← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 129

Sashe 83

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

itaba amma taki amsa tace hidimar tayi yawa ganin jayayyar tasu tayi yawa ya sanya Chuchu Maida kudin jaka da niyyar ranar da za akaita ta had'a mata dasu ....Mama Rabi ce Gaban malamin ta (nikam nace boka dai)Cikin tashin hankali ta ce "Malam baki na da naka kace Auren nan Babu shi bazaiyu ba akwai Babban al'amarin dazai ruguza Auren Kace basainasa anyi komai ba Amma har yanzu banga Alamun lalacewar Auren nan ba har ana jibi d'aurin Aure hankalina fa a matuk'ar tashe yake Malam" buga kasa bokan yayi ya ce "Kina da gaggawa a kowani al'amari rabi na buga na buga amma amsar d'aya ce Auren nan babu shi Leko ki gani da idanunki " Lek'awa cikin kwaryar Rabi tayi ta ce "Malam ban fahimta ba " Da yatsa ya nuna mata ya ce "Kinga wancen na nesa da Hasken nan guda biyu Wanda ya fad'i d'innan" tace Eh "To shine mijin da ake shirin daura Auren ta Riga tayi masa nisa nesa ba kusa ba Babu Aure tsakaninsu" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "To Malam hasken nan fa guda biyu Dana gani hannayensu rik'e Dana juna" Itace tare da Abokin rayuwarta tun sanda kikaban aikin nan Dana buga haka nake ganinsu Saidai naga Haske amma fuskokinsu sunki bayyanuwa "Cikin tsananin tashin hankali ta ce" Malam abokin rayuwarta kuma to meyasa Sukaki bayyanuwa sai Haske"Saboda suna da tsananin ibada da addu'a ko tsafi mutum yake tofa ina tabbatar maki bazasu tab'a Tab'uwa ba biyun nan ba kinsan ba irin aikin da ban maki ba kinsan yanda aiki na yake kamar yankan wuk'a to wannan Biyun bani da k'arfin ikon da zan iya musu asiri saboda babu Aljanin dazai iya tunkarar su yin kokarin hakan ma zai iya jawo mana asara babba Saidai a iya binciken da nayi su biyun suna da tsananin Kusanci da junansu sannan dukansu Haskene a cikin rayuwar kowannensu musamman ita Yarinyar da haskenta yafi nashi "uwar zufa ce ta ketowa Mama Rabi Cikin tashin hankali ta ce " Malam kace Haske ne su Duka biyun"Wannan maganar haka take kuma duk Inda kikaje haka za a fad'a maki"To Malam bazaiyu a raba su ba dan tun yanzu hankalina ya fara tashi aiduk Inda Haske yake alkhairi ne Taya za ayi Ace Zarah Haske ce kuma Shidinma ya zama Haske"Dariya yayi ya ce "Kina da tsananin hassada Rabi yanzu ki fad'a abunda ya kawoki " Goge uwar zufar data keto mata tayi ta ce "Malam Auren nan bana son yayu so nake ayi aikin da zai ji baya kaunarta ya tsaneta bazai iya Aurenta ba Wanda da kanshi zaizo ya furta hakan" Yana buga kasa irin tasu ta y'an tsubbu ya ce "Wannan mai sauki ne saboda yaron bashi da wani karfin ibada sosai A yanzu ma za a iya Gamawa dashi amma ina Kara tunasar dake kinyi gaggawa zaki k'ara daukawa kanki zunubi ne a banza Bayan Abun daman bazaiyu ba Auren nan babushi na fad'a maki tun farkon zuwanki da maganar nan" eh Malam nidai ayi aikin hankalina zaifi kwanciya"Dubu Biyar din da saida ta sayar da fantekun ta na Aure ta bashi da niyyar idan Aiki yaci zata cika masa sauran "......yau ta kama Juma'a kuma yaune