← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 129

Sashe 79

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da taimakon Asmy da mamansu ta gyara jikinta sosai ta d'an galabaita sannun kawai maman Asmy ke mata ta ce "Baki da lafiya daman?Gyada mata kai tayi ta ce " amma ba Sosai ba "Ikon Allah ai bamuga ta zama ba amarya ba lafiya maza shirya mu tafi Asibiti" A sanyaye ta ce "Mama Bafa wani Abu bane kaina ne kawai ke ciwo kuma nasha magani basai anje Asibiti ba " A a ban yarda ba shi kuma aman na meye ?rasa me zatace tayi ta ce "Wannan maganin ne Mama daman banason shansa shine kawai ya kawomun Tashin zuciya har nayi aman" to shikenan tunda kinki Aje asibitin Maganin nan kam dole ki dinga shansa saboda yafi kowanne amfani bazaki gane amfaninsa ba sai nan gaba "shiru tayi tana kasa da kanta Asmy da duk gabanta fad'uwa yake itafa zargin ciki takeyiwa Zarah Dan duk wasu alamomi na masu ciki take gani a tattare da ita tun a sch bare yanzu da suka dawo gida abun yayi gaba kama hannun Zarah tayi suka koma daki tare da rufe d'akin cike da damuwa Asmy ta ce " Zarah yaushe rabonki Da Perioud? saboda me kikamun wannan tambayar?saboda cire kokonta ki fad'amun Gaskiya "Ajiyar zuciya ta sauke ta ce " Rabon dai da nayi cikakken perioud wata Ukku idan yazo Kad'an yake zuwa kuma kwana daya ya tafi wata biyu baya nayi irin haka Wannan watan ne banyi ba ko kadan kuma naga lokacin ma da zanyi kamar ya wuce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Asmy ta shiga nanatawa ta ce " na shiga ukku Zarah Kardai ace ciki ne dake"a matuk'ar rude Zarah ta ce "Ciki kuma?Eh ciki ni duk alamomin masu ciki nake gani kamar tattare dake " dukda gabanta dake fad'uwa bai hanata Jan tsaki ba ta ce "Lallai baki da hankali Asmy me zai had'ani da ciki nikuwa Bayan nafada maki Watanni biyu baya nayi perioud kuma rabo na da Azzalumin mutumin nan wata Ukku taya kuma zan dauki ciki please kibar maganar nan kar tashin hankalin yayi mana yawa ga wancen bamu gama ba ki b'ullo wani"tagumi Asmy tayi ta ce " Zarah Bazan tabbatar ba har saimunje asibitin ki tashi muje a gwadaki idan akaga babu sannan ne hankalina zai kwanta Amma yanzu babu ni babu kwanciyar hankali"tsaki Zarah taja ta ce "Ba Inda zanje wlh Kuma ba wani ciki jikina Allah ya kiyaye Ya tsareni da Cikin azzalumin mutumin nan macuci ya cuce ni ya yaudare ni Allah ya isa tsakani na dashi " ta k'arasa fad'a hawaye na zuba daga idanunta "Naji ba ciki jikinki Zarah akwai matsala fa Auren nan na gabatowa na fara tunanin kawai mu fito mu fad'a Gaskiya bazai tab'a yiwa muna sane a daura Aure kan Aure ba" a matuk'ar firgice Zarah ta ce "Me kike nufi?ina nufin mu fuskanci su mama da maganar nan" wani banzan kallo na baki da hankali Zarah tayiwa Asmy tace "bantaba sanin baki da hankali ba sai yau taya kike tunanin zamu fuskanci iyayenmu da wannan Maganar hauka muke ,Sannan ya kike tunanin Baba zaiji Lamarin nan Duk wata yarda da Amincewa Baba ya Riga ya bani ya yarda dani 100% da wani ido zamu Kalleshi mu fad'a masa wannan Maganar cewa zanyi na Aurar da kaina kome ai bani da idon dazan iya Kallon Baba na fada masa wannan maganar" kuka ne ya kubce mata