← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 93

Sashe 36

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kyabe baki 'Yabbuga ta yi ta zauna, lokacin azahar ya yi, madadin su bari su fara sallah, sai suka yi kamar basu ji ma kiran sallah da ake ba,kwaba lallen Lamishi ta yi, Yabbuga na ta uban surutu, rabin surutun zagin Mai Buruji ne, dan ma Lamishi na taka mata burki, ta kan ce, ta tsani me zagin kishiyar ta, domin watarana zai zage ta ita ma.

"Ni hwa ban ga lallen ga na kamu ba" inji Lamishi, Yabbuga tace,

"Ke dai bari shi yi awa guda ki na ganin yanda zai yi kyawu kwarai"

Su na tsaka da saka lalle Mai Buruji ta dawo daga aiki, ga lalle an qunshe wa 'Yabbuga hannu da qafa da shi, ko da Mai Buruji ta dakko kwanukan cin abinci yawu ya fara ambaliya a bakin 'yabbuga, ta ji haushi saka lallan nan a hannu, da ta sani da a qafa kawai aka saka mata.

Ko da aka raba aka zo cin abinci sau biyu Mai Buruji ta bawa 'yabbuga a baki, suka yi ta cin abin su suna hira, Lamishi ta ce Allah shi kiyashe ta bawa qatuwa abinci a baki.

Ran 'Yabbuga in ya yi dubu ya ɓaci, ta kame bakin nan ta gume shi gum, a haka gyangyadi ya dinga dibar ta.

************************

Shigar su gidan Lawwali ke da wuya, ya qirga kudi dubu dari biyar ya bawa No 4, No 4 kuwa cikin dakiya, da danne abinda ke ran shi,ya dinga murnar dole ya amsa ya na godiya.

Lawwali na ta kallon shi, kallon da Lawwali ke masa ne ya fara shiga kowanne lungu da saqo na jikin shi,cikin hanzari ya fara qoqarin tafiya, Lawwali kuwa zama ya yi a daya daga kujerun da suka zagaye madaidaicin parlourn , ya dora qafar shi daya saman daya,No 4 na kallon zaman da Lawwali ya yi, ya tabbatar ba lafiya, cikin sarqewar murya ya ce,

"Oga na tafi..se..se..see da swahe,"

Hannu kawai Lawwali ya daga masa, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, qafafun No 4 na rawa ya nufi bakin qofar, ko da ya murda ya ji ta a rufe, juyawa ya yi ya ga Lawwali na kallon yatsun hannun shi, sake jan qofar ya yi, ya ji ta gam, cikin tsananin tashin hankali ya juya tare da zubewa a wajen,ya sake jakar kud'in a qasa ya na kuka, zufa da hawayen shi duk sun hade waje daya.

"Oga don Allah ka yi min rai, ka rufa min asiri ina da iyali, ka sani, ka san mahaifiya ta, ka ɗauke ta awat-taka,Oga ina da niyyar sanar da kai tsoro nika ji kar ka kashe ni, ina da qananan yara ka sani, har takwara na yi ma oga"

Har gaban Lawwali ya isa ya kama qafar shi ya na kuka ya na bashi hakuri, wani irin naushi Lawwali ya kai mishi sai da jini ya yi tsartuwa a qasa, bakin No 4 ya fashe.

Kasa ihun ma ya yi, dan ya san ya cancanci sama da haka ma, idanun Lawwali ba bu mai fatan ya gan su a wannan lokacin.

"Taheer ni zaka ci wa amana? aza ka ke bani ganewa? To na ji duk abinda kun ka ce kai da wancan qaramin dan iskan, ina kun ka kai min qauna ta?"

"Oga na san inda suke zan kai ka da kai na, Oga ka yahe min, ba da son rai na ba an ka ɗauke ta, ba ita mun ka tai dauka ba, qawar ta mun ka tai dauka, sun ruhe fuska bamu san da ita ciki ba"

"Yi min shuuu ! Munahikin banza, ka na jin har akwai wata sauran yarda a tsakanin mu? Ba bu yarda tsakani na da kai, maza ka gaggauta kai ni ga qauna ta, sai dai zai zama siri tsakanin mu, kamar yanda gwauna da wancan shegen basu son na sani, ban yarda ka sanar da kowa ba,in kuma ka sake cin amana ta a karo na biyu, zan kashe ka, zan kashe uwar ka, dan ba uwa ta ta ba, zan kashe matar ka da diyan ka,"

"Oga ko na hwarko ma tsautsayi na wallah ban koma cin amanar ka, Nagode  oga na go..."

"Dalla miqe ka je ka kai ni ga qauna ta"

Jiki na rawa No 4 ya miqe, a bakin kofa ya tsaya ya na jiran Lawwali ya bude qofar shi, sai da ya dauki makullin mota, ya lodawa bindigar shi harsashi sannan suka fita suka bar gidan.

Kafin su isa magriba ta gabata sosai, bai fi awa daya a kira ba, su na zuwa No 4 ya bawa Lawwali shawara su aje mota a nesa su qarasa da qafa, haka kuwa aka yi, sun isa qofar gidan, suka tarar an kulle da kwado, No 4 ne ya zari makulli a aljihun shi zai bude qofar, bai ankara ba ya ji an dafe qeyar shi da duka,

"Dan iska, makullin ruhe qauna ta na hannun ka, amma kullum muke haduwa baka taba hwadi min ba"

Su na shiga su ka ji gidan shiru kamar ba kowa, dakin da aka ajiye yaran suka shiga, ko da suka je sai ba su ga Mubaraka ba, sai su Murjanatu, tambayar su Lawwali ya yi ina take, cikin kuka Saliha ta ce,

"Wannan d'ayan mugun ya dauke ta, kullum in ya zo sai ya dauke ta ya hita da ita, daga baya sai ya dawo da ita, ta na kuka"

Wani irin ashar Lawwali ya saki,lallai in abinda yake zargi No 1 ya yi da Barakan shi,tabbas a yau dinnan zai kashe shi.

