Sashe 126
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
karkiga yanda mama rabi ta rame ta jeme Niko nace Allah ya Kara aniyarta ce ta kome Mata abunda taso ya faru Dake ne ya Kare a kan y'ay'anta har Biyun baba ma ya dawo shekaranjiya "dukda musgunawar da mama rabi tayi Mata Amma Zahra sai bataji dadin abunda ya faru ba kasa kasa ta Ce "Allah ya kyauta to ya kiyaye Dan Allah Asmy gobe kije ki amsomun number baba kituroman ta sabon layina da na kiraki ashi last week"Okay Insha Allah gobe na turo maki"Bayani sunyi bankwana sai sannan Zahra ta Ciro wayarta da ta mutu ta jona chaji gado tazo Harta kwanta saikuma ta kalli chuchu Dake chart ta Ce "Su Akhbar suna wajen ammy fa har 11 yanzu karsu hanata bacci"Naje daukarsu dazu ta Ce Wajenta zasu kwana akwai madararsu da abincinsu wajenta"Ajiyar zuciya Zahra ta sauke ta ce "Kice yau na kwanta sai safe"Gaskiyar Kam Ammy ta fansheki"Zahra Harta kwanta chuchu ta daddabata ta Ce "Momcy na Manta wlh gulmar Nan tun dazu take cina Wai da kukaje ana fadin abun Nan ya Amera tayi shegiyar Ashe duk Takama da gadara da take Akan kudi da duniya ita ta tashi cikin arziki kaza_kaza Ashe ma kudin dukiyar Kakanki ce kai gaskiya dai Baban amirar Nan yaji kunya wlh "Girgiza Kai kawai Zahra tayi ta Ce"Allah shiryeki chuchu Daman akan wannan ne har Kika tasheni bacci yaudai naji gulma kikeji nikuma bacci nakeji wlh"Dariya chuchu tayi ta Ce "Kamarko kin sani Allah yau y'an gulmar ne a Kai"washegari Zahra ta Kira baba a layinta bayan Asmy taturo Mata number Sosai suka Sha waya da mahaifin Nata sai Dadi takeji sunjima suna waya kafin suyi bankwana cike da kewar juna a cikin satin Nan aka yankewa Abban Amera hukuncin kiss ta hanyar rataya bisa ga rashin gardama da baiyi a Court ba yasanya shari'ar tasu tayi sauki Sai sannan hankalinta MD ya Fara dawowa jikinshi Koda yaje ya labartawa ammy Sosai taji Dadi Kuma tayi hamdala koba komai Shima zaije ya girbi abunda ya shuka a ranar suka koma gidansu shida Zahra tare da yaransa ranar dai Zahra taga yadan warware Wanda da taimakonta hakan ya faru da girki ta shimfida Masa Mai dadin gaske bayan ta dau gayu Kuma ta faranta Masa a shimfida washegari Zahra na kwance jikin MD kan kujera Tana zuba Masa shagwaba Yana biyeta Yaran ko suna tsakar polourn suna wasa da wutsil wutsiltu wayar MD tayi ringing yayi mamaki Ganin bakuwar number ta kirasa da special numbersa da makusantata ne kadai ke kiransa da ita kin dauka yayi Saida aka sake Kira Zahra ce ta Ce "Ka Dauka Mana Hubby ana kiranka fa"Dan kar Zahra ta zargi wani Abu ya sanyashi dagawa daga Bangaren Maman Amera ta na kuka ta Ce 'Ga Amira Nan mustapha zata mutu ba sunan da take ambata idan ba naka ba ka daure kazo ko bankwanar karshe ce kuyi Dan Allah"a zabure MD ya Mike ya ce "Subhanallah mama Kuna wani asibitin "BIBA HOSPITAL"ta fada Masa "Cikin sauri ya katse wayar ya ce "gani Nan"Mikewa yayi hankalinta tashe binshi Zahra tayi ta ce"Lafiya dai?Da sauki Amira ce ba lfy ki koma zanje na gano"ya fada Yana fita waje ba shiri komawa Zahra tayi ta zauna Tana tagumin kome ya samun amirar saikuma ta Tabe Baki ta koma wajen yaranta ta dinga yi musu wasa kafin