← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 93

Sashe 7

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murna a wajen Mubaraka ba a magana, sai dai can qasan ran ta, ta San ba kudin halal bane, har ta gaji da Yi ma Yayan nata nasiha, yanzu Addu'a ta koma Yi masa, ta na fatan watarana Allah ya amsa ya daina aikata dik wani abu Mara kyau.......

Shin ku na ganin wata Rana Lawwali zai daina halayyar shi kuwa?????

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 8:

Da yamma liss su Yabbuga suka Yi qungiya guda, zuwa gidan sabuwar maqociyar su Lamishi, Yabbuga ita ce a gaba, ita a dole ta San matar gidan.

Sun jima su na buga gidan, har Lamishi ta fara jin haushi ta ce su tafi, amma dake Yabbuga na tsananin son Shiga gidan sai ta ce,

"Ke wataqila kwana takai, ko ta zaga boli, mu jira kadan, ke dus-san ba ta hitowa lokaci guda daga bugun da be hi uku ba,"

Suna tsaka da jayayyar ko su koma ne matar gidan ta bude qofa, Yabbuga washe baki ta Yi, sannan ta kutsa Kai ciki, su Lamishi suka bi bayan ta, sai da Mai gidan ta fara zama sannan Suka zauna.

Gaisawa Suka Yi,Yabbuga ta gabatar da su baki dayan su, matar ta Yi murmushi sannan ta ce,

"Allah sarki ni ko suna na Asshibi, ai na so na shiga wajen ku, sai dai nicce Bari har na idasa gyara waje, har yanzu wajen bai kammalu ba, gashi kin rige ni zuwa, to na gode sosai"

Budar bakin Mai Buruji da ta kalli matar ta ga Yar babba ce, Dan ko za ta girme ta to da kadan ne, sai ta ce.

"Ina Yan yara,"

Cikin jin nauyi matar ta ce,

"Ba yara, ai ni din amarya Nike"

"Amaryaaa"

Suka fadi a tare, sai Kuma Suka yi shiru, abin Sha da Dan motsa baki ta je ta kawo musu, kan ta kawo har sun fara gulmar ta, ta na dawowa Suka Yi shiru.

Lamishi ce ta fara daukan cincin ta Kai bakin ta, Wasa Wasa sai da suka cinye komai suka shanye lemo tass sannan suka Yi hamdala, Suka mata sallama, sannan Suka fita.

Tun daga qofar gidan Suka hau gulmar ta,

"Kee ni na ga duniya, ke gane ta kuwa? Gudan gudan tulluqa, ga ta baqa qirin awar bayan tallen miya,Wai amarya take," Yabbuga ta fada cikin al'ajabi.

"Kee Yabbuga Ina kyautata zaton zaura ta, wallah"

"Lamishi baki da dama wallah, Wai zaura , yo baku gane min hoton mijin ta ba ga giina ta rataye, kyawu nai da gani ya hada dangi da hillani"

"Ohhh wanga Hadi nasu Kam shi ah-hadin Allah, in ba Allah ba wa'iisa yin wanga hadi"

Dariya Suka dinga Yi kamar wasu qananan yara, a qasan bishiyar su suka zauna Suka dora da hirar su.

Hansatu na jin sun fara hira ta San an kafa dandalin munafurcin kenan, tagumin ta ta gyara domin ba ta da lokacin ma saurarar su, tunani ta hau yi game da abinda za ta quqqulla ta dafa ko ta kwadanta masu su ci da daren.

Ta duba kaff gidan ba wani abu, sai wani tsakin masara da ya Yi qwari, tunani take ta Yi, akan yanda zata sarrafa shi kafin yaran su dawo, ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce,

"Mara shi ba ya hushi, dole ni tai nemo abinda nika ciyar da diya na"

Mayafi ta zara ta duba qafarta, takalmin ta da ke ihun gajiya da taka shi ta kalla, murmushi ta Yi, lokacin da ta tuna sai takalmin da ta so na qasashen turawa shi take sawa qafar, amma yanzu ita ke saka wannan takalmin da ko mai aikin gidan su ya fi qarfin shi.

Tun daga zaure sukai ido hudu da Yabbuga, cikin magana qasa qasa ta sanar da su Lamishi ga Hansatu Nan zuwa, shiru Suka Yi kamar ba su ke gulmar Yahai ba, kasancewar Ta Yahai din Bata samu zuwa dandalin gulmar ba, Yahai na gida ba lafiya.

"Assalamu alaikum, mun wuni lahiya? Ya yarori,"

A tare suka ce,

"Lahiya lumui, ya su Amina,"

"Lahiya lumui suke,....na ji ku na hira na nicce Bari in taho don Allah taimakon Nan dai da kun ka Saba, shi nika bid'a, 'Dan Mai nika so da d'an gishiri ku sammin in dahwa muna abinci kahin su dawo, da swahe ma Basu ci komi ba, Rana ma ta wuce ga dare ya Shiga,"

"Tauuuu, Isa bai gari halan? Irin wanga horon yunwa? Gaskiya bashi kyautawa, wanga zalumci ne wallah, ka bar diya har ukku da mace ba abinci, wanga zalumci na"

"Ke Lamishi Ina ruwan ki? Ba ita tagga tana iyawa ba? Duk wacce ta maishe da namiji uba ai ko ta na macewa marainiya, gashi Nan ta na dandanar azabar namiji, biyayyar da ta ka wa mijin ta, walle ni bani Yi ma nawa, gashi lahiya lau Nike da miji na, ci da Sha da, sutura kuwa wadda manya za su sawa haka nika sa ta,yanzu haka jiya yakkawon naman sanuwa, saboda bani son aiki nan nibbar mai abu nai, shi yayyi muna abinci mun ka ci dazu, komi ya aje muna, duk da qaramin ma'aikaci na, ai maza Zuma na, sai da wuta, wa ka ragawa namiji yanzu?"

