← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 93

Sashe 78

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya kam ranar Hansatu ta yi ta har da hawaye, daga qarshe ta zari dubu daya ta bawa 'Yabbuga ta ce ta sai madara, dan kuwa bata ga ta inda abinci ze shiga bakin nan ba, ba tare da an ci azaba ba, Godiya ta dinga yi kuwa, ta na so ta yi murmushi ba hali.

Hansatu bakin titi ta je, ta sai musu kayan miya da naman miya, ta koma gida, dan d'ora girki, kafin yara su koma gida.

************************

Sultana na zaune a bakin qofar dakin su, ita da Sultan su na hira, ta sanar da shi abinda Lawwali ya ce, na hana su zuwa ganin Daddyn su, bai b'ata rai ba, bai kuma nuna damuwa ba, ya ce kar ta damu, duk sanda ya bar su za su je ne, hira suke sosai akan abubuwan da suka faru a baya, suka ga motar Lawwali ta nufi wajen da suke aje motoci, gaba dayan su hankalin su ya tattara ya koma kan masu fitowa daga motar, Sultan na ta kallon mubaraka, sultana kuwa idon ta na kan gwarzon mijin nata.

Lawwali na ta wani had'e fuska, shi a dole kar Sultana ta ce ya sakko daga fushin da yake da ita, gaisawa suka yi sama sama da Sultan ya shige daki, Mubaraka na qunshe dariya, cike da murmishi ta miqa wa Sultana ledar ta na kallon idanun ta, dan ganin kalar murnar da za ta yi, in ta ga me ke ciki, Sultan kuwa ita ya ke kallo, ya na murmusawa, yana yin ta ba qaramin tafiya da shi ya yi ba.

Taheer ne tafe zuwa wajen su Mubarakan, dan tunda ya ji dawowar su ya tsaya ya ɗan gaggyara shi ma a gan shi fess, tun daga nesa ya hango irin kallon da Sultan ke yi ma Mubaraka, kwafa ya yi, a ran shi ya ce,

'kaii wanga ba dan yanzu mun aje harka ba, ai da tuni na sheqe shege, ji wani kallo awa baqin maye'

Sake kwafa ya yi, sannan ya d'aga qafa dan zuwa wajen nasu.

"Mubaraka wannan fa?"

Dan duqawa Mubarakan ta yi saitin kunnen Sultana, ta mata rad'a, ita kuwa wani irin annuri ke fita daga fuskar ta, ta na fitar da siririyar dariya,mai dad'in sauti,

"Mi na na kuke fadi ba a so na ji? Mubaraka ba kyau fa abinda kin ka yi yanzu, mu na tare ki ware ta ku yi magana a gabana ban ji ba"

Dariya ta yi, sannan tai qasa da murya ta ce,

"Ba na so yaya ya ji mi na ce, matso ka jiya"

Matsawa ya yi, sannan ta  kai bakin ta  kunnen shi za ta masa rad'a Taheer ya katse su da fadin,

"Mi na na haka? Ke Mubaraka me ke nan?"

Ba tare da ta kula da yanda ya b'ata rai ba, ta ce,

"Wata magana zan fada masa, bana so yaya ya ji"

"To muje ta can ki fada masa, amma me ye na masa rad'a ga kunne?"

Sultan kuwa ba abinda yake banda dariya, shi gaba daya Taheer dariya yake bashi, ko ta ina Sultan ya masa zarra, amma ba laifi wajen gwadawa, wataqila ta zabi Taheer din shi ta bar shi.

"Basshi kawai Sulty Baby za ta hwada min, ba dai ke sanar da ita abinda za ki fadan ba?"

Daga kai Mubaraka ta yi, ta na dariya,

"Tau ya yi, sai an jiman ku"

Sallama ya miqa wa Taheer hannu su yi, kamar kar ya miqa hannun, amma ya miqa, ya kuwa matse hannun Sultan din da qarfi,Sultan ya ji matsar da aka masa, amma sai ya yi kamar bai ji ba, sai da Taheer ya gaji dan kan shi, sannan ya sake masa hannu, Sultan ya wuce ya bar Taheer da Mubaraka a wajen, anan ne Mubarakan ke bashi labarin zuwan su wajen No 1.