Ranar da za a fara Event din bikin Wanda yau walima kawai za ayi tunda Zarah ta tashi yau ta tashi da zazzabi mai zafin gaske da ciwon kai ga tashin zuciya Chuchu da Asmy kadai suka sani basu fad'awa kowa ba har Wajen 12:PM tayi Tana kwance jikin Chuchu jikinta yayi zafi rauu cike da damuwa Chuchu ta ce " Kinki a kaiki Asibiti momcy taya zaki zauna jikinki da zafi haka "Girgiza mata kai tayi ta ce " zanji sauki"Asmy data shigo da Ruwan tea a hannunta data had'o mata ta ce "Ki tashi kisha zakiji k'arfin jikinki Kinga ba abunda kika ci tun safe" Nanma girgiza mata kai tayi ta ce "Na koshi bana son Cin komai Asmy " Matsowa Inda take Asmy tayi tare da Aje cup din ta tallabota ta ce "Bazaiyu ba saikinsha wlh kinji na rantse " badan Zarah ta so ba saidan yanda Asmy ta rantse dole saita sha ya sanyata yunkurawa ta karba a hankali Tana rumtse idon kanta dake mata ciwo "Kurba d'aya Tayi taji Madarar ta taso mata Batasan sanda ta saki cup d'inba sakamakon aman da taji ya taho mata da gudu ta Ruga tayi waje kafin ma ta k'arasa makwararar gidansu ta fara sheka amai Kamar zata amayar da y'an cikinta dangin Baban ta da na Mama Rabi da suka zo Duk Kallonta suka tsayayi Yanda Take kwarara amai Chuchu ce ta biyo ta ganin ba Wanda yayi yunkurin taimaka mata ya sanyata d'aukar butar data gani a tsakar gidan ta cika ruwa tare da nufar Inda take ta fara jera mata Sannu a lokacin ko magana bata iyayi Asmy ma wajen tayo su Suka taimaka mata ta gyara jikinta Daya daga cikin K'annan babanta ta ce " Keko Zahra'u Me yake damunki Irin wannan aman"shiru tayi ta kasa magana.Mama Habi ta ce "Dake fa ake" Dagowa tayi ta Kalleta ta ce "Bakomai Mama" A a daga ganinki kaga marar lafiya ni sai yanzu ma na lura maza shirya na kaiki Asibiti anyi ciwo ba magani ciwon ma kuma na amarya"Hakanan Zarah taji gabanta ya fad'i "Chuchu ce ta ce " Mama Anjima basai a kaita ba yanzu tad'an huta "Mama Habi tace " to shikenan Sai Anjima idan ta tashi kizo ki fad'amun "To Chuchu ta fad'a daki suka koma Inda Asmy ta dirmiya duniyar tunani tsoro da fargaba cike da ranta tsoranta Allah tsoranta ace Zarah ciki ne da ita tasan shikenan tasu ta gama " Chuchu ko lallaba Zarah tayi harta samu tayi bacci sai sannan ta sauke ajiyar zuciya ta Kalli Asmy ta ce "waiko tana da typord ne " Girgiza mata kai tayi ta ce " a a a "Ikon Allah kuma take Amai haka to Allah ya bata lafiya Gaskiya ya kamata Aje asibitin Kar wuri ya K'ure amarya ba lafiya " Shiru Asmy ta dirmiya duniyar tunani ganin haka ya sanya Chuchu janyo wayarta ta fara chat sai wajen la'asr Zarah ta farka ta tashi jikin da sauki Saidai kasala da ciwon kan Kad'an nan suka shiga yi mata Sannu har khairat data shigo Inda taje ta fad'awa Mama Habi Ta tashi "Da Abinci a plate Mama Habi ta shigo d'akin Bayan ta zauna Kallon Zarah tayi ta ce " Anshi kici Nasan ba abunda kikaci"Dagowa tayi kamar zatayi kuka ta ce "Na koshi Mama" wani kallo tayi mata ta ce "Baki isa ba Anshi maza kici kar ranki ya baci" Zarah tana amsar abincin kafin ma takai Baki taji zuciyarta ta tashi amai na shirin zo mata "Cikin