Sashe 5
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ga Isa da Dan banzan son yin kiss, ga baki na wari, Kuma Hansatu bata Isa ta nuna hakan ba, duk wani qoqarin ta na Sanya shi ya dinga wanke bakin,abun ya gagari tunanin baya ta fara, ta gwada aje masa hodar wanke baki da suke amfani da shi, ya yi fatali da ita, qarshe sai da yajibge ta, ya ce ta raina shi, shi zata kalla ta ce bakin shi na wari?
Ta gwada Yi masa magana direct, ya jibge ta, Kuma ya mata kiss ta qarfi, ya ce in mutuwa zatai sai dai ta mutu, Amma yanzu ya fara.
Gani ta Yi tunani ba zai kai ta ba, ya na iya fizgar ta da qarfi, da kan ta ta cire kayan ta ta kwanta a saman qaton gadon nasu, Wanda ya yi matuqar bani mamaki, ace kamar Hansatu masu ci da kyar ta na da irin wanna gadon.
Addu'a kawai take a ran ta har ya gama abinda zai ya tashi, fatan ta Allah ya raba ta da daukan wani cikin, ya Kuma bashi ikon dinga wanke bakin shi, tunda ta Yi dik wani qoqari ya qi farawa, Allah ne kawai zai sauya masa ra'ayi ya fara.
Cikin daren Isa na barci,jikin Hansatu ya dau zafi Mai tsanani, ga wani irin sanyi da take ji, bargon ta ta ja ta lullube jikin ta da kyau, Amma dik da haka sanyi take ji, Isa bai ma San tana Yi ba, Kuma in ta tashe shi ta San sauran, tunda naquda ma ya yi fada da ta tashe shi ballantana zazzabi.
Haka ta kwana da mummunan zazzabi, da zafin jikin ta ya dame shi ma sauka ya yi daga gadon, ya sa pillow a qasa ya kwanta, ya na ta surutai qasa qasa.
Hawayen baqin ciki ne suke kwaranya a idanun ta, har aka Kira asuba,ta na Nan kwance, takasa tashi.
Ba ta samu damar tashi ba kuwa sai da safiya ta fara Yi, da kyar ta iya hura wuta ta sa musu ruwan wanka, Amina da Bilkisu ne Suka shiga gidan Yabbuga duka samo ruwa, sai masifa ta ke masu, ta na fadin wata Rana ta ga alamar sai sun qafar mata da rijiya.
Ta na gama wanka ta Yi sallah, Isa ya fita tun tini, ya na can wajen Mai soya masa, ya ce a bashi ta dari biyu abin shi.
Kayan da ta daure jiya, ta kunce ta raba, ta Dora ma yaran ta ce,
"Maza ku kai wa mama Lamishi, ki ce mata Ina godiya,in ta na da ra'ayi ta na iya kawon wani wankin Nan gaba, ku Yi sauri kafin su fita, sun kusan tahiya gidan Gwauna , maza"
Da sauri kuwa Suka je, suka isar da saqon Mahaifiyar su, aiko wanki ya yi wa Lamishi kyau, ta ce zata kawo wani in ya taru,Mai Buruji ma ta ce za ta kai nata.
A hanyar su ta komawa ne Bilkisu ta ce,
"Amina mu je ta wajen Mai masa, na San baba na can,"
"Kin San dik ya kammana muna leqen shi Kashi zai liqa Muna ga banza ko?"
"Dun Allah mu tai, ni ko yawu na hadiya, mu dawo"
Da sauri ta kama hannun yayar ta da ke son guduwa gida, suka nufi rumfar me Masa.
Isa akwai jarabar wanke hannu, an zuba masa ya ja gefe shi kad'ai ya aje masar shi, ya tafi wanke hannu.
Bilkisu kuwa lallabawa ta Yi ta dauke kwanon Masa, ta ja hannun Amina Suka gudu gida.
Su na zuwa suka miqawa Maman su, Suka ce
"Gashi baba na yacce a kawo maki"
Cikin matsanancin jin dadi Hansatu ta amsa, ta sa yara a gaba Suka fara dukan waina da ci, su na ci ta na murmushin jin dadi.
A can rumfar me Masa, wasu matasa da Suka San isan da yaran shi,sun ga sanda Suka dauka, Dan haka dariya kawai Suka dinga Yi.
Isa na zuwa bega Masa ba, ya hau matasa da duka, ya na fadin sai sun biya shi masar shi, da kyar aka raba fadan, Nan suke sanar da Isa su ba su bane, diyoyin shi ne mata Suka dauke.
Wani irin ashar ya Danna, sannan ya Sanya takalmin shi guda da ya fadi wajen dambe ya nufi gida.........
A GARIN MU
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 6:
Da qafar shi ya daki qofar gidan, gaba dayan su zabura Suka Yi a tsorace, Hansatu ce ta Dan Yi murmushi da ta ga shi ne, godiya ta ke da niyyar Yi ta ji ya hada yatsun shi biyar da fuskar ta.
