← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 93

Sashe 46

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tayi kewar ki fiye da yanda baki tsammani, amma lokaci ba zai bari ba, na san yanzu haka ta na sallah, bari na kira na hada ku,gobe da asuba zan kai ki gida, daga nan mu wuce tasha, duk wanda kin ka gani a matsayin wanda zan hada ku, ki yarda da shi, na san ko waye shi,ki yarda da shi,ba zai cutar da ke ba, na sai Maki waya da komai da zaki buqata, na sai gida duk da sunan ki, na sai motar da za a dinga hidima dake makaranta da duk wani abu da zai inganta rayuwar ki Baraka na na yi miki, hankalin ki kawai ni ka so ki kwantar,duk sanda ki ke da buqatar gani na ki hwada min ko a waya ne zaki ganni ke ji?"

Ba abinda take in ba kuka ba, ba ta jin za ta iya jure zama ba shi, amma ba za ta iya masa musu ba.

Da misalin hudu da rabi na asuba ya kira sultana, kamar ya sani kuwa sallah take, sai da ta idar ta kira shi, jin Muryar Mubaraka ba qaramin dad'i abin ya mata ba, ajiye wayar ta yi ta yi sujjadar godiya ga Allah sannan suka hau hira, duk kalar tambayar da Lawwali ya hana ta amsawa bata amsa ba, sai dai ta ce bata sani ba itama.

Biyar saura minti goma suka yi sallama Mubaraka ma ta yi alwala ta yi nafila.

Ta na idarwa Lawwali ya sa ta yi wanka ta ci abinci, sai gidan Alhaji Dan Talo.......

*Ai na manta ashe bai je Makka ba😂😂🤭*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 36:

Tun sanda Lawwali ya girgide musu qofar ya jingine, har yanzu ba a samu mai zuciyar da ya tsakura daga kudin da Lawwalin ya ke basu ba aka gyara qofar, dan haka yau ma da qafa ya daki qofar ta bude, ta na kaiwa qasa hankulan mutanen gidan da maqotan su duk sai da ya tashi, domin qarar ta yi matuqar tsorata su.

Mubaraka ce ta kalle shi ta kada kai, dan ta gama fuskantar a fusace yake, ba dan ta matsa masa ba ba za su je ba.

A tsaitsaye suka tadda mutan gidan, cikin sallallami da jimamin me ke faruwa, idanun su na sauka akan Mubaraka, murna ta kama su, musamman su Jameelu, wanda sai da suka runtuma a guje wajen ta, za su taba ta Lawwali ya dakatar da su, ba musu suka ci birki.

"To kin gan su mu tafi?"

"Yah Auwal ka bani minti goma dan Allah"

"Whatt? Minti goma? Mi za ki yi halan?"

Takawa ta yi gaban Lamishi da ke ta wangale baki, har cikin tsokar zuciyar ta ta ji dadin ganin 'yar ta ta, haka ma Mai buruji da Dan Talo, amma su na jin tsoron zuwa gare ta ɗan tijarar nasu ya musu rashin mutunci.

"Umma na, na dawo, Alhamdu lilLAAH, Yah Auwal ya kwato mu daga hannun azzaluman da sun ka sace mu ni da su Murjanatu, Ummana na yi kewar ku sosai, duk sanda na tuna ku ina can, sai na ji hankali na ya tashi, sai in dinga hango wa zai dinga miki girki in ba abinci? Wa zai gyara miki daki? Wa zai zanka kai miki ruwan wanka ke da Baba, wa zai zanka shara da wanke-wanke? Ummaa na sai in dinga tuna wa zaki dinga yi wa hwada in ya yi ba daidai ba? Hankali na na tashi inna tuna duk sanda ki ka tashi baki ganni ba wane irin qunci zuciyar ki za ta shiga,.......ashe.....ashe ni damuwar banza nikai, hankalin ku kwance shike da bata na, na so matuqa na ci gaba da zama da ku, domin ko zuciyar ku ba ta so na, ni tawa zuciyar na son ku da qaunar ku, amma a halin yanzu zan bi yaya na, duk inda ya sanya qafa nan zan aje tawa, na gode da zama iyaye da kuka yi a gare ni na tsawon shekaru,za ku ci gaba da kasancewa iyaye na har abada, sai watarana"

Cikin hawayen da ke ta zuba mata ta juya za ta koma wajen Lawwali da zuciyar shi ke ta tafasa, ya na jin zafi da takaicin abinda suke wa Mubaraka duk da ta kasance yarinya mai biyayya, Lamishi kuka take sosai na nadamar abubuwan da ta aikata, amma ba yanda zata yi ta hana Mubaraka bin Lawwali, dan bama ta isa ba, d'an zagi da fadan ma da yake d'aga mata qafa ta na masa yanzu babu dama, ya toshe hanyar su, dan yanzu zai hargitsa musu lissafin gida, juyawa Mubaraka ta yi ta kalli Lamishi da ke kuka qasa qasa, ita da Mai Buruji, sannan ta tsaya ta ce,

"Yauwaa wane suna ma ki ke yawan kira na da shi ? GANTALALLIYA yar iska, da sauran su ko? To ina mai maki bushara da ni din nan, da kike kira da gantalalliya na godewa Allah da ya sa bani na dauki qafafu na na tafi gantali ba, daukata an kai aka kai ni wajen gantalin, me ki ke fata na aikata a wajen Gantali?...."