"Keee Yabbugaaa raba kan ki da bawa matar mutane irin Wagga shawarar, tauuu, in ki na Bata abinda taka bid'a ki Bata, in baki Yi tau, Dan mu mun Yi nesa da gida"

Bata rai Yabbuga ta Yi, Dan ita ma kayan abincin sun Yi qasa, gashi ta gama yabon miji komai akwai, tashi ta Yi Rai ba dadi, tace wa Hansatu ta bita ciki.

Ko da suka je, wata tsohuwar jarkar manja ta Bata, in an narka be fi a samu dan kadan ba, ta debar Mata uban gishiri kamar auna shi tai Dan yawa, ta debar Mata barkonon da ba a daka ba, ta Bata Maggi biyu.

"Tauu ga su Nan, ki boye dai ba sai sun ga mi nibbaki ba su Yi ta tsintse, tunda ke San dai abin magana bashi musu kadan"

Durqusawa Hansatu ta Yi ta na ta godiya, saboda hakan ai babban taimako ne a wajen ta.

Zata fita ta ga zogale ya Yi fala fala,gwanin sha'awa, roqar shi ta yi, cikin bacin rai Yabbuga ta tsinkar mata kadan ta bata, tare suka fita, Hansatu na boye bubuwan da ta samo a mayafi, Yabbuga na qara kare wa har sai da ta shige gidan ta, sannan ta koma wajen zaman su.

Ta na zama ta dinga lissafin qarya na abinda ta bawa Hansatu, harda cewa ta bata busasshen kihi yara sun ji galmi galmi.

Nan dai sukai ta mata jinjina, ta na basarwa.

Tuno Asshibi ta yi, ta kece da dariya , sannan ta kalli Lamishi ta ce,

"Hummm walle dun-nittina matar can sai dariya ta kammin,( duk na tuna matar nan se dariya ta kama ni) kun ga shegiya baki awat-ta'adin yuqa? (Baki kamar ta'adin Wuqa)"

Dariya sosai su Lamishi suke ta yi.

Hansatu kuwa na can na sarrafa tsakin masara domin yaran ta.

Cikin ikon Allah kuwa sai ga faten tsaki ya samu, wanda za su ci su dan maida yunwar su, cikin murnar samuwar wannan abincin Hansatu ke komai,ta na hamdala ga Allah,ta na kammalawa ta zubawa kowa na shi,ta shiga wanka, ta so ci kafin su dawo,sai ta tuna su da suke yara ma suka hakura da yunwa balle ita?

Da misalin shida na yamma su Amina suka koma gida, murna a wajen Ahmad ba ta faduwa, tun da ya ga murhu ya ga toka,ga guntun icce jiqe ya san an yi dahuwa.

Cike da so da qauna, tare da kulawa ta zuba masu ruwa suka wanke hannayen su, sannan suka fara cin abincin, suna yabawa qoqarin ta.

Bayan sun gama sun sha ruwa, Hansatu ta fara koya masu karatun boko, Amina ta iya rubuta Hausa, turanci kuma ta na ji amma bata iya mayarwa dika, Hansatu ta ga tunda ita ta iya, yaran ta basu samu damar zuwa boko ba, mai zai hana ta koyawa yaran ta a gida?

Su na nan su na bacci Isa ya koma gida a zafafe kamar kullum ya shiga, bai amsa gaisuwar yaran ba balle ta uwar su.

Abincin shi ya jawo, ya zura hannu a aljihun shi ya zaro ledar kifi, dan dari biyu.

Ya juye ciki ya cinye.

Bai tambayi komai game da girkin ba, ya samu ne kawai,kuma ya ci,ya qoshi ya bar kwanon a wajen.

Ahmad ne ya je wajen shi, cikin tsoro, da kuma murnar nuna masa sabuwar kalmar da ya koya, ta Father, wato Baba,

Cikin Bata Rai Isa ya ce,

"Wato Hansatu kin rantse da Allah ke sai raina ya baci ko? Ban hana Maki koyawa yarana karatun nasara ba? Ni da na yi zuwa Sakandire uwar me ya tsinana min,in ba tuqin motar uban ki ba? Ke da ki ka yi zuwa Sakandire yanzu ta amfana da shi ne? Kawo littafin nan"

Amsa ya yi,ji kike kyyyaaaat ya yaga, yaro kuwa ya buga kuka.

Korar shi waje Isa ya yi, sannan ya zauna abinshi ya na hango su,suna jimami, dan sun ji komai,shi kuwa Isa kallon yaran ya yi ya kalli mahaifiyar su, wani irin shu'umin murmushi ya yi, sannan ya furta,

"Allah ya kaimu....."

Me ye a ran ka Isa????
A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 9:

Yau Lamishi ta tashi ba ta jin dadin jikin ta, zazzaɓi ya dame ta, dan haka da Mai Buruji za ta tafi aiki, sai ta ce Mubaraka ba inda zata sai dai ta raka Mai Buruji ta yi mata aikin ta.

Mubaraka bata so ba, domin har ta shirya, ta saka uniform, zata makaranta, duk magiyar da take akan a barta ta je makaranta, Lamishi ta qi, qarshe ma zagi ne da qoqarin kai mata duka ne ya biyo baya, bata da zabin da ya wuce ta bi Mai Buruji, a ranta ta na ta jin haushi rashin Auwal a gida.

Dan Talo ma tirsasa ta ya yi, ya ce sai ta je, wa ya sani ko ita ma a ɗauke ta aiki, hanyar samun su ta qaru.
Chapter 7 · 0% Book details