← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 93

Sashe 9

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashin hankali ne ya sake shigar ta, ta kama hannun Lawwali da qarfi ta ce,

"Yah Auwal ka bar aiki gidan Nan, bana so, in ka ci gaba zan mutu"

Wani Mari ya sakar Mata, cikin tsananin bacin rai,sai da ta ga gilmawar walqiya, nan take nadamar saurin fushin shi ta shige shi, amma ai laifin ta ne, dan ta san ya na son ta shi ya sa take maganar mutuwa,da sauri ya rungume ta, ya na lallashin ta,

"Yi hakuri baraka na, Kar ki qara furta mutuwa akan ki, ba Zaki mutu ba, inshaa Allahu zan bar aikin Amma sai da dabara Inna Bari yanzu ku na cikin matsala, kinji?"

"Ka Yi alqawari?"

"Na Yi alqawari Barakana "

Share Mata hawaye ya Yi, sannan ya ce,

"Kinga yanzu dole ki Sha maganin da muka siyo Dan yanzu kan ya fara ciwo da gaske."

Nama ya miqa Mata gaban ta da komai, ya ce ta ci, ta Sha maganin sannan ya tafi, kasa ci tai ta koma aikin kuka.

Shi kuwa har suka tafi maboyar su bai daina jiyo kukan qanwar tashi da ya ke so sama da kowa da komai a duniya ba.

Dakin shi ya shige ,ya kwanta, kamar ko da yaushe, ba ya shiga shirgin yaran da aka sa su kamawa, indai ba 'yan siyasa ba, kusan a ce ma duk wanda suka kama ba su san shi ba, No 1 zuwa No 5 kawai suka sani.

Sai juya kalman ta yake a ran shi,

'Za mu iya jure rashin abinci, ba za mu iya jure wutar Allah ba'

**********************

Da misalin takwas na safiyar asabar, Isa ne ke zaune a majalisar su ta masu zaman banza, labarai ake ta bayarwa da suka ja ra'ayin shi matuqa, shiruuu ya yi, ya na sauraron su, bai tanka ba, matashin da ake kira da Idi ne ya ce,

"Yau Malam Isa ya shiga tunanin uwar gida, ko dai gida za ka koma ne, kar ka yi laifi"

"Habaa Allah ya kiyaye, ai mata bayin mu ne, sai yanda muka yi da su, da sassafen nan me zan mata a gida inna koma? Zaman gida ai sai matan"

Miqewa Idi ya yi zai tafi, Isa ma tashi ya yi, ya bi bayan shi, sun yi tafiya mai nisa Isa ya ce,

"Ka na ta sauri Ni fa biyo ka na yi game da maganar da kai a majalisa, da gaske ka ke sana'ar saida goro a Makka indai an samu ta shiga akwai riba ?

"Kwarai da gaske, kai baka taba ji ba?"

"To a ina zan ji? Ni ba wasu yan uwa masu maiqo nake da ba"

"To da gaske ne, yanda ka ji din nan, haka abun yake"

"To na gode, zan neme ka inshaa Allahu"

Dariya Idi ya yi, ya kalli Isa sama da qasa, sannan ya tafi ya na dariyar ina Isa zai samu kudin siyan goro ya kai Makka, balle ya samu na kujerar tafiya makkan ?

Isa gari ya shiga, ya dinga yawo, domin neman qarin bayani akan sana'ar saida goro, abun ya kidimar da shi ,yanda ya ji ana samun kuɗi, ai kuwa ya qudiri aniyar fara saida goro, shi ma ya fita layin su Dan Talo , wato masu mutuwar zuciyaaaa......

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 10:

Tissue ce a qasa jiqaqqu an wurgar a tsakiyar parlour'n, ba abinda ke tashi sai sautin kukan Sultana ,jikin ta sai rawa ya ke, idanun ta  da fuskar ta sun yi jajawur, abinka da farar fata, kallon wayar ta sake yi a karo na ba adadi, ta na kallon wani video ne a YouTube, mata ne da yara tare da mazaje na wani qauye da ke a cikin garin Zamfara aka yi wa barna, an karkashe mata da qananan yara, mazajen su an masu yankan rago,gidaje na ci da wuta, wasu daga cikin iyayen na ta rusa kuka, an dauke masu 'yan matan yaran su, wata mata ta na kuka ta na fadin,

'A gabana yakkashe ta, yabbi ta ya taushe-a gabana ya kashe ta, ta bi ta ya taushe... Fyade) , mahaifin ta ya tai  wajen, kar a ci ma diyatai mutunci, sun ka yanka shi, ina gwaunati take? Shin ba mu da masu taimakon mu ne? Ana kashe mu, da diyoyin mu, ana halaka dukiyoyin mu, yanzu ki duba gidajen can da an ka bankawa wuta, ina na zamu koma? Wa zai karbe mu? A dangi wa muka ajiye da zai amshe mu da lalurorin mu? Kowa ya na fama da kai nai a wanga yanayi na matsin rayuwa'

Kuka ne ya ci qarfin matar da ke magana, da dukkan alamu ita kan ta 'yar jaridar kuka take, Sultana kuwa kamar ta sume saboda tausayi,Lamishi na tattare tissue da Sultana ta ke zubarwa ta na hawaye.

