Sashe 38
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A zahiri kuwa kad'a kai kawai ta yi, ta maida qafafun ta cikin motar ya rufe, bayan ya zauna ya daidaita komai, ya kunna motar, d'aga kai ya yi, ya kalle ta ta madubi, shi kawai ta zubawa ido, kamar wanda zai gudu ta dena ganin shi.
"Ran ki shi dade Lawwali ne dai ba wani ba, in ki na min irin kallon ga za ki sa mu hwada rami,"
Kashe mata ido daya ya yi, tare da murmusawa ta gefen baki, Sultana ji ta yi kamar ta narke daga cikin jiki, da zuciyar ta,amma a zahiri dauke kai kawai ta yi ta maida gilashin ta sannan ta ce,
"In kai ma ka gama kallon nawa zamu iya tahiya yanzu"
Dariya ya yi sosai, sannan ya ja motar suka bar gidan.
Labulen dakin ta saki, tare da kallon Gwamna Halliru ta ce,
"Daddyn Sultan ka ga abinda nake ta hwada maka ka qi yarda ko? In baka d'auke yaron ga daga gidan nan ba, to ina mai tabbatar maka da sai an kawo maka shi a matsayin suruki watarana"
"Ke hwa in ki ka tsani mutum ruwa in ya taka sai ki ce ya tada qura, yanzu mi na na ki ka hwadi hakan ga? Ke San dai Sultana yarinya ce mai son mutane, halin ta ne kunya da fara'a, ko dan ki na nan huska awat-ta tamacen alade ba a gane dariya ko hushin ki, shi kenan yarinya ba zata yi hwara'a ba, a waje ma yi wa wasu takai ballantana yaron da ka tuqa ta"
Har cikin ran shi ya fi aminta da Lawwali Ya kusanci Sultana sama da kowa, amma shi ya rusa amincin da Lawwali ya bashi, da martabar da yake ganin shi da ita a ran shi.
Tsaki ya ja ya bar jikin windown da tun da lawwali ya budewa Sultana mota suke tsaye su na kallon su.
Hajiya Ikee ta qulu ta kai bango, alwashi ta ci a cikin ran ta, ba wanda ya isa ya hana ta korar Lawwali a gidan nan, dan kuwa bata haifar wa driver diya ba, Sultana matar manya ce, manyan ma na qololuwa,sabon shugaban qasa da suke saka ran ya ci zabe ta ke wa tanadin Sultana, Dan haka bata ga dalilin da zai sa driver ya shiga tsakanin burin ta ba, last week ta gama tallata sultana a wajen dan takarar shugaban qasar tasu, a lokacin da suka kai masa ziyara garin su, gaba daya ahalin, shi ne ake so a mata sagegeduwa, to ba zai yu ba.
************************
A wajen aiki ma, yau sun shaida sultana na cike da farin ciki, dan haka wajen ya zama a raye da farin ciki da nishadi, ba tare da sanin Sultana ba, Lawwali ya zari jiki, ya bar wajen, bai zame ko ina ba, sai maboyar da aka kai su Mubaraka, copy din makullin gidan da Taheer ya bashi ya dauka,duk wani abu da ya kamata ya sani Taheer ya sanar da shi, a daidai wannan lokacin su na can sansanin su, sai da rana d'aya daga cikin su ke zuwa a basu abinci.
Sai kuma da dare nan ma wanin su ko su duka za su kai masu abinci, da sassafe kuma No 4 aikin shi ne zuwa ya kai masu na safe, ya kuma tabbatar da ba abinda suke buqata.
A tsakiyar parlour ya tsaya ya na jiyo karatun qur'anin Mubaraka, zuciyar shi ta yi matuqar karyewa, musamman da ya ji ta na kuka dan bai san ma'anar abinda take karantawa ba, ballantana ya san ayar ce ta sanya ta kuka, saboda kwadayin rahamar Allah.
A tunanin shi kuka take saboda ta na cikin matsala.
Takawa ya yi cikin sanda,ya leqa ta bulin key din, zaune ya hango ta saman carpet din sallah, sai qawayen ta a saman gado, su na sauraran karatun ta.
Dan kuwa ba bacci suke ba, idanun su biyu.
Hannu ya sanya zai murda qofar,sai ya tuna bai karbi key din dakin ba, saboda ba ya so su san ya na zuwa duba su, har lokacin da ya daukar wa kan shi kubutar da su, ba dan an fi qarfin shi ba, sai dan shi ma ya na son ya rama abinda aka masa.
Yanda Lawwali ke jin kan shi, ba kusa bane, ji yake duk qasar nan ba mai iya karawa da shi, ya na jin ba abinda ya ke son yi wanda ba zai iya shi ba, sai dai in be so ba.
Cikin sanda ya bar gidan ,garin ya fita ya yar da gorar ruwa, wadda aka sha aka rage, ba a rufe bakin ba sosai .
Da sauri ya qarasa fita ya bar gidan, ya kulle, inda ya aje motar shi ya nufa, ya shiga, har zai tada ta, ya ga No 1 ya tunkari gidan daga can nesa, a motar shi, kallon agogo ya yi, ya ga ai yanzu ba lokacin ba su abinci bane, me ya kawo shi? Dube dube ya ga No 1 na yi, sannan ya bude gidan ya fada.
