← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 93

Sashe 6

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan shafa bayan yarinyar kawai ta yi, ta ya za ta budi baki ta sanar da yaran ta me ta aikata? Sakayya ce ta qin yin biyayya ga mahaifiyar ta ke bin ta? Shin a wani bangaren ba umarnin mahaifin ta ta cika ba? Tunda dama ya so a yi auren? Ta ya zata sanar da yaran ta mahaifin su azzalumi ne? Shin wadannan abubuwan da suke faruwa da ita silar waye?

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 7:

Lawwali ne da yaran shi zaune a wani tsohon kamfani na gwamnati,waje ne da ya qunshi sashe sashe, da dikkan alamu ofishin ma'aikatan wajenne, Lawwali kuwa ya maida wajen a matsayin ma'aikatar shi ta yin garkuwa da dik Wanda aka bashi umarni, ko Kuma ra'ayin kan shi ya bashi da ya Yi hakan,waje ne da ya ke a cikin wani surquqin daji, da dikkan alamu gina shi aka fara yi domin wani aikin na gwamnati kuma aka bari ba tare da an kammala ba, ko an waiwaye shi, Lawwali da yaran shi na ta qoqarin Neman network dan yin waya amma sun rasa.

Ya fi awa uku ya na abu d'aya, cikin nasara kuwa ya samu wayar da ya ke son Yi ta shiga, da hanzari ya fara magana.

"Hello Excellency  ba waku, yunwa ta addabe ni da yara na, ga shi ba ruwan sha, mu na buqatar kayan caji,...hello...hello"

Wayar ce ta sake katsewa, cikin fushi ya buga ta da qasa, ya daki jikin ginin wajen, wani dattijo ne daure a jikin ginshiqin da ke a tsakiyar faffadan wajen da suke, bakin shi ya bushe, da alama yunwa da qishirwa suna damun shi, idanun shi a rufe suke, ba ya ganin kowa, amma ya na sauraren su.

Cikin wahalalliyar murya ya ke magana,

"Yanzu Lawwali duk irin amanar ka da na dauka, na riqe, haka zaka saka min da shi? Ba irin taimakon da ban maka ba a rayuwa, amma saboda wancan dan adawar ya biya ku kudi qalilan kuke wulaqanta ni haka"

Cikin fushi Lawwali ya kalli mutumin da ya haife shi, ya shure shi da qafa, sannan ya naushe shi sau ba adadi, har sai da wani daga yaran shi ya riqe shi.

"Oga ka Yi hakuri,Kar ya mutu, in ya mutu Excellency ba ze Mana da kyau ba, ajiya kawai ya ce muyi, ba kisa ba, ya jaddada Mana hakan, sai bayan zabe mu sake shi"

Bangaje yaron nashi ya Yi ya duqa gaban bawan Allah n da ya gama duka, cikin qunci yake magana.

"Ka riqe ni amana? Wace iriyar amana ka riqe? Amanar shaye-shaye? Ko ta Neman mata da kisan kan mutane? Ko kuma amanar fyade da garkuwa da mutane Dan neman kudin fansa? Kai Bari ka ji, ka ga da ace Excellency ze sauka, Wanda ya sake Hawa ya ban irin wannan umarnin, shi ma qaddamar Masa zan, taimako d'aya ka min a duniya, shi ne Iyaye na Dake aiki a gidan gwamnati har yanzu, dik da ka sauka su na Nan suna ci gaba da Yi, da wannan aikin gidan mu suke ci su qoshi, su Yi sutura, Dan haka iyakar godiyar da zan maka kenan, in ma zan Yi maka godiya"

"Oga Lawwali ya suma fa,gashi ba ruwan yayyafa Masa"

Murmushin mugunta Lawwali ya Yi, babu bata lokaci ya kunce wandon shi ya fara tsiyaya ma wannan mutumin fitsari akai, sai kuwa gashi ya farfado.

Kula da abinda Lawwali ke Yi ne ya Sanya wannan bawan Allahn qoqarin kaucewa, Amma dake ya na a daddaure ne, sai ya kasa matsawa.

Dariya Lawwali da yaran shi Suka dinga Yi.

Har magariba ba wani bayani daga wajen gwamna, yunwa dik ta cinye su da qishirwa, ga wayoyi sun mace ba caji, sai torch lights suka kukkuna, su na Nan zaune, har isha'i ta Yi, Lawwali ne ya tada mutane uku ya ce su dau mota su shiga gari,su sama masu abinda za su ci,Dan ya na ta jiyo kukan yaran da ke killace a wasu sashen da ke gidan da ko rufin kwano babu a wasu sashen, ya kuwa tabbata yunwa ke damun su,kudi ya Basu akan su siyo Dan wani abu ko ba yawa a fara da shi, Kuma su tabbata sun samu ganin Gwamna a daren ko Kuma su Yi magana da shi ta waya, a Kai masu abinci da ruwa.

Har za su tafi Lawwali ya dakatar da su,

"Yauwa ga waya ta ku tafi da ita, a sama min caji"

"To Oga,"

Mota suka tada Suka dauki hanyar shiga gari.

Sun samu sabani da mutanen gwamna, Dan kuwa Basu jima da tafiya ba aka kawo qatuwar mota lode da abinci da dik abinda suke buqata.

Ba bata lokaci yaran Lawwali da za su Kai su goma suka dirar wa abincin suka dinga shigar wa wani daki ana lodewa, bayan sun kammala shigar da duk wani abu da ya kamata suka zauna cin biscuits da juice dan kawar da yunwa kafin matan da ke cikin wajen su dafa abincin, drivern da ya kawo saqon ne ya tsaya ya na bawa Lawwali saqon gwamna.

