Sashe 74
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke da kin ka taho nan, ki na surutun banza, da ba zuwa kin kai ki ka shirya kayan ki ba, ki ka sani ko shi bar ki can?"
"Kuma fa haka ne Yah Taheer, ina zuwa"
Miqewa ta yi cikin azama, da murna kamar qaramar yarinya, Taheer kuwa da sauri ya ce,
"Ki zauna can ba sai kin dawo nan ba"
Sultan da ya fuskanci inda Taheer ya dosa ne ya saki wata siririyar dariya, ya dauki wani dan qaramin kara ya saka a wuta, ya kafe kallon shi a cikin wutar.
Sai da Mubaraka ta bacewa ganin su sannan, Sultan ya ce,
"Ka dena bata ran ka aboki na, ita mace irin wannan allura ce cikin ruwa, sai ka ga mai rabo ya dauka, mu yi addu'a mu barwa Allah komi"
Taheer ya dan ji kunya da nauyin fadan da ya yi, sai kawai ya miqe ya bar wajen.
Tun da sultana ta leqa ta ga ana ta shara, ta ji gaban ta ya fadi, domin abinda take shirin aikatawa zai iya jawo mata mummunan hukunci wajen Lawwali, amma ta riga ta yi niyya, ba zata fasa ba.
Sauri ta yi ta koma d'akin, ta taya shi shirya wa, kaya masu kyau ta daukar masa, sannan ta d'aukar wa Mubaraka ma wasu kaya masu kyau daga nata dan ta saka, sun yi kyau sosai, Lawwali gaba d'aya ya sauya, nutsuwa kamala, da hankali sun samu wajen zama a jikin shi.
Su na kammalawa suka yi wa sultana sallama ya kama hannun Mubaraka, suka fita, mota suka shiga su na d'agawa juna hannu, Sultana kuwa yaqe take ta yi, tafin hannu da qafar ta sai zufar tashin hankali suke fitar wa.
Motar su na barin harabar wajen, sultana ta fad'a dakin su, ta tattaro, laptops wayoyi, da duk wani qundin ajiya, ta yi waje,direct d'aya daga drums din da ake kunna wuta a qona shara ta nufa, ta fara zuba su, d'aya bayan d'aya, ta na zuba disc na qarshe a wuta ta ji qarar motar Lawwali, wani irin tsoro da tashin hankali ne ya shigi sultana, sai da cikin ta ya murda, ta dafe marar ta, ta durqusa a wajen.
Ta na nan duqe Lawwali ya nufo ta, cike da tsananin bacin rai, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, hannun shi dunqule ya nufe ta, bakin ta ne ya fara rawa, hawaye na zuba, hannun ta dafe da marar ta, ta ke ja da baya, tana kad'a masa kai, leqawa ya yi, ya ga yanda abubuwan da ta sa ke ci da wuta, ga baqin hayaqi ya turnuqe wajen.
Cikin tsawa da hargowa ya nufe ta ya daga hannun shi zai kife ta da mari, ya ji an riqe hannun, ido suka had'a da Mubaraka, na zubar da hawaye, cikin tsoro, abinda bata taɓa ji ba game da yayan nata, dan ta san ba zai taba cutar da ita ba, amma yanayin shi a yau ya firgita ta.
Hannun shi ya sauke ya fara kaiwa da komawa, ya na shafa kan shi da hannun damar shi, cikin bacin rai ya kalli inda Sultana ke durqushe ta na kuka, Mubaraka na lallashin ta, ta na so ta d'aga ta tsaye.
"K..k...kayi hankuri....bb.ba zan iya bari ka aikata...abinda ka ke da niyya ba...ba domin kar mahaifi na ya shiga hannun hukuma ba,...ko kar a hukunta shi...ya cancanci dukkan hukunci...ba zan iya rayuwa ba kai ba...zan mutu a duk sanda na budi ido na ga babu kai....dan Allah kar ka yi abinda ka ke shirin aikatawa....na qona shaidun ne saboda a kowannen su ka na ciki,..."
"Yi min shiru ! Kar ki kara magana ! Kin ci amana ta Sultana, ba zan yahe miki ba,ke qona ne saboda ba ki son wancan azzalumin mahaifin na ku ya karbi hukunci a hannun hukuma ko? To ki sani, a yanzu in na je na bada shaida, na kawo jami'an tsaro nan, suka ga komi, hakan ya wadatar, mahaifin ki ba shi da wani qarfi a gwamnati a yanzu, har an dora wani a madadin shi, ba zai iya mulkar jama'a ba, da shayayyar qahwa, sultana me ya sa ki ka ci amana ta, bayan na yarda da ke, wadannan bayin Allah da muka zalunta shekara da shekaru ki na zaton sun yahe muna ne? Kin san yanda muka lalata rayuwar su ne? Har yanzu ina jin zahin lalata qaunata da aka yi, kamar mashi a qahon zuci, su fa? Ki na tunanin sun mance ne? Ko kuma ba su jin zahin abun? Sultana me yasa ki ka aikata haka? Me ya sa?"
Naushi ya kaiwa drum din da ke ci da wuta, ya fadi qasa, wutar ta yi taratsatsi, mutanen da suka taru a wajen yanzu duk sun fuskanci me Lawwali yake magana akai, zuciyar su ta karye matuqa da jin kalaman shi, ashe shi ya sa ya maida wasu ga iyayen su, kuma ya ke qoqarin ba wa wasu wanda suka rage a wajen ingantacciyar rayuwa, ashe ya na so ya miqa kan shi da duk mai hannu a kamen su ga hukuma? Lallai zuwan sultana cikin su alkhairi ne,domin ta sa Lawwali ya sauya daga Oga Makashin mutane zuwa Auwal mai tausayi da sanin ya kamata.