"Baraka, mu je"

Ba ta yi shiru ba, so take ta bawa Lamishi labarin abinda ya same ta a wajen, amma ba zai iya jure sauraran abinda aka mata ba, jikin shi har rawa yake saboda bacin rai, Lamishi kuwa kuka take bil haqqi, a rayuwar su kaff Mubaraka bata taɓa maidawa wani magana haka ba, me aka mata a can din? Me ya same ta, Lawwali ne ya daka mata tsawa a qoqarin ta na son sai ta qarasa labarin ta, jan hannun ta ya yi ta fuskance shi, su na hada idanu ta sanya kuka sosai, da qarfi ya rungume ta a jikin shi ya na numfashi sosai, dan kuwa shi ma kukan yake ji.

Maida Mubaraka gefe ya yi, ya kalli iyayen nashi ya ce,

"Wannan kukan munafurci  na ku kai wallah, ai murna za kuyi ku taka rawa, abinda kuke so, ya samu diyar ku, kullum fatan ki ta yi yawo ko? Ta yi gantali, ke kin san ma'anar Gantali kuwa? Ki ke hada d'iyar ki ta cikin ki da wannan mummunar kalma? Kin yi kuskure matuqa, ga gangali nan ki na gani, ko da shi ke ke rayuwar da muke ciki bata dame ki ba, ba a maganar mijin ku (subhallah mahaifin shi ya ke kira da mijin su) shi dai gashi nan ne d'ai, a dahwa a bashi ya ci shi kwanta da ku, ku haihwa, ya shiga gari ya yi hira da abukkai shi dawo, shi ci abinci, shi tai yawo, shin baka gajiya da aiki guda yau da gobe ba wani sabon abu da zaka qirqira da zai amfane ka da iyalin ka? Ko ni da nike wannan harka watarana gajiya nikai, to yanzu burin ku ya cika, kun haifi kalar diyan da kuka so, sai ku yi ta kuri a unguwa, mu tai, lokaci na tahiya"

Har sun kai soro ya koma ciki, a fusace ya debi dika kudin aljihun shi ya watsa musu, ya daki bokitin da ake dama kunu a gidan, ya ce,

"Gashi nan, ga abinda kun ka fifita sama da jini da tsokar ku,...ohh yi hankuri na hwashe muku bokiti, ku sai wani"

A tsaye a bakin mota ya tadda Mubaraka ta na rizgar kuka, al'ajabin iyaye kamar su Dan Talo take yi, wai wasu mutanen a duniya me suka dauki aure ne? Mai suka dauki samar da zuri'a ne, shin sun cancanta ma su zama iyaye?

Ba su bar wajen ba sai da Lawwali ya lallashe ta, ya bata baki sosai, da yi mata nuni da rayuwar da yake mata fata a gaban rayuwar ta.

Cikin gidan Dan Talo kuwa bayan tafiyar su Mubaraka, Lamishi d'aki ta shiga ta ci gaba da kuka, tare da danasanin abubuwan da ta dinga aikatawa, ba abinda ke mata gizo sama da kalaman Mubaraka na qarshe, shin me ya same ta?

Mai Buruji kuwa tattare kudaden ta yi tsaf, ta na gamawa Dan Talo ya je gaban ta, ya ce,

"Bakkani su nan (bani su nan)"

Wani kallon tara saura kwata ta masa, sannan ta ce,

"Me ya sa da ina tattarawa baka taya ni ba, sai da niqqare, zaka ce na baka? Tau ban basuwa, yaya zan bawa"

Cikin kad'a kai, da kyacci (qwafa)ya bar gidan, domin kuwa haske ya bayyana sosai, kowa na ganin kowa, gari ya washe.

A tasha kuwa Mubaraka kuka ta sanya ta na tirjewa akan ba zata bi su No 4 ba, tun Lawwali na lallashi har ta suqurar da shi ya hau fada,

"Gidan uban wa za ki zauna in baki bi su ba? Waje na? Rayuwar ki ta zauna cikin hatsari? Na rasa nutsuwa ta? Ko na kasa aiwatar da ayyuka na na yau da gobe, ko kuma wajen wadancan mutanen ki ke son komawa(iyayen su ya ke nufi).

Ita dai ta yi dif hawaye na zuba, ganin yanda take a tsorace ne ya sanya shi jan ta gefe ya daga kan ta, ya na share mata hawaye, sannan ya rungume ta, kukan ta ne ya qaru, ita dai da zai taimake ta, da ya barta a duk inda ya ke, bata son barin garin, musamman da No 4.

"Baraka na ki saurare ni da kyau ki ji, Taheer ba zai taba cin amana ta ba, na san inda zaku zauna, na san komai game da rayuwar shi, ba zai cutar da ke a kan sanin shi ba, ko wancan bai san ke za a dauka ba , sanda ya sani lokaci ya qure, na yarda da Taheer kamar yanda na yarda da kai na, dan Allah kar ki qi binai, hankali na zai hi kwanci in ki na can,ke ga shi na da iyali, ba shi d'ai na ba, ga mahaifiya tai, ga mata tai,ga diya nai, ba ke dai ta ba hwa"

Ita dai jin shi kawai take, ta hakura zata bi su,amma ba dan zuciyar ta na so ba.

Lawwali na tsaye ya na ganin yanda Mubaraka ke share hawaye, daga musu hannu ya yi sanda motar su ta tashi.
Chapter 46 · 0% Book details