"Oga Lawwali gwauna ya ce na hwada maka, kudin fansa da za a ce dangin Lamido su bayar ace su basuwa  milliyon dari biyar, kar a rage masu ko sisi, dan ya San ya saci ya hi haka nan, da zarar sun kawo kun amshe ku qarasa shi, ya gama Yi wa qasa banna"

Daga Kai kawai Lawwali ya Yi cikin Isa, da nuna shi ne oga a wajen,dik qoqarin cin binci da kowa ya ke, shi bai  je ba ya na gefe, ya na son ya ga kowa ya qoshi har da yara da matan da suka kwamushe, Dan haka yaron shi Mai kula da wajen in baya Nan ya aika, ya kwaso Mata uku su raba abinci, haka kuwa aka Yi, kowa ya ci ya qoshi, daga qarshe Lawwali shi ma ya samu ya ci a nitse.

A wajen ba a Kiran kowa da sunan shi saboda tsaro, Lawwali Oga suke ce Masa direct, daga Mai bi Masa zuwa mutum.biyar da ke qarqashin shi, da Number ake Kiran su.

No 1 shi ne Mai bi ma Lawwali, sai No 2 Mai bi Masa, haka haka, har No 5.

A cikin mutanen da aka kwamushe akwai wadan da iyayen su ko 'yan Uwan su sun zaci sun rasu, domin an amshi kudin fansar su, Kuma an qi maida su gida, sun fi shekara a wajen, sun Saba ma da wajen, wasu Kuma har yanzu ba su Saba ba, Neman duk wata hanya da zata fidda su ta maida su wajen ahalin su suke, musamman manya masu hankali.

Wasu Kuma sabbin zuwa ne, bangaren sabbi daban na tsoffin zuwa ma daban, wasu daga yaran Lawwali sun Yi 'yan Mata a wajen, su na dik wani abu da suka so da su, cikin sauqi, ba tare da sun takura su ba, Lawwali ya San da hakan, Kuma bai Hana ba.

Wajen ya zama kamar prison ga wasu, wasu Kuma kamar unguwa suka je, su na saka ran komawa gida watarana, wasu Kuma kamar gida Suka dauki wajen, kowa da yanda yake ganin wajen.

In ba an samu akasi kamar na yau ba, a wadace suke Koda yaushe da abinci, ruwa da dik abinda suke buqata, wutar lantarki ce kawai babu a wajen.

**********************

Watarana Mubaraka ta dawo daga makaranta, ta gama cire Kaya ta Yi wanka, ta shirya, ta dau abincin ta, ta fara ci, Lawwali  ya shiga kamar kullum ba sallama.

Sanye yake da qananan Kaya kamar ko da yaushe, sun Yi matuqar Masa kyau, zama ya Yi a kusa da ita, suna ma juna murmushi, hannu ya sa ya amshi spoon din ta, ya Yi Loma daya, sannan ya Bata a baki.

"Yah Auwal ni fa ba yarinya bace"

"A waje na ke jaririya ce har yanzu"

Murmushi suka Yi a tare, ledar da ya shiga da ita ya janyo, ya dudduba, wata Yar madaidaiciya ya dakko, ya bude masu, sannan ya ja kujera qarama ya zauna da kyau.

Nama ne gasasshe a ciki, zuba masu ya yi. Saman abincin ya ce su ci,

"Na Yi kewar cin abinci da Kai Yayana"

"Nima haka qanwa ta"

"Amma za mu ragewa su Umma ko?"

"Ga nasu can, wannan namu ne, Ina sane na zo yanzu, na San kin dawo, ko Zaki ci abinci, ko ki na wanka, "

"Sai Kuma gani Ina ma cin abincin, da na qoshi ka kawo da na Yi fushi"

"Ai Ina aiki da lokaci, na san ma baki ci ba"

Sama akai da kwanon, ana masifa.

"Lawwali zaka ci uban ka Wallah ita d'ai ta a gidan da ka bata nama hakan ga Mai yawa?"

Cikin Bata rai Lawwali ya ja ledar gefen shi ya cire wata Leda ya miqawa Lamishi,

"Aje Mana abincin mu, ga naku Nan, Dan mugun kwadai ya maki yawa Lamishi wanga nama da bai da yawa shi na ki ka wa baqin ciki mu ci, Wanda kuka ci gidan Gwauna in an hada da wanga ko rabi be ba,"

"Uban ka ke bamu nama a gidan Gwauna?"

"Lamishi na fada maki ki dena zagi na ko,"

"Mi zaka min Dan uban ka? Waje ka ke Zaki, gida mussa ka ke wallah"

Dariya Mubaraka ta Yi, Dan ita dariya suke Bata, cikin dariya ta ce

"Yah Auwal tsaya biyewa Umma na canye"

Da dariya Shima ya Debi biyu a tare ya sa a bakin shi, Lamishi da ta ga ta na ta masifa Basu kula ta ba, sai kawai ta tafi, ta na tafe ta na laluba ledar, ta na diban naman ta na watsawa a baki, kafin ta raba masu ta ci da yawa.

Bayan Lawwali ya gama cin abinci da Mubaraka, sai ya Kira ta dakin shi, ta zauna bakin gadon shi, Mai kyau kamar na wata amaryar.

Waya ya zaro ya miqa Mata.

"Ga taki, kin huta da aron ta Lamishi ana zagin ki, za ki iya Kira na duk sanda kk so, zan dinga saka maki Kati akai akai"
Chapter 6 · 0% Book details