Sashe 76
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fahimta "Cikin Sauri ta Goge hawayen tace ina sauraranka honey" Hajiya ce tazo kuma take nema na kinsan zancenta bai wuce na Rashin haihuwar da banayi akan na k'ara Aure to shine nake son mu samawa Kanmu mafita tun kafin Abu yazo yafi karfinmu kinsan halin Hajiya sarai"ya nemu ya biye mata maganar ta ta baya Dan karta k'ara shiga tashin hankali "Dukda haka saida hankalinta ya tashi cikin kuka ta ce " to yaya zamuyi Honey ina mafita Bansan yanda zamuyi da ita ba ni kaina na k'agara naga jini na Ina son haihuwar nan fiye da yanda baka zato honey Allah ne bai bani ba "ta k'arasa fad'a cikin kuka " cikin sigar lallashi ya ce "Akwai mafita" Firgit ta d'ago ta Kallesa ta ce "Wace mafita ce Honey" Zamu cewa Hajiya kina da ciki zamuje tare yanzu kiyi pretending din ciwo akwai maganin da zakisha Zai sanyaki amai Dan duk su tabbatar da abun kafin mu nemu mafita"cikin tsananin mamaki ta ce "Idanfa suka gane honey nan gaba Bayan munsan ba cikin garan ba" Ajiyar zuciyaya ya sauke yace kibarmun sauran abunda nakeson kiyi yanzu kenan kawai"Nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Shikenan honey zanyi hakan Allah yasama na samu cikin gasken kafin Su gane" Murmushi ya sakar mata ya ce "Ameeen My Merah" k'arfe 11am tayi musu a Palourn Ammy a lokacin kowa na palourn har Hajiya Har Aunty Zey da tazo Bayan an gaggaisa Amera ma wannan Karin cikin ladabi ta gaishe da su Hartana tambayar Zey ina su Mema Zey Ta ce "suna gidan kakarsu sunje mata yini" masha Allah na kwana biyu bangansu ba ai da sun yarda da sunyi mana Hutu muma"Murmushi zey tayi ta ce "Aikam dai" Chuchu ta k'asar ido take Hararar Amera a ranta ta ce "munafuka batayi mamakin yanda ta gaisa da zey ba saboda daman Chan ita Zey kamewa gareta har mutane suna cewa duk gidansu itace mai girman kai hakan yasa Amera ke shakkarta Dan tasan halinta ba shiga harkar mutane take ba Amma aka shiga tata akwai masifa " Ammy ce ta ce "Chuchu ki kawowa Amera abun Tabawa mana ga Alamun sunshawo hanya" Badan Chuchu ta so ba ta tashi tare da dauko mata juice ta koma Inda take tana Danna waya A cup Amera ta zuba ta fara sha tana cikin sha taji maganin da MD ya bata a mota ya taso mata cikin Sauri ta Aje cup din tare da yamutsa fuska "Ammy ce dake lura da ita ta ce " Lafiya dai ko?Tana yamutsa fuska tace "Naji Inajin amai....bata k'arasa fad'a ba Taji ya tunkaro mata da gudu ta Riga toilet din palourn nan ta fara kakarin amai harta samu ta danyi Kad'an Duka mutanen dake cikin palourn da Kallon mamaki suka bita Hajiya ta ce " Ikon Allah itafa wannan aman me take"Shiru MD yayi ya kyale ta "Har Amera ta fito daga toilet din tana Murmurdewa irin anji jikin nan cike da kulawa Ammy ta ce " Sannu yaushe kika fara irin haka?nafi sati biyu ina yi amma kwanannan yafi matsamun?kuma kunje Asibiti "?girgiza kai tayi ta ce " a a a Ammy bamuje ba"Hajiya ce ta ce "Kinji sakarkaru abunda ake nema shekara da shekaru ya samu shine zaku watsar kunjimun Sakarkarun yara kai kasan da haka shine baka sanar mana tun wuri ba " MD yasan sarai da shi Hajiya take ya kauda kai yana maida Kallonshi ga television "kaji da mugun halinka dai Hajiya ta fad'a tare da Kallon Amera ta ce " Sannu ko bari a kira likita ya duba ki "Murmushin jin dadi Amera tayi ta kwanta kan doguwar sopa tana maida numfashin karya Kallon Ammy Hajiya tayi ta ce " Fatima kirayo likita yazo ya duba yarinyar nan Allah sa abun alkhairi da muka jima muna jira ne ya samu"Murmushi Ammy tayi ta ce "To Hajiya " Nan Ammy ta kira Family Dr d'insu Akan tanason ganinshi zai duba patient "Har lokacin MD hankalinsa gabak'i baya ga y'an d'akin Har Dr yazo Wanda gaisawa kawai sukayi da MD ya shigo Inda Hajiya tayi masa bayanin gwajin da zaiwa Amera nan ya shiga gwadata Inda ya dauki jininta da awon fitsari yaje baima bar gidan ba ya tsaya a mota Bayan few minutes ya dawo rik'e da paper da murmushi a fuskarsa Hajiya na ganin haka ta washe baki ta ce " Kardai kace mun ciki ne Dr "Da fara a a fuskar Dr ya ce"Tana dauke da cikin Wata Biyu " Ai gudar da sukaji Hajiya ta rangadane ya kawo kowa ya maida hankalinta Wajenta "Alhmdll Alhmdllh Allah nagode maka ranar da nadade ina jira gashi tazo da raina da rayuwa kai amma yau rana ce da bazan tab'a mancewa da ita ba a rayuwa ashe da rabon zanga jinin Mustapha a rayuwa kai Allah na gode Maka " sosai Hajiya ta shiga sabbatunta na murna Ammy ma ita kadai tasan farincikin da ta shiga haka su Chuchu da Zey MD ta ido yayiwa Dr d'in jinjina Irin aikinsa yayi kyau murmushi dr yayi masa "Hajiya ce ta kalli MD da babu Alamun yayi farinciki da abunda aka fad'a ta ce " Ikon kaji mai mugun hali ayi maka wannan Babban Albishir da muka dad'e muna jira ka zauna haka sototo ko fara'a babu a fuskarka"Sai sannan MD ya kalli Hajiya Yana hade fuska ya ce "me kikeso nayi nagodewa Allah a cikin zuciya ta Bayan haka me zanyi kuma"tsaki Hajiya taja ta ce Wlh tunda nake rayuwa bantaba ga mutum mai irin bakin halinka ba shekara goma Kana neman haihuwa yanzu Allah ya kawo kaki nuna farincikinka ai nazata likitan dinnanma yau sai anyi mishi tukuici babba" Shiru MD yayi baice komai ba danshi hankalinshi ba anan yake ba "Ammy tayi mamakin yanda MD yayi da murmushi a fuskarta ta ce " Congratulations Baba na Allah ya rik'a"Ameen Ammy"ya fad'a ba walwala a fuskarsa "Zey ce ta ce " Congratulations yaya Gaskiya munyi murna wlh Allah ya raba lafiya"Murmushi itama ya sakar mata ya ce "Ameen sis" Cikin farinciki Chuchu ta ce "Congratulation yaya nayi farinciki Sosai wlh kaima zaka zama Daddy harna k'agara naga fitowar Babynka" Murmushi ya sakar mata Itama Mikewa yayi Ya ce "Ina zuwa Ammy " yana fita da Kallo Hajiya ta bisa tare da tab'e baki ta ce "Allah ya yaye maka wannan mugun Abu" nan fa Amera taga tarairayar wajen Hajiya da da bata kaunarta yanzu ita ce hada cewa me take so a girka mata Chuchu ma dukda basa shiri da Amera sosai taji dad'in samun cikin nata kuma ta tayata murna MD na fita suka had'u da Dr Jinjina masa yayi ya ce "Nagode Dr Dan Allah wannan din ya zama sirri tsakaninmu" Karka samu matsala ranka ya dad'e insha Allahu daga wajena bamaijin wannan