ta Kara kimtsa Gidan da turarruka kamshi saikuma ta shiga kitchen Dan Dora sabon girki"Soaai MD hankalinshi ya tashi ganin halin da Amira ke ciki numfashima dakyal takeyi "hankalinsa tashe ya kalli Mamanta ya ce "mama tun yaushe ta Fara ciwon"Tun ranar da tashin hankalin Nan ya faru take kwance Daman dai duk zaman da tayi gida ba lafiya ta fiya ba yanzu dai yau batama gane wadanda ke zuwa da dawowa sunanka kawai take iya fada kafin Dr yayi Mata allurar bacci"innalillahi wa inna ilaihiraji'un"MD ya dinga maimaitawa kafin ya rike hannun Amira Yana kallonta yanda numdashinta ke fits dakyal Sosai yaji tausayinta Ganin irin ramar da tayi Yana rike da hannunta Yana ta kallonta Yanajin rashin kyautawarshi na kin. Waiwayarta Wanda a nashi salon Dan ya hora ta ne su zauna lafiya Shi yasan idan yace baya kaunar amera yayi karya kodan sabon zaman shekara goma ai ba wasa ba saidai kawai yaji a ranshi yafison Zahra fiye da soyayyar da yakeyi Mata a Cikin ranshi duk abunda mahaifinta yayi baijin Zai rabu da ita saboda Laifin mahaifinta daban ko a lahira Nata daban Laifin wani baya shafar wani ita kanta Mamanta tayi mamakin yanda MD bai nuna komai ba duk wani abunda za a bukata Saida MD ya bada kudi koda amira ta farka da sunanshi a bakinta Yana kusa da ita ya ce"Bude idonki ki ganni honey nine mijinki a tare dake "A hankali amera take kallonsa kafin ta Fara hawaye ta garkame hannunsa ta Ce "Ka yafemun honey duk Laifin da nayi maka Dan Allah honey inajin a jikina mutuwa zanyi honey zuciyata ji nake kamar zata fashe ka yafemun Kace ammy da su Hajiya su yafemun da duk Wanda nayiwa laifi.."ta karasa fada Tana hawaye"Sosai hankalinmu MD ya tashi rukota yayi Sosai ya ce"Kidaina fadar irin maganar Nan My Merah bazaki mutu ba Zaki tashi mu cigaba da rayuwar mu muma zafin ciwo ne Dan Allah kidaina fadar Haka Kina tayar mun da hankalinna"Murmushi yake kawai Amera tayi "Mamanta ce ta karaso ta Ce "Ki daina fadar Haka Amira kinsan ke daya Kika ragemun a fadin duniyar Nan ke daya gareni ba uwa ba uba ba miji bazan rasaki ba amera zamu rayu"Hawaye kawai Amera take Tana kallon maman Tata ta Ce "ki yafemun Dan Allah mama"kuka Sosai Mamanta ta ke tace bakiyimun komai ba amera Baki da hakkina a tare Dake inma akwaishi na jima da yafe Miki banason kina kalama. Nan kina tayar mun da hankalin"MD ji yake kamar Shima yayi kukan mikewa yayi yaje wajen Dr din domin chuku_chukun a fidda ita waje cewa Dr yayi ba matsala sai a shirya fitar da ita din zuwa jibi "yinin ranar mD Shi yayi jinyar Amira Yana rungume da ita duk abunda take so Shi yake Bata Daren ranar shine baikoma gida ba Saida yaga ta samu bacci sai wajen karfe Sha biyu ya koma gida Koda yaje bai samu Zahra a parlour ba Yana shiga bedroom Amma ganta kwance ita da Yaran su duka suna bacci Banda ita daya same ta Tana kallon gefe Tana tunannika Wanda Saida yakira sunanta tukwana tasan da zuwanshi kallo daya tayi Masa da har bazata Masa magana ba saidai ta danne kishin da takeji Tunda yayi Daren Nan tasan Yana tare da matarsa ta Ce "Ya Mai jiki"Numfashi yaja kafin ya ce "Da sauki dai za ace Amma waje Zan fitar da ita gaskiya ban yarda da kwarewar asibitin