← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 93

Sashe 62

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takardar ta bude ta karanta kamar haka.

~Hafsat ina fatan ki na lahiya da jikoki na? Na san dai mijin ki ya sanar da ke shi na nan dawowa qarshen wanga sati, to ga kayayyaki nan,ki yi amfani da su yadda na nuna maki rannan da ki ka taho, sannan wannan bagaruwar da ganyen magaryar, ki na diban bagaruwar kadan da ganyen magaryar ki tafasa ki zauna ciki, amma a yanzu ki dauki bagaruwar danyar ki matse ruwan ta ki liqe a wannan haqorin da ya bule-

Ta na gama karantawa ta dinga dariya,dan ta gane haqorin da Hajiyan ta ke nufi,Hajiya akwai hikima, ta tuna sanda take mata complain din ta na jin gaban ta kamar ya bude, shi ne Hajiyan ta yi wannan dabarar,dariya ta dinga yi, sanda ta tuna, wani lokaci kafin auren ta, an yi auren qanwar Hajiyan, sai suka je gidan, suka shiga har dakin amaryar suka ga gadon amaryar duk ya ɓaci, ta na ganin Hajiya na kallon wajen, sai ta cire dankwalin ta ta rufe wajen, ta na ta jin kunya.

Bayan sun koma gida sai Hajiya ta haɗa dankwalaye ta bawa Hansatu, ta ce ta kai ma auntyn ta ta ce mata, in ji Hajiyan wai ta yi amfani da dankwalin nan ta rufe saman gadon nata saboda qura, amma da zata cire ta wanke qurar da ya fi.

Sai bayan ta yi aure a washe garin daren ta na farko ta fahimci me Hajiya ke nufi da hakan.

Ta na tsaka da dariya ta koma kukan baqin ciki, Wannan wace iriyar rayuwa take ciki? Wai ace mijin ka bai damu da kai ba, yau kusan watan shi daya da tafiya, ba kira ba saqo, sai dai ta ji maganar shi a bakin mahaifiyar ta, ba komai, za ta bashi mamaki.

Tattare kayan ta yi, ta ware duk wanda ya kamata ta ware, sannan ta kira su Ameena ta deba musu soyayyan naman suka ci, cikin nishadi.

**************************

"Ni fa Sultan ban san me ke faruwa ba, yau kwana biyu kenan, ina kai qawaye na gidan su Sultana Amma ina ganin gidan a ruhe ,shin lahiya? Ko ba kuyin waya ne kaima? Dan ni dai na kira layin ta ba shi shiga"

"Ni ma dai layin nata bai shiga Hajiya, amma na san duk inda take ta na tare da mijin ta, kar ki damu"

Ai sai a wannan lokacin ne hankalin ta ya shiga jikin ta, a zabure ta miqe, ta hau kiran layin Gwamna Halliru, ta kira ya fi sau hudu ana sanar da ita ya na meeting,daga qarshe masifa ta balbale mai amsa wayar ta ce ya kai ma gwamna wayar shi, ba ruwan ta da wani meeting ita.

Yanayin yanda ta daga hankalin ta ya bawa Sultan Mamaki.

Mene ne abun damuwa dan an ce mace na tare da mijin ta ba kwarto ba????......

*Gane min hanya Sultan, wai makaho ya so gulma*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 46:

Fitowar gwamna Halliru daga meeting ba wuya, Hajiya Ikee ta sake kiran wayar, da  sauri aka miqa masa ya karba, bayan ya amsa ne ya kara a kunnen shi,jin Muryar Hajiya cikin tashin hankali ne ya sanya shi matsawa daga cikin mutane, ya fara tambayar ta dalilin tashin hankalin ta, Sultan ta kalla wanda ya dauki remote ya na sauya tashoshi hankali kwance, ta ɗan matsa daga inda yake, ta fara magana.

"Sultana fa da wannan shegen yaron ba su gidan su,ni ina jin tsoro musamman tunda ka ga basu fada muna inda su ka tafi ba, Kuma gashi ba a samun ta ga waya"

"Kwarai da gaske yau nake so na tambaye ki ko ku na waya, ban samu dama ba, tunda ban kwana gidan ba, amma abin ya na dauren kai ace ba ta kiran kowa, bari zan bincika in ji, ki kwantar da hankalin ki, kin dai san ba yarinya bace ke, tunani kadan zai sa miki ciwo"

"Wai kai in ba ka fadan baqar magana ba baka jin dadi ko? To ai na san ba yarinya ni ke ba, ba se ka maimaitan ga kunne na ba"

A hasale ta kashe wayar ta koma ta zauna, tunani ya mata yawa, ina su Sultana suka tafi?

Miqewa ta yi ta haye sama, Sultan na bin ta da kallo, tunawa ya yi, me ya sa wai ba zai kira Lawwalin ba, ya ji su na ina?

Gwada layin Lawwali ya dinga yi be samu ba, murmushi kawai ya yi, da dukkan alamu ba sa qasar nan, kallon shi ya ci gaba da yi hankali kwace.