maganar"Ajiyar zuciya Md ya sauke Bayan yayi de transfer 200k motarsa ya shiga tare da hade kansa da sitiyarin mota Jaber ne ya fad'o masa arai Tabbas dole ya neme sa dukda yasan har yanzu fushi yake dashi amma dole ya nemesa Dan shine kawai zai iya sama masa mafita dukda waccen mafitar tashi ita ta ruguza komai.. Yau tunda ta tashi takejin jikinta ba dadi ga wata irin kasala da takeji haka dai take daurewa amma ita kadai takejin yanda takeji ga bata iya cin abinci yanzu Kowa daka Kalleta saikagane ta zama so silent ga wani fari da kyau data Kara kowa sai ya lakanta hakan da dilkan amare ce da aka fara mata Sosai hankalinta yake tashe kasancewar Bikinta da Hafiz dake k'aratowa Dan yanzu idan bazata mance lissafin ba saura kwana goma ba wani shiri da take daga bangarenta Dan ko Anko bata fiddo ba haka rabon invitation daga ita har aminiyarta ta basa cikin walwala Musamman Asmy da har wata irin rama tayi Dan kullum da abunnan take kwana take tashi sai kowa ya lakanta hakan da rabuwa ce da zasuyi ya sanya sukayi sanyi yauma Zarah tana kwance Kanta keyi mata ciwo sosai Kamar zai tsage da gudu taji shigowar khairat tana cewa Aunty Zarah"Dukda ciwon kan da Zarah take bai hanata farincikin tarbar y'ar uwar tata ba Rungume juna sukayi Zarah ta ce "Badai har kunyi Hutu ba " Eh Aunty dawowata yanzu kenan bakiga ko unifoam ban cire ba ke na fara nema "Kama hannunta Zarah tayi ta ce " Gaskiya ne Autar Baba Ke boarding dinma amsarki tayi naga hada su kiba kikayi"Dariya tayi ta ce "Kai Aunty wlh ba dadi boarding din Bari naje na cire kaya akwai labari Allah ya taimakeni Ina nan za ayi bikin ki " Murmushi kawai Zarah ta mata tana barin d'akin ta koma ta kwanta koba komai taji dad'in zuwan khairat Dan ta samu Mai d'ebe mata kewa dukda Asmy kullum tana gidan ko kuma idan taje gidansu amma khairat ita har daki daya zasu iya kwana "ya rage saura sati d'aya biki aka kawo Lefe Sosai kowa ya yaba irin kokarin da Hafiz yayi kala hamsin ya zuba mata a akwati dangin babanta da makwafta sai yaba kayan suke Mama Rabi ma ko itace uwar zakalkalewa hada guda " A lokacin Zarah na kwance a gidan su Asmy Dan yau da zazzabi ta tashi Kiran Hafiz ne ya shigo wayarta Bayan ta d'auka ya ce "My love Kinga kaya sunyi maki dai ko ko a sauya sannan dinkunanki da zakisa da biki suna wajen tela katsina insha Allah gobe zasu Iso ina fatan suma zasuyi miki Dan na lura baki da shirin badawa shiyasa na bada maki"Banshiga gidan ba na Kalla ya Hafiz amma nasan sunyi Allah ya k'ara budi " Ai komai nayi maki ban fad'i ba Zarah kin chanchanci fiye da haka "Bayan sun gama wayar sosai Zarah ta fara hawayen tausayin kanta Hakika ta cutar da Hafiz ,ta yaudareshi,taci amanarsa ,batayi masa halacci ba yayi mata Rana tana shirin yi masa dare "dukda tasan ita kanta bada son ranta Hakan ya faru ba K'addarar ce ta zaba mata hakann taya zata iya fuskantar wani da wannan Maganar?Taya Kuma zata yarda A daura mata Aure kan Aure ?wannan wace irin kaddararriyar rayuwace ta tsinci kanta Batasan lokacin da hawaye masu d'umi suka shiga zubo mata ba Maman su Asmy