ba Tana Shan jiki Sosai ciwon Nata ya dagamun hankalinta"ya fad'a fuska ba walwalar"Allah ya bada sauki"ta fada Tana juya baya tare da rumtse Ido tanajin kishin amera Sosai a ranta "Tana jinshi ya dauke Yaran ya mayar dasu gadonsu na iri Wanda ake turawa kowanne Mai net dinsu kafin ya kwanta ya janyota jikinsa Zahra Najin haka ta marairaice Cikin shagwaba ta Ce "nasan ka shawo gajiya kanason ka yi bacci please ka kwanta yanzu danka tashi da wuri Abbansu Amar"d'an murmushi MD yayi Yana jinjina hikima da wayewa irin ta Zahra Bata iya cemasa ita ta gajine bazata iya ba shiyasa ta sauya. Maganar cikin hikima baiyi Mata komai ba sai janyota jikinsa da ya karayi ya ce"Mu kwanta....washegari tun asuba MD ya wuce Asibitin ba yanda Zahra batayi dashi ba Akan Yama tsaya yayi breakfast Amma yakiya Bayan fitarsa Tagumi tayi tana Jin yanda zuciyarta ke nukurkusa akan kishi wata zuciyar tace Mata matarsa ce fa tun kafin ya sanki suke tare shekara goma Sha ,Bata da lafiya dole yayi fiye da Haka ma '"Saurin mikewa tayi ta Ce "Au'zubillah"Kafin ta cire duk wani kishi da tasa a ranta ta aje gefe saima.adduar samun lafiya da tayiwa Amira Bayan sun kimtsa Gidan tare da taimakon Yan aikinta Nanny din yaran Suma sun shiryasu kitchen ta shiga tayi girki Mai d'an yawa Bayan ta gama komai ta Sanya a warmers a lokacin 1:pm Cikin sauri tayi Wanka ta shirya Cikin kayanta masu kyau Bayan ta Sanya katuwar hijab dinta irin ta larabawan Nan har kasa wayarta ta dauka tare da Kiran number MD Bayan ya dauka ta Ce "ya sunan asibitin na shirya ne Ina son nazo na duba ta "Ki Dan jira minti biyar ga driver Nan zanturo ,zaizo ya kawoki Asibitin"ya fada a sanyaye"Okay"ba ayi 10 minute ba Saida driver yazo ya dauketa ita da yaranta sai nannynsu daya data rike Mata biyu koda suka isa har dakin da Amira take Sosai Zahra taji wata irin faduwar gaba Ganin yanda MD ya rungumo Amera jikinsa Yana bare Mata ayaba dakyal ta iya control din zuciyarta da take Jin kamar zata rabe gida biyu ta gaishe da maman Amera ta amsa Mata Cikin mutunci Dan ta gane ta tare da tambayar ya Yan Gidan ta ce "Alhmdllh"Dagowa MD yayi ya kalli Zahra dayaga ta Dan sauya zamewa yasoyi tun dazu Amma amera ta garkamesa Yana Jin nauyin mamantama Dake wajen Amma tun safe da yazo taki barinshi tashi a sanyaye Zahra ta kalli Amera Dake Numfashi dakyal ta ce "Ina yini ya jikin"Kallonta Amera take da idanunta da suka Fara sauyawa tsabar wahala ta gyada Mata Kai ta ce "Alhmdllh"Kallon MD amera tayi ta Ce"Ce ta mikomun yaran na gansu"Ta fada Tana hawaye kallon Zahra MD yayi ya ce "Mamy d'an Miko Mata su "Zahra ji tayi kamar ta ce "a a a Dan Bata mance lokacin da Amira taso halaka yaran ba dakyal tayi shahada ta Mike da little Dake haannunta ta nufi gadon Mika hannunta Amira tayi tana daga kwancen ta amshe ta "Zaki iya daukarta kuwa"Kirkirarren murmushi Amira tayi ta ce"Eh Zan iya yau jikin yafi koyaushe mun sauki"Alhmdllh Daman haka nake sonji Insha Allahu Zaki warke gobe ne tafiyar da za ayi Dake Egypt"Girgiza Kai kawai Amira tayi Zahra ji tayi kamar zuciyarta ta fashe juyawa tayi zata koma amera ta ruko Hannunta juyawar da Zahra tayi sai gani tayi tana