A guje Lawwali ya kama hanya zai fita daga gidan, No 4 ya yi maza ya kulle ko ina ya bi bayan shi da mugun gudu,shan gaban shi ya yi ya na haki, wani naushi Lawwali ya kai mishi a ciki, sai da ya duqa

"Oga ka san mutanen ga basu da dad'i, na sani Gwauna da kai ya ke taqama a duniyar siyasa,amma ba a cin munahuki da yaqin gaba da gaba, shi ma ka hito mai ta inda bai zata ba, babbar nasarar da an ka samu shi na ka san wanda ya dau qanwar ka,"

Tabbas maganar No4 gaskiya ce, to ta yaya zai rama abinda gwamna ya masa?

Kan shi cike da tunani ya shige mota, ya bar No4 a wajen, No4 komawa ya yi, ya gargad'i su Murjanatu, akan kar su kuskura su sanar da zuwan su, da yayan Mubaraka, su na sanar wa za a kashe su nan take.

Tsoro ya kama su, dan haka sun yi alqawarin ba za su fad'a wa kowa ba, har ita kan ta mubaraka din.

************************

'Yabbuga bata farka daga baccin da ya kwashe ta ba sai da ta ji qarar bude qofar gidan da qarfi, a kidime ta farka ta na fadin,

"Wayyoo Allah mun shiga uku, mi ya hwaru, ake bude gambu kamar ana girgizar qasa?"

"Me ki ke yi a gidan nan a wanan lokacin,"

Bude baki 'yabbuga ta yi iya qarfin ta takurma ihu, marin kan ta tayi, wai ko za ta tashi, wataqila a baccin wahalar da ya dauke ta ne ta ke ganin shi a idanun ta.

Qafa ya sa ya kwashe kujerar da ta dora qafafun ta ya yi wurgi da kujerar, kafin ya qara kaiwa d'aya kujerar duka 'yabbuga ta miqe, ta taka qafafun ta biyu a qasa, ta diba waje a guje, tsantsin ledar na diban ta, kai ba ko dan kwali, gashi duk ya tuttuje haka ta isa gida.

Dan jumma na ta gyara ma'ajiyar abincin su da awaki suka shiga suka yi wa barna, gani ya yi ta afka gidan ba ko sallama, zani qanqame a hannun ta, kai ba dankwali, duk Leda a qafar ta, tsoro da tashin hankali ne suka rufe Dan Jumma, dan a tunanin shi ko masu kidnapping ne suka dauke ta ta gudo, tunda yanzu abun qara yawa yake.

"Daga ina ki ke? Wa ya biyo ki? Masu kidnapping na halan?"

"Wanga ya ci uwar masu kilnapim, ni da gidan Dan Talo har abada,tunda ba aljanna aka rabo a gidan ba,"

Wani irin tsaki Dan jumma ya saki, sannan ya kalle ta ya ce,

"Dama can ki ka tahi na shigo na tadda bisashe (awaki) sun canye min kayan abinci? Ni da na gan ki a hirgice ma aza nikai ko sace ki an kai ki ka gudo, tunda na san ki da gudun ceton rai"

Kar kacewa ta yi rai bace ta ce,

"To mi ka ka nuhi? Wanga ba gudun ceton rai na ba halan, ka ga wadda Yaron nan ya shigo? Ka ga wadda ya dinga fatali da kujeru? Da na tsaya mi ka ka tunanin ze min? Dan Jumma na kula baka san hatsarin yaron can ba ne, Allah shi gama ku watarana"

Cikin sauri Dan Jumma ya ce,

"Ba Amin ba 'yanneman me mugun hwata,"

Haka sukai ta kace nace a tsakanin su, har ya gaji da hayaniya da ita ya bar gidan.

Can gidan su Dan Talo kuwa Lawwali na can na musu ta'adin da ya saba, daki guda su Mai Buruji suka shige, su na ta bashi hakuri, amma bai kula su ba, sai da ya gama musu ta'adin da ya so, sannan ya shiga dakin Mubaraka ya kwanta a katifar ta, hawaye ne ke bin gefen fuskar shi masu dumin gaske, da a so samun shi ne yanzu ya samu ya ɗan hahharbe ko da mutum biyar ne, amma dole zai yi hakuri ya bi shawarar Taheer, zai dauki fansa ta inda gwamna bai zata ba.

Ya na nan kwance har daya na dare, can dakin kuwa sun san bai fita ba, dan basu ji motsin shi ba, ga fitsari ya matsi Lamishi, Mai buruji ce ta ce,

"Yaya kar ki yi min boli (fitsari) ga daki, ke hwa uwar shi ta, ki tai ki bolin ki ki dawo,ko ki tai dakin ki"

Wani mugun kallo Lamishi ta sakarwa Mai Buruji, bata ce komai ba, se kwafa da ta yi, tare da sake leqawa, cikin ran ta ta na fadin,

'Ya jima da yin niyyar ajali na, ina hita a wannan halin da yake ciki, sai ya cika alqwani nai wallah'
Chapter 36 · 0% Book details