Mubaraka ce ta jingina Sultana jikin wata bishiya, sannan ta tsaya a gaban Lawwali, cikin zuciyar ta cike da tsoro, amma ta na qoqarin nemo jarumta irin tashi ta sanya a fuskar ta.
"Yah Auwal ba laifin Aunty Sultana ba ne, ni ta na bata shawara a qona, saboda na gan su, kuma na yi tunani in wani abu ya same ka wa nake da shi a duniya? Ka riga ka tuba ga Allah, ka kuma dau duk matakin da ya dace dan ganin ka gyara abinda ka bata, kana tunanin su hukumar da za ka kai kan ka wajen su, mutanen kirki ne? Ko ka na tunanin in aka binciko lehin da wasun su ke aikatawa za a bar su a raye ne suma? A yanzu yanda hukuma ta lalace mutane na gari ma da ke cikin ta ba su da qarfi,neman durqusar da su ake kullum, Yah Auwal kai wa Allah ka fahimci Aunty Sultana, ba ta da lehi, ba ta so ta fadi gaskiya ne ka ji haushi na, shi ya sa tai shiru"
Hawaye ne kawai ke zuba a idon Sultana,tare da jin qauna da soyayyar mubaraka na ratsa ta, tabbas wannan dalilin na cikin dalilan da ya sa Lawwali ke son ta, ta na da hankali da hangen nesa.
Lawwali bai ce komai ba ya bar su a tsaye a wajen,ya tafi dakin shi ya dauki wayar shi da ya manta, ya shiga cikin daji sosai, dan so yake ya yi nesa da su, ya na so ya kad'ita.
*Ohhhh Oga akwai son kai, dake Mubaraka ce ya yi shiru, amma da zai kai wa yar mutane duka😏*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 55:
Mubaraka da Sultana kuwa d'aki suka koma, bayan Mubaraka ta taimakawa Sultana ta zauna a bakin gado, Sultanan ta kalli Mubaraka ta ce,
"Mubaraka me yasa kin ka yi wa yayan ki qarya, bayan a kullum shi na yabon ki akan rashin yin qarya? Me ki ke tunani in ya gano baki da hannu a abinda ni na aikata ba ke ba? Gashi yanzu kin rusa muku tafiyar da ki ka jima da burin ki na son ya amince ku yi,"
"Babu komi aunty na,nasan ba zai iya kwana shi na hushi da ni ba, zai sakko ne, ni kuma ba zan iya jure ganin ki cikin halin baqin ciki ba, zai fahimce ki, bashi lokaci ya yi tunani, haka yake, ya na da saurin hushi, amma da ya fahimci gaskiya ya na saurin sauka"
"Allah ya sa ya sauka da wuri, ba zan iya jure fushin shi ba, amma me ya sa kuka dawo?"
"Waya tai yam-mance, shi na mun ka dawo dauka, ya shiga dakin yaga waccan locker a bude, shi ne na ga hankali nai ya tashi,ya na neman ki"
Murmushi Sultana ta yi, ta kalli Mubaraka ta ce,
"Na gode"
Su na nan zaune kamar marayu ya dawo, a rayuwar Lawwali ya tsani rashin cika alqawari da cin amana.
Ya san ya yi wa Mubaraka alqawarin kai ta gida,ga kuma Sultana ta ci amanar shi, dan haka dole ya dau mataki,
"Ki taho mu tai,...ke kuma na janye zuwan ku gida a gobe, har sai na gano gaskiya game da abinda kin ka yi min"
Murmushi mai quna ta yi, akwai zafi, wanda ka ke so, ka yarda da shi ya zama shi bai yarda da kai ba.
"Babu komi, Allah ya sa ka gane irin son da nake maka, ba zan yi komai dan na cuta maka ba"
Kallon cikin idanun ta ya yi, nan da nan na shi suka fara sanyi, da hanzarin shi ya bar dakin,tare da fadin
"ki taho mu tai"
motar shi ya shige, ya na zaune ya na jiran Mubaraka, qasan zuciyar shi na ayyano masa fuskar Sultana,mai cike da ban tausayi, da tsantsar soyayyar shi, ba ya so ya yarda da cewar amanar shi ta ke son ci, amma ya kasa dauke hankalin shi daga abinda ta yi din, anya ba da gaske saboda Daddyn su ta qona ba?
Mubaraka ma bata b'ata lokaci ba ta bishi , ta na shiga ya bar wajen da gudu, ta waya ya bada umarnin a shiga wajen Sultana a duba ta, a ga me ya sa ta ciwon ciki.
Sun isa gidan Dan Talo da misalin sha daya na rana, har a wannan lokacin mazaje masu zaman banza na zaune, a jikin katangar gidan,a jingine da gini, su na shan hantsi, ana ta zuba qarya,domin abun na su ya wuce hankali .
Hango mota mai kyau suka yi ta na tunkarar su, nan da nan kuwa a cikin su aka samu wani maqaryacin ya ce ai ya taba ganin me motar har sun ma gaisa rannan, wasu sun yarda wasu sun qaryata, tunda sun san junan su.