Lawwali ne ya bude qofar cikin tsananin fushi, ya sanya hannun shi a bayan rigar shi ya zaro 'yar qaramar bindigar shi, ya riqe, idon shi ya rufe, tsabar fushi da tashin hankalin da ya ke ciki, gidan ya nufa a fusace.......................
*Hummmm Ni kuma anan na ji naaaaa gaji zan huuuutaaa😅😉😝😝*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 31:
A guje Lawwali ya ke bin hanyar da za ta sada shi da gidan, kafin ya isa No 1 ya rufe qofar, har zai saka key ya bude wani tinani ya zo masa, cikin ran shi ya ke fadin.
'Haba Lawwali, ai bai kamata ka kashe wannan qaramin dan iska cikin sauqi ba, ka yi mishi kisan nan dai da ka yi niyya tun da can, ka bawa zuciyar ka hankuri, komai na da lokaci nai'
Da sauri ya bar wajen, ya nufi motar shi, dan ba ya son ya ga me No 1 ze aikata a gaba, gashi lokacin tashin Sultana na ta gabatowa, wataqila ma ya na isa time ya yi, a dayan bangaren ma ba zai so rusa plan din shi ba na wajen Sultanan, dole ya na ji ya na gani ya hakura.
Ya na tafe ya na sauke wani irin numfashi,kamar wani mayunwacin zaki, duk wanda ya san wane ne asalin Lawwali, a wannan lokacin is not a good idea ka bata masa rai, dan yanzu zai ma lahira sabon baqo da mutum.
Gudun da yake zubawa har ya wuce misali, wataqila da a qasashen turawa ne da tuni an tsaida shi .
Birkin da ya ci ne ya janyo hankalin mutanen da ke wajen, cikin su har da sultana, da ke saka hannu a wata takardar da za a fitar da buhunan shinkafa domin mabuqata.
Ta na kallon idon shi ta ji wani irin yanayi da bata taba ji ba game da Lawwali, wato tsoro,sai dai ta bangaren Lawwali, su na hada ido sai ya ji bacin rai da baqin cikin shi ya ɗan ragu, har murmushi ya ɗan yi mata.
Ganin murmushin shi ne ya sanya ta sakin nata, ta kawar da tsoron da ke ran ta, amma tabbas fuskar da Lawwali ya sanya a baya, bata fatan sake ganin irin ta har gaban abada.
Kafin ta zo ya bude mata qofar,ta na shiga ya mayar ya rufe da qarfi,sai da ta ɗan razana, shi din ma da qarfi ya shiga ,ya kuma rufe da qarfin, cikin sauri ya tada motar dan ya na buqatar leqa sansanin su, ya ɗan huce haushin shin shi a can.
Ba tare da ta yi wani tunani ba ta miqa hannun ta zuwa kafadar shi, a hankali ta shafa saman rigar tashi kafin ta matsa kafadar tashi sannu a hankali, wata iriyar ajiyar zuciya lawwali ya sauke mai qarfin gaske, tare da gangarawa gefen hanyar ya tsaida motar, kifa kan shi ya yi a jikin sitiyarin motar, ya na sauke numfashi, quncin da ke cikin zuciyar shi ba shi da misali, ya na ji ya na gani qanwar shi take a wulaqance, kafin ya gano ta ya zaci ba tashin hankalin da ya fi rasa ta da ya yi, amma yanzu ji yake wannan tashin hankalin ya fi na rasa ta da ya yi, shi ba qarfin shi aka fi ba, ba komai ba, amma ya ke azabtuwa.
Bai san sanda ta zauna a gefen shi ba, sai jin hannun ta ya yi a saman qeyar shi ta na shafawa a hankali, idanun ta na zubar da hawayen tausayin masoyin nata, ta san duk damuwar shi ba ta wuce ta rashin Mubaraka ba.
A hankali ya daga kai suka kalli juna, gaban ta ne ya yi wani mummunan faduwa, Lawwali kamar ba shi ba, fuskar shi ta yi jawur, idanun shi ma haka, ga wani dagawa da komawa da qirjin shi ke yi, cikin sauri ta zame hannun ta, ta sunkuyar da kan ta qasa, ba za ta iya jurar kallon shi ba.
Muryar shi na rawa, ya ce,
"Sultana....qauna ta a duk inda take ta na buqata ta, ina ji a jiki na, ta na cikin matsala,"
Tsigar jikin ta gaba daya ta miqe, sakamakon kiran sunan ta da ya yi, bata taɓa zaton bayan iyayen ta da suka saka mata suna sultana ba, akwai wanda ya iya fadin sunan ya yi daɗin saurara kamar Lawwali ba, ga wani matsanancin tausayin shi da ke addabar zuciyar ta, cike da raunin murya ta ce,
"Allah na tare da ita ko ba ka nan, zai kula da lamarin ta, baka cutar da d'an kowa ba, kai ma ba za a cutar da taka qaunar ba"
Da sauri ya kalle ta, sannan ya ce,
"In kuma na cutar da wani fa? Sai a cutar da tawa qaunar ki ka nuhi?"
Yanayin yanda ya yi maganar ya sa ta jin kalaman ta ba su yi dadin saurara ba a kunnuwan shi, cikin sauri ta ce,
"Nooo ba haka ni ka nuhi ba, mu je gida mu sake wa Daddy magana, Ni kai na na damu da rashin Mubaraka,"