← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 93

Sashe 53

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani abu sai ka zo Makka,takarun nan na nan Alhaji, bari kawai, sai ka zo kawai, yanzu mu yi magana akan wannan babbar harqallar da za mu hada,"

Nan Isah ya sanar wa da Laminu duk irin abinda yake son su yi, cikin dariyar kwararrun 'yan duniya Laminu ya ce,

"Shegen sama, ka na son ka hini iya tsiya hwa"

"Babu komai, kai ne dai uban gida na"

Sallama suka yi Laminu ya duba wayar shi, ya ga Isah ya tura masa da No da zai kira, nan da nan kuwa ya danna kiran yaran shi biyu, ya basu umarnin da ya dace da abinda suke qullawa,barin gidan ya yi ya tsaya nesa da unguwar su sosai, sannan ya cire sim din shi da yake amfani da shi,ya sanya wani ya danna kiran No da aka tura masa, cikin maqale murya ya ke magana, ya na gamawa ya cire sim din ya karya shi ya yar, sannan ya tada motar shi ya bar wajen.

************************

"Yaya ba fa zaki hushi ba akan abinda ya faru ki ce baki koma zuwa aiki, ke ma ke san aikin da mukai ba wani aiki bane, alfarma ce dai aka mana ba komi ba, walaqanci kuwa ba kalar wanda bamu gani ba a baya"

"Wani ya taba kiran mu da barayi? Cewa fa tay-yi in mun tai su na rasa abubuwa, ana musu sata, Allah na tuba duk a halaye na marasa kyau bana sata bana maita, yo akan cin mi, za a ce na yi sata?"

Dan Talo ne ya ajiye butar hannun shi, ya zauna a bakin qofar dakin su Jameelu, ya wage baki ya na hamma.

"Ke dai san in baki tai ba yawan abinci na raguwa ko? Tunda in an tashi kason ragowar abinci ba a kasawa da na ki, tunda baki tai ba, ko wanda aka dafa wa masu aiki ba a sawa da kason ki, ko dai baqin ciki ki ke mana"

Wani mummunan kallo Lamishi ta watsawa Dan Talo, cikin bacin rai ta ce,

"Ban zuwa din, lalataccen yohi kawai, baka da aiki sai son banza, baka b'arkata komi a gidan ka sai dai mata su maka, kaii Arrrr, tur da miji irin ka, ni na rasa ma mi na sa na aure ka, ba fusss, ba ka da lissahin da ya wuce wanne abinci muka kawo, da ya akai ya qare kamar kai ka nemo, baka nemo ba amma ka iya bin diddigi, kai....."

Mai buruji ta san in aka bar Lamishi sai tai awa uku tana zage Dan Talo, gashi lokaci na ta tafiya, dan haka ta katse ta ta ce,

"Yaya ki wa Allah, ki rabu da wanga mai matacciyar zuciya, ga hijabin ki na doko miki, mu tai ki dena ganin shi ko ran ki ya yi hwari, ni kai na mamaki ni kai, wai hankalina na ina sanda ya je garkar mu neman aure na, har na amince na auri miji kamar shi"

Dan Talo ne ya miqe tsaye ya na dariya ,ko haushin zagin da suke masa baya ji, ya kade rigar shi ya ce,

"Haka dai kun ka ganni kun ka ce ku na so"

*************************

Driver take ta jira ya dawo daga inda duk ya tafi ya kaita asibitin amma shiru, ta tambayi mai gadi ya ce be jima da fita ba, bai san inda ya tafi ba, gani ta yi lokaci na tafiya, bata san takamaimai me ya faru ba, har aka kira ta, cikin sauri ta dauki hijabin ta saka jakar ta dauka ta fita harabar gidan.

Makullin mota ta fitar daga jakar ta, tare da bude daya daga cikin motocin gidan, zama ta yi ta kunna, tare da danna horn da qarfi, cikin tashin hankali da damuwa ta bar gidan.

A hanyar ta ta barin unguwar tasu ta ga wani yaro a saman titi ya na ta tsala kuka, cikin sanya birki mai qarfi ta tsaya gaban yaron, fita tayi ta duqa zata tambaye shi daga ina yake dan da ganin shi ba a irin gidajen unguwar yake ba.

Wani abu ta ji an fesa mata ta shaqa, kan ta ya mata nauyi, kafin jiri ya qarasa diban ta ta kai qasa an tare ta, da kyar suka ciccibe ta suka danna a motar su, suka sanya wata takarda a motar ta daidai mazaunin driver, suka ja tasu motar a guje su ka bar waje . ......

*Allah ka shiryi kilimapas*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 40:

Inda suka saba ajiye mutane nan suka kai ta, suka yi wa Laminu waya, ya isa, ya na zuwa ya leqa ta bulin da ya saba leqen wanda ya sa akamo,  agogon hannun ta da sarqar wuyan ta ya sa su cire su kai masa.