Inda ta had'a kai ta gwuiwa ta shiga rerewa gwanin ban tausayi.... Shiru jaber yayi kamar bazai magana ba saikuma ya Ce " A Gaskiya da nace Babu ruwana a sabgarnan bloody Saboda Gaskiya ba k'aramun b'atamun rai kayi ba last time anma ya wuce yanzu me.kake so ayi wannan hukuncin daka yanke nayiwa iyayen ka k'aryar Amera Nada ciki mai bullewa ce kuwa?Nima bansani ba Jaber na zab'i nayi hakan ne kawai saboda ragewa kaina damuwa ina cikin damuwar da bakowa zai fahimci yanda nakeji ba a cikin raina jaber kome nema yake ya jagulemun taya zan nemo yarinyar Chan ina tsananin buk'atarta a halin yanzu"Kaika bata komai tun farko MD me yasa baka sake ta ba tun farko data bukaci hakan da ka saketa da komai yazo da sauki sai mu samu wata manufar amma kin sakin nata da kayi k'alubale ne babba ta bangarenta ka cuceta sannan ta bangarenka kuma bangane abunda kake nufi nakin sakinta ba Yanzu haka Inaji ina gani saboda kai sai blocking din Asma'u nayi Bayan son yarinyar nake Har cikin raina ni kaina ka jazanun matsala wlh"duk yanda MD yake cikin damuwa Kuma yake neman shawarar jaber bai hanashi Jan tsaki ba ya ce "Mu koma magana me mahimmanci meye mafita kasan dai dakai aka k'ulla abunnan to dakai ya kamata a samu mafitar warware matsala" Ajiyar zuciya mai nauyi jaber ya sauke ya ce "Babu mafitar da ya wuce ka saketa" Bazan iya sakin ta ba"Ya fad'a kai tsaye "mamaki d'auke da fuskar Jaber ya ce " saboda me "Saboda ina tausayinta" Murmushi jaber yayi ya ce "Bloody kodai son yarinyar nan ka fara bamu sani ba " Tsaki MD yaja ya ce "kana da matsala Jaber nafada maka ina tausayin yarinyar ne ,na zalince ta farkon Haduwarmu ,sannan na zalince ta a karshen rabuwarmu dole ne na gyara mu'amula ta da ita karta rikeni a zuciyarta babu abunda nake bakin ciki a rayuwa kamar na mutu Da hakkin wani dole ne na nemi yarinyar nan Duk Inda take " numfashi jaber yaja yana ayyana yanayin abokin nasa Har wata rama yayi cewa yayi"Kasan garinsu ne"a a a "Tirk'ashi aiki ja" jaber ya fad'a kafin yace "To me zai hana na kira Asma'u a waya nasan zata d'auka saimu basu hakuri ka saketa ta Cikin wayar Inajin hakan zaifi sauki " wani irin kallo MD yayiwa jaber ya ce "so kake ayi ta maimaita maka magana d'aya To bazan sake ta ba " Ikon Allah to idan baka zaketa ba Me zaka mata ka saketa tayi Aurenta wannan shine adalci"tsaki MD yaja yana maida Kallonshi ga kofa ya rasa abunda yake masa dadi shiru Jabir yayi kafin ya d'ago ya ce "Muyi serious magana Dan Allah saboda me bazaka sake yarinyar nan ba kowa ya huta?Saboda ina zargin cikina a jikinta"ya basa amsa kai tsaye " wara idanu sosai jaber yayi ya ce "what ciki Kuma?Of course ciki?ya akayi kasan tana da ciki?Jabir ya tambayesa" Naga alamominsa ne tattare da ita a takaice yabawa jaber labarin sauyin daya dinga gani a Wajenta har aman da tayi"shiru Jabir yayi sosai ya Lula duniyar tunani kafin ya d'ago ya ce "Ana wata ga wata" Tabbas indai hakane akwai k'amshin Gaskiya to amma tun kafin ta tafi meyasa kak'i kaita Asibiti aka gwadata"naso hakan takiya nikuma banason in takurata hakan yasa na rabu da ita"Tabbas indai hakane ya zama.dole mu nemu garinsu sannan ya zama tilas a dakile