Sauri ta mik'e tare da rugawa tayi waje duk da kallon mamaki Mama Habi dake zaune ta tab'a hannu ta ce " me nake gani haka ni Habiba"batayi amai sosai ba saboda ba komai cikinta nan fa Mutane aka fara ido ido musamman dangin Mama Rabi ita ko "Fitowa tayi ta ce " Subhanalla Zarah me nake gani haka kiyi amai da safe yanzu ma haka lafiya kike saikace mai ciki"Kallon da Mama Habi tayi mata ne ya sanyata yin shiru tsaki taja tace Tashi Muje ki sanya hijab d'inki muje Asibiti "tab'e baki Mama Rabi tayi ta koma ciki ita da y'an uwanta suna cewa " shidai abun duniya baya rufuwa kome akayi sai anjishi ba wani boye boye "girgiza kai Kawai Mama Habi tayi Da taimakonta ta shiga toilet Dan tayi wanka Bayan ta fito D'akin da su Zarah take ta shigo shigarsu kenan Khairat ta shigo Tare da Kallon Mama Habi ta ce " Mama Baba yace wai kije keda su Mama Zainabu Yana dakinshi"To kice masa ina zuwa ta fad'a tare da mik'ewa kallon su Chuchu tayi ta ce "ta shirya kafin na dawo" yanayin yanda suka samu Baba ne hankalinsu saida ya tashi dafe da kanshi kallo d'aya zakayi mashi kasan yana cikin tsananin damuwa "dak'yal K'anwar tashi da Yayar tashi suka karasa " Mama Zainabu ta ce "Lafiya dai Malam" Sai sannan ya d'ago ya ce "da sauki Zainabu Yanzun nan shigowar da kikaga nayi dangin yaron Chan ne sukazo akan wai Yaron ya ce ya fasa sun kasa gane kanshi tun jiya gidansu ba irin Fafatun da ba ayi ba karya maidasu kananan mutane amma ya murje ido ya ce " ya fasa Auren kuma ma aka kuskura aka daura zai iya sakinta a ranar Dan haka shine sukazo suka bamu hakuri akan muyi hakuri a d'auki abun matsayin kaddara wlh hankali na matuk'ar tashe yake ina farincikin zan Aurar da Amanar Allah Murnata ta koma ciki wlh nayi mamakin yaron nan yanda lokaci guda zaice ya fasa saida ya bari ana gobe d'aurin Aure kafin a sanya Ranar Auren karkiga irin rawar k'afar da yake gaba d'aya hankali na ya tashi kaina ya kulle na rasa ta Inda ma zan fara"Cikin tsananin tashin hankali Suka rafka Salati Mama Habi ta mik'e ta ce "Allah ya kiyaye yaron nan ba yaudarar yarinyar nan yayi ba Yayi mata ciki yace ya fasa" ciki"Baba Da ?Mama Zainabu suka fad'a lokaci guda hankali tashe "Yo eh mana ciki inba ciki ba me zaisa yarinya tayi ta kwarara amai Tun safe sannan kuma yazo lokaci guda yace ya fasa ai wannan ba maganar d'auka bace da walaki Goro a miya" Girgixa kai Baba yayi yana dafe saitin zuciyarsa da Yakejin wani irin zafi a dabarbarcewa ya ce "Ba haka bane Habiba na yarda da Zarah d'ari bisa d'ari bazatayi abunda bai dace ba na d'auki hakan a matsayin kaddara Da rubutun Allah ya rubuta ba mijin ta bane Dan haka ku hada lefensu ku mayar musu Har gida" Kallon Mama Zainabu Mama Habi tayi ta ce "Kije ke da su Kande ku mayar musu da kayansu ni kuma bari muje Asibiti wlh abunda nake zargi ya tabbata basu isa ba Saidai duniya ta zagemu amma bai isa yayi wannan yaudarar ba yaci bulus tana komawa d'akin ta samu Zara harta sanya hijab cikin muryar b'acin rai Dan ita daman zafi gareta ta ce " Wuce mu tafi "Asmy ce ta ce "
Chapter 83 · 0% Book details