Ko da suka ciro ya jujjuya su a hannun shi, ya girgiza kai, a kiyasi in aka siyar za su kai million daya da dan motsi haka, murnushi ya yi, ya ce,

"Aikin ku na kyau, yanzu ku taho mu tai, a saishe da wanga, sai na baku kuddin sallama a ciki, dan wannan kayan da kuka gani, mai hatsari ne, ba zan so ku zauna kusa ba, asiri ya tonu, a yi kame da ku"

Godiya suka yi ta yi, dan ba wani wayo ne da su ba, ya samu irin majiya qarfin qauyawan nan ne kawai su na masa aikin da ya so, ya sallame su da kudi qalilan su tafi su na murna abin su.

Ya kira Isah ya sanar da shi duk abinda ke faruwa, Isah ya sanar da shi duk wata hanya daya kamata ya bi,dan ba ya so ma abun ya dad'e, gudun tonuwar asirin su.

*************************

Asshibi ce ta yi lullubi ta tafi gidan Hansatu, ta na zaune ta na tsintar gumi, (shinkafa yar gida kenan) ta ji sallamar Asshibi.

"Ahh ah maraba, Bismillah shigo"

"Ba zama zan yi ba, na dora sanwa, wayar ki ce ke ta kuka, na ce bari na kawo maki, wataqila kiran na da mahimmanci, ko mutanen Saudiya na sun ka kira, na taho shigowa na ga waccan wahalalliyar matar garka, ita da abokiyar  fadan ta, har sun shirya kenan?"

"To ina na sanin musu, ni da ke cikin gida, Allah ya sa sun shirya din ne, ai hwada ba dadi"

Dan guntun tsaki Asshibi ta yi, ta ce,

"Ke ai ba ki son rikici, gashi nan an sake kira ki doka"

Da sauri kuwa Hansatu ta amsa, zuciyar ta na tsananin fata da begen Allah ya sa mijin ta ne, wata iriyar murya ta ji, na mata magana,

"Ke ta Hansatu ko?"

"Eh ni ta, da wa naka magana?"

"Ba ki da buqatar sanin wanda ka batu, ki sanar da yayan ki, mun dauke Hajiyar ku, mu na da buqatar kuddi kafin mu sake ta, in kun kawo yau, ba tare da kun sanar da jami'an tsaro ko wata hukuma ba, yau din ga muna sako maku ita, amma in kun tsaya bin diddigi da kwakkwafin mu, tau ku na ganin gawar ta kuwa,ko da an kama mu mun dai kashe ta"

Hawaye sun jima da wanke fuskar Hansatu ba abinda take kira sai Innalillahi wa inna ilaihirraji'un.

"Bawon Allah, ka yi wa Allah kar ku cutar min da ita, zan sanar da yayana ko nawa kuke so indai muna da shi za a baku, dan Allah kar ku cutar mana da ita,"

"Zan sake kiran ki"

Kuka take sosai ta na neman hijabin ta, da dan kudin ta da zai kai ta gidan su.

Asshibi na tambayar ta me ya faru, ta na kuka ta na sanar da ita komai,

"Dan Allah ki min alfarma diyan ga su zauna wajen ki, har na tai na dawo"

"Ba ya da komi, Allah shi bayyana ta cikin aminci, wadannan mutane masu aikata wadannan laihukka Allah shi tona musu asiri azzalumai, su ko satar ma ba basu iya ba, su rasa wadda za su dauka sai boyar Allah, irin Hajiya mace mai sauqin hali, da halin kirki, anya masu satar ga basu san ku ba kuwa?"

"Hummm Asshibi kenan, su ina ruwan su da halin ta, in ba na kuddi ba? Tunda ko sun san ta na da halin kuddi ai shi ne dalilin dauke ta, bari na tai,ku yi ta taya mu da addu'a dan Allah"

"To Ummaa sai kin dawo, Allah ya bayyana Hajiya lafiya" in ji Ameena, da ta fi sauran 'yan uwan ta wayo, dan haka ta fahimci me ke faruwa.

"Ameeen"

Kafin ta kai bakin titi yayan ta ya kira ya sanar da ita, an kira shi an fada masa an sace Hajiya, sun fadi cewar a basu milliyan ashirin, sun yi ciniki za a basu million goma, yanzu hada kudin yake ze kai, ta zauna a gida ba sai ta fito ba, kar a yi biyu.

(Mutane na kuskuren qin sanar da jami'an tsaro irin wadannan abubuwan, ko dake jami'an tsaron suma tsoro suke ji, Allah dai ya bamu tsaro da kan shi a wannan qasa da duniya baki daya)

Hankalin ta bai kwanta ba, amma bayanda za ta yi, dole ta koma kamar yanda ya Umar ta, ashe ma sun kira Yayan nata shi ne suka kira ta kamar ba su sanar da shi ba, Allah ya saka musu, ya bayyanar da Hajiya lafiya shi ne addu'ar da ta dinga yi, har ta koma gida, ta na zuwa kuwa ta tarar da su Asshibi na qoqarin rufe gidan, za su tafi, labarta mata komai ta yi, ta mata godiya, akan ba sai yaran sun bi ta bama tun da ta dawo.

Ko da suka shiga gidan alwala ta yi ita da yaran ta, suka yi nafila, raka'a biyu, sannan suka yi ta addu'a, ba qaqqautawa, akan Allah ya kare Hajiya ya bayyana ta da gaggawa cikin aminci .
Chapter 53 · 0% Book details