****************************

Hansatu ce ke ta duba kayayyakin da babu a gidan,ta na ta rubuta abinda za ta siyo in ta je kasuwa, gani tayi garin da Hajiya ta haɗa mata, take kunu da shi ya qare, gashi bata san kayan hadin ba, daki ta koma ta dauki wayar ta, ta kira Hajiyan, sai da suka gaisa, sannan ta ce,

"Hajiya kayan hadin garin kunun nan ni ka so ki hwadi min, ya qare, ina so na hada wani"

"Tau ki na ji ba, in kin je kasuwa, ki bidi wajen masu awo, ki siyi, alkama Sa'i guda (kwano daya/mudu daya), ridi rabin sa'i,(kantu) farar shinkafa rabin sa'i , aya irin qananan nan na kunun aya rabin sa'i, sai ki tai wajen masu Islamic chemist, sun fi saida hulba mai kyawu, ki sai hulba mai kyawu roba biyu, ki sai diyan ('ya'yan) habbatussauda, to da kin dawo gida gyara kowannen su za ki yi, ki wanke, ki busar, hulba kuma ki soya ta haka nan, sai ta yi qamshi, sai ki game su, a niqa miki kamar gari, sai ki zanka damawa ki na sha da madara, wannan hadin man shi na nan be qare ba ko?"

"Eh Hajiya be qare ba, ko ba man tahwarnuwa (tafarnuwa) da man hulba, da man zaitun, da man hancin kade, (kaninfari) ba? Shi na nan ina yin matsi da shi, kuma na ji sauqin qaiqayin da na ke ji sosai, na ji har da matsi shi na yi Hajiya,"

"Kwarai da gaske shi na da kyawu kwarai wallah, tau yanzu ga wani ki siyo in ki na tahowa, ki siyo man zaitun, da man hulba, ki game su waje guda, ki Zanka shafawa ga maman/nonon ki, shi na da kyau kwarai kwarai,"

"To Hajiya na gode sosai, Allah shi saka maki da alkhairi"

Sallama suka yi, ta kira Ameenah ta ce ta kula da gida,da qannen ta, ta ce ta kulle gidan, in an buga bata leqa ta gan ta ba, kar ta bude ko da ta ji Muryar ta,ta sanar da ita za ta duqar da kanta jikin wata yar bula da ke kofar in suka hada ido to sai ta bude mata.

Ta na fita kuwa Ameenah ta yi kamar yanda Umman su ta ce, Ita kuwa hansatu bakin ta dauke da addu'ar bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala quwwata illa billah ta bar gidan, ta na tafe ta na yin dik wani tasbihi ga Allah da ya fado bakin ta.

Hansatu saboda ta san ta bar yara su kadai bata wani jima ba ta koma.

Sai da ta musu abinci, ta gyara gidan sannan ta samu carrot da cucumber ta goga su a abun goga kubewa, waje mai qanana qananan, sai suka fito kamar an markada su, ruwan ya fito sosai.

Tace ruwan ta yi, ta zuba masa zuma, da lalle, da madara kadan, sai sugar da dan gishiri, sai baking soda da ta siyo, ta fasa kwai guda daya, ta matse lemon zaqi daya, da lemon tsami daya, sai madarar turare mai qamshi, sai kurkur, ta juya sosai sannan ta bi jikin ta duk ta shafa, Ahmad ne ya dinga nuna ya na jin tsoro, ai kuwa ta dinga bin shi, su na ta guje guje da wasa da yaran nata, su na kyalkyala dariya.

Bayan ya yi awa daya ta je ta wanke jikin ta ta yi fesss.

Man carrot din da ta hada sati biyu da suka wuce ta dauko ta ga ya yi yanda ake so, ta tace, ta diga masa madarar turare ta shafe jikin ta da shi, nan da nan ta dau qamshi da kyalli, duk wanda ya san Hansatu a baya, ya gan ta yanzu ba zai tabbatar ta samu sauyi mabayyani, ta hadu ta hadu ta gaji da haduwa, ta cika ta yi bul bul da ita.

(Yanda ake hada man carrot, za ki wanke carrot din ki ki kankare dattin ki goga a abun goge kubewa, ki zuba a mazubi mai murfi, sai ki kwara masa man zaitun/kwakwa ki rufe, duk bayan kwana biyu ki dauko ki juya ki juya,ki mayar ya qara kwana biyu, a haka har sai ya kai sati biyu, zaki tace, ki na shafawa ya na matuqar gyara fata kwarai)

Hansatu dai da yara kullum a cikin gyara gida suke da kan su, ta sanya sabuwar ledar daki, ta sauya zanin gado da labulaye, ta sauya masa food flask ,ta sauya masa jug da spoons,hatta da sleepers sai da ta sauya masa, ta sai masa towel din wanka.

Yau ma kamar kullum sun gama gyara gida Hansatu na zaune ta na kallon qaramin madubi, ta na ganin yanda fatar ta ke sheqi, kalar ta mai ruwan cakulan mai duhu na komawa wani ruwan madara mai haɗe da coffee kadan, sai zabga murmushi take, dan ta san ta gama komawa mace mai aji, macen da ta fi qarfin walaqancin namiji, ta kowanne fanni, sauran abu daya take so ya faru, dan ta qara kankaro darajar ta.

A baya rashin kudin gyara jikin ta, da rashin bata abincin da zata ci mai kyau ya gina mata jiki, ta amfana shi ma ya amfana da ita, ya sa duk ta lalace ta kowanne fanni, hatta da gashin ta a da ya lalace, ba wani tsaho ba kyawun gani, dan ko man kitso bata da shi.

Komai nata a lalace a wulaqance, amma a yanzu wannan Hansatun ta daban ce, dan ko a da ba ta yi wannan haduwar ba, a yanzu in Isah ya gan ta ya kuma kusance ta bai sauya hali ba, to ba zai taba sauyawa ba.
Chapter 62 · 0% Book details