Bikinta da nake tunanin ana gab dayi"a matuk'ar zabure MD yace "kana tunanin bikin ya kusa ne " Bama tunani bane confirm Bikinta yana kusa saboda bazan manta lokacin da muke waya da Asmy takan Cemun Bayan gama makarantar su bazai wuce da wata d'aya bikin Zarah ba "Sosai MD ya shiga sabon tashin hankalin da yafi Wanda yake ciki a matuk'ar firgice ya ce " Impossible bazaiyu ba wlh"Mikewa yayi kamar zai tashi sama tare da shiga d'akinshi yabar jaber a palour girgiza kai kawai jaber yayi ya Mike tare da fita daga gidan yana tunanin Yanayin abokin nasa Tabbas indai ba idonsa ne yayi masa karya ba kishi ne yake gani k'arara a idonsa a zuciyarsa ya ce "Ina zargin MD ya fara son yarinyar nan " amma Indai haka ne sonta MD yake Nayi al'ajabi babba Mutumin da bai tab'a fad'awa tarkon son mace ba Har y'ar president ta sosa bai amince mata ba manyan mata masu ji da kudi gayu,mulki,sarauta,y'ay'an manya masu fad'a aji a k'asar ,suna sonsa yana Disgasu amma lokaci guda ya fad'a soyayyar k'aramar yarinya kamar Zarah da ko fari na azo a gani bata dashi"saikuma wata zuciyar ta ce "Amma kuma ba mamaki saboda yarinyar tana da komai daza aso ta tana da sihirtaccen kyau Tako ina tacika ta had'u dukda ba fara bace sosai amma ta ninka wasu fararen kyau nesa ba kusa ba Tana da kyau ,sosai jaber ya dinga sake_sake a ransa ya saka wancen ya since wancen.....MD yana kwance Sosai yake jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa rumtse idonsa yayi sosai da sukayi ja tsabar bacin rai " Tabbas dole na nemo ki duk Inda kike Mamy"ya fad'a a fili Wayarsace tayi ringing ganin Ammy ce ya sanyasa d'auka daga bangaren "Ammy ta ce " Kana ina Baba na wai kwana biyu rabonka da gida Tundaga ranar da akace Matarka Nada ciki baka Kara zuwa gidan nan ba me hakan ke nufi meke damunka wai watanninan na kasa gane maka kaida ya kamata kayi murna da farinciki kyautar da Allah yayi maka lokacin da bamuyi tsammani ba Amma kwata-kwata ka watsar Kamarma baka farinciki da samun cikin Amera "ba haka bane Ammy akwai Uzurrrukan da sukamun yawa ne a harkar kasuwanci na shiyasama amma kiyi hakuri anjima ina zuwa" hmmm harda uzurin dazai hanaka nuna farincikin babbar kyautar nan da Allah yayi maka"Numfashi ya fesar ya ce "Ba haka bane Ammy ina cikin tsananin farinciki da hakan kune bazaku kula da hakan ba " Hmm to Allah ya kyauta saikazo"to"Ammy ya fad'a Bayan gama wayar sosai ya Lula duniyar tunanin Zarah "ina take?ya tambayi kansa". Kwance take ta d'ora kanta saman cinyar Asmy Kallo d'aya zakayi mata kasan hankalinta a matuk'ar tashe yake Kahirat ce ta shigo gidan ta ce " Aunty Zarah Mama Habi(kanwar babanta)sunzo tace a kira mata ke ?Okay jira mu tafi tare "Zarah ta fad'a tana yunkurawa ta mik'e saboda bataji dad'i dauriya ce kawai take Kallon Asmy tayi ta ce " Natafi ba lalle na dawo ba gobe idan na samu lokaci na shigo"Gyada mata kai Asmy tayi da ita tamafi Zarah rama saboda ita kadai tasan yanda takeji ji take inama kome ya dawo baya ,ta gyara kuskuren data aikata ganin irin yanda Asmy ta tayar da hankalinta ya sanya Zarah ta manta da komai na itace silar shigarta wannan halin ta dauki hakan
Chapter 79 · 0% Book details