha wani maganin da ya wuce wannan"Saboda me?Saboda haka nace maki"Shiru tayi tare da kwanciya ta juya masa baya"Ki tashi daga baccin nan na fad'a miki"Tana turo baki dukda baya ganinta ta ce "ba bacci ba zanyi" Da Dare tanaji MD ya fara yamutsarta ta fashe da kuka "Sosai MD yayi mamakin abunda bata tab'a masa ba kenan " Hakan yasa ya rabu da ita yana tunanin ko jikin nata ne dayan d'akin ya koma Zarah najin fitarsa ta sauke ajiyar Zuciya raba dare tayi tana salla Wanda yawaici duk adduarta akan mahaifiyarta ne Sosai take roka mata Rahama A wajen ubangiji saida taji bacci ya fara daukarta tukwana ta lallaba ta koma ta kwanta MD ko tunda ya koma ya kasa bacci yana tunanin sauyin yanayin yarinyar abunda bata tab'a masa yau tayi masa A ranshi ya ce "Kodai itama ta fara gajiya ne?To amma me yasa da Chan bata tab'a nuna Rashin So ga abunba sai yanzu" Karfa ciki ne da ita?kai gsky ba ciki bane saboda tace tayi perioud? Meke damunta ne?haka dai MD yayi ta sake sakensa "washegari Zarah duk yanda taso taje lectures MD ya hanata saboda yana tunanin bata da lafiya ita dai tasan lafiyarta qalau yanzu kam ba yanda ta iya ta hakura ta zauna saboda yanzu batasan yawan musu dashi tunda dai kowa ya kusa kama gabansa Ranar da ta cika wata Tara Cif da yarjejeniyarsu Aurensu Wanda MD mancewa ma da lokacin yayi Zarah ko tana sane sarai tunda safe Ta hada duk abunta da tasan nata ne a gidan ta sanya a akwati Kayan d'aya saya mata ta barsu a ciki Wanka kawai tayi hijab d'inta har k'asa bata shafa komai a fuskarta ba zallar ainahin Kyawun da Allah yayi mata ne bata samesa a palourn ba hakan ya tabbatar mata da yana ciki zaunawa tayi zaman jiransa ya fito ya furta mata Kalmar saki ko kuma ya bata takardar sakinta ko ta samu nutsuwa a cikin zuciyarta gashi Allah ya taimaketa kafin lokacin bikinta ta gama idda tayi minti sha biyar zaune kafin taji fitowarsa cikin shigarsa ta alfarma tunda ya shigo Palourn k'amshin turarenshi ya kauraye Duka ilahirin palourn lumshe ido Zarah tayi a ranta ta ce " Baya ragawa Turare"cikin Tafiyarsa ta izza ya Iso palourn "batare da ta Kallesa ba ta ce " Ina kwana"Morning muntashi lafiya"Steady"ta basa amsa a kad'aice "Kallon akwatin dake gefenta yayi ya ce " wannan fa "Cikin k'arfin hali ta ce " kaya na ne zankoma hostel "da izinin wa kuma saboda me?saboda Yarjejeniyar *Auren wata tara* yazo karshe yau wata Taran ya cika nasan kaima.kana lissafi ina jiran ka bani takardar saki na ne kafin na tafi"wani irin kallo MD yake binta dashi Wanda bazata iya fassara yanayin da yake ciki ba lokaci guda mood din fuskarsa ya sauya cikin dauriya ya ce"Kina nufin wata Tara ya cika da aurenmu?"Eh mana Ka lissafa mana ina tunanin ma harya so ya wuce" shiru MD yayi kafin ya d'ago ya ce"Bai cika ba ki koma Lokacin da ya cika zan sallameki da kaina?wani irin kallo Zarah ta dinga binshi dashi na ka rainamun wayau ta ce "Kamarya me kake nufi wlh ya cika kuma yau d'innan saika sakeni tunda ba a garin gab'a_gab'a muke ba " Dukda MD yayi mamakin jin furucin ta Wani murmushi ya saki da bazaka iya sanin na meye ba tare yin shiru ya lumshe ido cikin nutsuwa Hankali kwance"da karfi zuciyar Zarah ta dinga Bugawa bata San lokacin da ta fashe da kuka ba Ta ce "Wlh baka isa ba saika sakeni aiba haka mukayi daku ba,wannan ba adalci bane,kamar yanda a baya lokacin da naki Amincewa da Auren nan Abokinka yayi mana gori bada son raina ba harna amince yanzu kuma wata taran yayi kace bazaka sakeni ba wlh baku isa ba " ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka"Sosai take kuka kamar ranta zai fita MD jin kukan nata Yake har cikin ransa "Bar kukan indai kinason muyi magana ta fahimta" cikin Sauri Zarah ta bar kukan tare da Fara Goge hawayenta "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " Saki kike buk'ata ko?Gyada Masa kai tayi"Okay give me 2 minutes"ya fad'a tare da barin dakin ya shiga d'ayan ba ayi minti goma ba taga fitowarsa rik'e da takarda Yana linke ta dukda Zarah abunda take buk'ata a yanzu kenan saida gabanta ya fad'i k'arasa shigowa palourn yayi tare da makullin mota a hannunsa ya ce "Muje na saukeki" a sanyaye Zarah ta bisa parking space taga ya nufa ya fiddo mota nuni yayi mata da ta shiga Ciki ba musu ta shiga horn yayi mai gadi ya bud'e masa get tsit kakejin motar shiru bamai magana har suka isa cikin Makarantar daidai sanda yayi parking Dagowa yayi ya Kalleta daidai Shima ita d'in yake kallo Saurin kasa da kanta tayi "saida sukayi kusan 10 minute bame magana cikinsu kafin MD ya damko hannunta ya sanya mata takardar A hannunta Dagowa tayi tare da kallonsa ta kalli takardar hannunta da bai saki hannun ta ba har lokaci Bayan few minutes ta tsinkayi muryarsa da cew" Murna kike zamu rabu ko"Shiru Zarah tayi gabanta na fad'uwa "Murmushin da batasan ma anar sa ba taga ya sakar mata tare da sakin hannunta ya ce " Ina ne garinku?Shiru tayi saikuma ta ce"basaikaji ba"wani murmushin ya kuma saki ya ce "Bakison na halarci bikin naki kenan?Gyada masa kai tayi alamar eh"muga wayarki ya fad'a tare da amsa kwafar numberta yayi ya sanya a wayarsa Wanda duk bata lura da hakan ba kafin ya mik'a mata ya ce " Gashi Amarya sai wataran"Amsa tayi sosai tayi sanyi" Bud'e gaban motar tafi tare da fita a hankali harta fita MD baibar kallonta ba Itamadin so take ta Kallesa amma nauyi ya hanata Tanajin tashin motarsa ta juya ta dinga Kallon motar har ya bar wajen a sanyaye tayi hanyar hostel Asmy kadai ta samu a ciki tana ganinta ta taso tare da cewa "Ya sakeki dai ko?A sanyaye Zarah ta gyad'a mata kai" Alhmdllh "Asmy ta fad'a Tana shirin amsar takardar Zarah ta rik'e cikin