"Uwar daki na ki yi hankuri, masu aikata wadan ga muggayen laihukka(laifuka) ba mutane na ba, domin shi mutum ba shi kisan dan uwa nai, kuma su ba dabbobi na ba, domin ko zaki bauna da barewa suna cin abinci kusa da shi bai tabe su ba, saboda a qoshe yake, duk kin ka ga dabba ta kashi 'yar uwar ta, to yunwa taka ji, wadan ga mutane ba aljanu na ba, domin aljani ma sai an masa wani abu yake daukan fansa, ko kuma wasu daga azzalumai suna aiki da su, suna sanya su aikata mugunta, wadan ga mutane Allah dai yassan su, kuma shi zai muna maganin su, uwar daki na kukan ya isa haka nan, zaki zazzaɓi"

Cikin tsananin kuka Sultana ta ce,

"Baba Lamishi Ina za su tafi? Wandancan gidajen su ne gidajen su, an qone su, an yanka wasun su, kuma an sace matan su, ya zuqatan su suke a yanzu? Baba Lamishi what if su ma aka tunzura su, tunda ba mai taimakon su, suka fara irin abinda aka musu? Shin laifin waye ? Waye silar samar da ta'addanci a qasar nan ne? Ya Allah ka kawowa bayin ka agaji a cikin wannan musibar rayuwar da suke fuskanta,"

Kukan ta ne ya qaru da ta ga wata mata ta fita da gudu, ana tare tare, ashe a gaban ta aka yanka mijin ta da matashin yaron ta, aka tafi da yan matan yaran ta uku.

"Ke Lamishi,amshe wayar nan ki kashe, sanan ki tashi ki tafi,"in ji cewar Hajiya Ikee da ke isowa cikin parlour'n cikin b'acin rai.

"To Hajiya, Allah ya huci zuciyar ki, ran ki shi dade,"

Wayar ta karba cikin ladabi, ta kashe, sannan ta ajiye a gefen Sultana, ta qarasa tattare tissue din zata fita, Sultana ta miqe dan komawa dakin ta, wani jiri ne ya ɗebe ta, ta kuwa tafi luuu za ta fadi, Hajiya Ikee da Lamishi suka tare ta, Hajiya sakin ta tayi, Lamishi ta kai ta har dakin ta, ta taya ta ta kwanta, ta rufe ta, soyayyar Sultana na huda duk wata gaba ta jikin Lamishi, domin tausayin ta ga talakawa, da da hali ita aka damqawa shugabancin ba mahaifin ta ba.

Ko da Lamishi ta koma parlour kafin ta Isa ta ji Hajiya na bayanin dalilin zubar tissue Mai datti a qasa,

"Sultana ce fa, daga ganin abinda ya faru a wannan qauyen da ake ta haskawa a gidajen talabijin da kafafen sada zumunta shi na duk ta daga hankalin ta, yanzu haka ta na daki kwance"

"Wai me ya sa ba ki jin magana, shin ban hana ki barin ta kallon irin wadannan shiraruwa ba? yanzu da ta ji sauqi zata yi ta tambaya ta kamar ni na kashe su"

Da qarfi ya ke tafiya cikin bacin rai, wanda bai boyu wa, cikin zuciyar Lamishi kuwa cewa ta yi,

'Dan buta uba mai suhhwar tumakin Dan Talo, wanga mutuni mara tausayi Allah ka yi muna magani nai,'(Dan buta uba mai siffar tumakin Dan Talo, wannan mutumi mara tausayi Allah ya mana maganin shi)

Lamishi bata fita daga qofar dakin Sultana ba, sai da ta ji qarar rufe qofar shi ,Hajiya ta bi shi ta na ta bashi hakuri, ya na ci gaba da zazzaga masifa, kwashe komai ta yi ta je ta zubar, jikin ta duk a sake.

Har suka gama aikin su bata sake walwala ba, lokaci zuwa lokaci ta na leqawa dakin Sultana ta ga ya take, kukan dai shi take yi, kamar a lokacin ta ke ganin abinda ya faru.

Lokacin da Lamishi ta yi shigar qarshe dakin Sultana ta gan ta zaune ta na tunani mai zurfi.

"Uwar daki na lafiya? Ko na kawo maki abinci ne ki dan taba kadan? Saboda ke ne kawai ban tahi gida ba,"

"Lamishi, Ni kam na tambaye ki mana,"

Da sauri Lamishi ta zauna a gefen Sultana ta Bata dikkan hankalin ta,

"Dan Allah gidan ku ya yake?.. Amm... Ina nufin akwai sirri? Wani zai iya zama ba tare da an sani ba?"

"Tab gidan mu yanda ki ka san bakin kassuwa haka yake ,kowa shiga yake, maza na qofar gida, mata na ciki, dan dai a ci abincin da muke tahiya da shi, da an gama ne dai baki koma ganin wasu sai wanshegari"

"Ok, ba komai jeki kawai,....kuma ba ki san ko ina ba da mutum zai iya zuwa na sirri haka?"

"Gaskiya ban sani ba..... uwar daki na, in hasashe na ya Yi daidai, ke ce ke son fita daga gidan ga ko?"

Shiru Sultana ta yi, ta juyar da kan ta, hawaye na tsiyaya a idanun ta, jin ta take kamar a gidan kurkuku

"In haka kike tunani ran ki shi dade ki bari, domin zaman ki anan shi ne ruhin asirin ki da kariyar ki, kinga duniyar da ke a wajen gidan nan? Duniya ce ta azzalumai, duniya  ce ta daukan rai ,duniya ce ta shan jini, da kwace muhalli, duniya ce azzaluma,duniya ce cike da miyagu masu raba Mata da maza da mutuncin su, zaman ki a inda iyayen ki sun ka killace ki shi kad'ai ne kwanciyar hankalin ki da kariya a  gare ki"

Cikin kuka Sultana ta ce,

"Su kuma bayin Allah da ake kashewa fa? Haka za su ci gaba da rayuwa?"

Tashi ta yi da gudu ta fita daga dakin,
Chapter 9 · 0% Book details