A kidime ta kalle shi, domin sanin laifin da ta aikata, Amina da Bilkisu ne suka shiga tsakanin su, ya ja hannun Amina ya kife ta da mari, zai qara mata Bilkisu ta riqe shi ta na kuka,
"Baba ka bar dukan su, ni ta nid-d'akko, ni zaka daka, Kuma ni nicce Kai ka bayar mu zo gida mu ci"
Wurga ta ya yi gefe, ta fadi ta dauje guiwar hannu, kuka ta Sanya Mai qarfi, tuni Hansatu ta durqusa ta na duba hannun nata, cikin sanyin murya da mamakin halin mijin nata ta ce
"Yanzu akan wainar jikka biyu ka fiddawa diyar ka jini? Ka daki matar ka ? Wadda ta sadaukar da millions saboda Kai, anya Isa Kai ne Wanda na fada son shi shekaru Sha uku da Suka wuce kuwa? Anya Isa Kai ne Wanda ka min alqawurran kyautatawa kala kala? Haqqin ka ne fa ciyar da mu, Amma ba ka Yi, da na san ba Kai ka Basu ba dakkowa suka Yi,da bamu cin ta wallah, ka Yi hankuri inshaa Allahu ba mu koma tambayar ka kuddin abinci, ko Kuma mu dau abun ka, tashi Mu je na wanke maki, sannu"
Kalaman ta Basu ratsa fatar shi ba ma, balle tsokar jikin shi, hasalima wata fassarar ya Yi ta daban.
"Auu abun gori Kuma ya koma Hansatu? To da ni da ke wa ya fara furta ya na son wani? Sannan wa ye ya kafe ya guji kowa na shi saboda masoyi? Kar ki dakko maganar baya akan haramun din da ki ka ci ke da yaran ki, duk Wanda ya sake min wannan gangacin zai ga ganganci"
Kamar ta sanar da shi ba su ci haram ba, sai ta kama bakin ta, saboda ta San dukan banza za ta sha, har ya shiga daki ba Wanda ya sake motsawa a cikin su, sai sautin shassheqar kuka kawai ke tashi.
Ya na shiga daki ya laluba ko Ina bai samu ko sisi ba, fitowa ya Yi sannan ya ce,
"Ba kuci banza ba, ki tabbata kin nemo min dari ta biyu"
Daga Kai ta yi ta na bin shi da wani irin kallon mamaki.
Tunanin baya ta fara Yi, shekara goma Sha uku da Suka wuce, shi din yaron mahaifin ta ne,mutumin kano ne shi, ita Kuma mutuniyar zamfara, ya na ma mahaifin ta tuqin mota, ta haka suka fara soyayya, mahaifin ta na da lalurar hawan jini, kafin ya rasu soyayyar su batai qarfi ba, Amma dik da haka ya fuskanta, Dan haka ya ce ya bawa Isa ita, Yan Uwan ta da dangin ta kaf aka dinga surutu, Dan me zai dauki gudan Yar shi mace tilo ya aura mata yaron shi, budar bakin ta ta ce wa Mahaifiyar ta da Yayan ta ta na son shi.
An saka ranar biki da ta gama candy, mahaifin ta a satin ya rasu, sun shiga damuwa sosai a zuri'ar baki daya, saboda shi din mutumin kirki ne, me son dangi ne da taimakon su, mutan unguwa da abokan aikin shi sun koka rashin shi, balle Kuma iyalan shi, Hansatu kuwa har ruwa sai da aka sanya mata a asibiti, saboda yawan suman da ta dinga Yi.
Bayan rasuwar mahaifin su da wata bakwai, Yan Uwan ta Suka yanke shawarar a raba gado, sannan a aura mata Dan abokin mahaifin ta, Wanda ke riqe da kampanin Baban su, Dan ya ci gaba da kula da ita, da dukiyar ta, Amma ta dage, ta nace ta ce sai Isa ,a lokacin nan Isa kan shi ji yake in aka raba su zai iya shiga mawuyacin hali.
Rashin lafiyar da ta dinga Yi bai bawa dangin ta tausayin komai ba, su dai qoqarin su su raba ta da Isa, har korar shi akai daga wajen aiki.
Wata Rana da daddare ta tattare kayan ta tsaf, ta gudu wajen shi, a dakin da ya kama, ta roqe shi da su je ko masallaci ne a Daura masu aure, in yaso sun koma a matsayin mata da miji, ba mai raba su.
A wannan daren haka suka kwana daki daya, rungume da junan su, dik da ba abinda suka aikata na masha'a amma hakan ba daidai bane.
Washegari suka samu aka aura masu junan su a masallaci ,a ranar suka koma dangin Hansatu a matsayin ma'aurata,mahaifiyar ta ta ji takaicin hakan matuqa, Yayan ta babba ya ce ba za su bata ko sisi ba, a gaban mahaifiyar ta, kuma bata sanya baki ba, Hansatu kuwa yarinta ce? Giyar soyayya ce? Ko kuma rashin tarbiyya ne ya sanya ta shigewa dakin ta dake gidan ,har sun fara murna ta ji maganar su, kawai sai suka ganta dauke da akwati, ta kama hannun Isa suka bar gidan.
Da kudin sarqoqin ta suka sayi gidan da suke ciki, aka sanya sunan Isa a takardar,gadon ta da komai na gidan duk da kudin da ta gudu da shi ne suka siya.
Lokacin da kudi suka qare ne, Isa ya fara fito wa da Hansatu asalin kalar shi, rashin mutuncin yau daban na gobe daban, da ciki ko ba ciki in ya ga damar dukan ta, zai daka, da ya ji kawai ta bata masa rai, zai mata abinda kamar bai taba furta mata kalmar so ba.
Wani irin kuka ne mai tsanani ya turniqe Hansatu, Bilkisu ce ta fada jikin ta ta na kuka, ta ce,
"Mama dan Allah ki dena kukan haka nan, lehi na na, bazan sake ba,ki yahe min,"