Sultana kuwa ta shiga d'aki ta tarar da Lawwali na ta kaiwa da kawowa, daga shi sai dogon wandon kayan da ya sanya, jikin shi babu ko vest, ajiye ledar ta yi, ta zagaya ta bayan shi, ta zira hannayen ta ta rungume shi, idanun shi ya kulle, dan jin yanda take taba shi a hankali, kan ta ta kwantar a bayan nashi, cikin murya mai sanyi da sace zuciyar mai sauraro Sultana ta ce,

"Auwal ka yi hankuri, ka yahe min duk abinda ka ke tunanin na yi maka shi, ba haka bane a raina,ka sani a duk duniyar nan ban taba son kowa ba, bayan kai, kai ne namiji me matuqar mahimmanci ga rayuwa ta, kai ne dalilin da ya sa na aikata komai,ban yi dan Daddy ba, dan Allah ka min murmushin ka mai kyawun nan ko zan ji sanyi ga rayuwa ta,bana so na wayi gari ban ga hwarin ciki ga huskar ka ba, ina so ka ci gaba da kasancewa cikin walwala da annashuwa, da annuri,ina yi wa Allah godiya da ya bani kai a matsayin miji na,kai ne rayuwa ta, kai ne komai nawa,kai ke bawa rayuwa ta farin ciki, jin dad'i da nishad'i, ina murmushi ne kawai in ka na murmushi, zan shiga damuwa da tashin hankali in ka dena fara'a,soyayyar ka da kulawar ka, su ne kawai abinda suke riqe da ni a yanzu, inna rasa su, zan rasa rayuwa ta ne gaba daya"

Hawaye ke zuba a idanun ta, kalaman ta sun yi gini mai qarko a zuciyar Lawwali, cikin sanyi ya juya, ya daga fuskar ta, ya sanya hannun shi duka biyun ya na share mata hawaye, bude idon ta tayi, ta kalle shi, gani ta yi ya na murmushi, nan da nan kuwa ta saki na ta, daukan ta ya yi cak, ya nufi gadon su da ita ya ajiye ta a bakin gadon ya durqusa a gaban ta, ya na wasa da hannun ta.

"Sultyna na fahimce ki, amma abinda na ke so ki gane shi ne, na yi wa qasa barna,ni babban mai lehi ne,ki na sane da cewa gwamnatin tarayya na nan ta baza jami'an tsaro a nemo mu duk inda muke, da ba dan mahaifin ki na da hannu a lamarin ga ba, kuma ba wanda ya sanni sai amintattun jami'an tsaro, tabbas da tuni an kama mu, to su ma su na so asirin su ya ruhu, shi ya sa ba su hwadi ba, amma tunda ni Allah ya sa na fahimci gaskiya yanzu ba ki ganin ya dace ace na kai kai na ga hukuma?"

"Auwal ka hini sanin halayen shugabannin nan namu, su kan su ba gaskiya ne da su ba, da ace qasa ce da ake tsaida Shari'a irin ta addinin Musulunci, tabbas da ni da kai na zan raka ka dan ka wanke kan ka, duniya da lahira, amma a irin wannan qasa , wannan yanayi, indai ka san ka yi lehi, to ka nemi yahiya wajen Allah, ka tuba iyakar tuba shi kenan, in Allah ya yahe maka shi kenan"

Dora kan shi ya yi a cinyar ta, ya zauna sosai a wajen, ya yi shuru ya na nazarin maganganun ta.

Fata take ta yi Allah ya sa ya fahimci abinda take so ya fahimta......

*Ni ma fata na kenan amarya Sulty*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 58:

"Ki shirya gobe ku je ku ga Daddyn ku, ki zauna a can nan da sati guda zan je na dauke ki, mu koma gidan mu"

Da wata iriyar murna ta fad'a jikin shi, ta qanqame shi ta na ihu, cikin hanzari ya daga ta ya na dariya, ya sanya hannun shi ya toshe mata baki, sannan ya sanya yatsan shi guda a kan labban shi da ke murmusawa,

"Shiiiiiiii, so ki ke a ce wani mugunta na ke miki?"

Janye hannun nashi ta yi, ta maida lips din ta, ta sunbace shi sau daya, sannan ta ce,

"Ko ma me zaka min, ko ma me ka min, ni taka ce, kai nawa ne, ina qaunar ka miji na, ina son ka miji na, kai ne abokin rayuwa ta har abada"

Shiru ya yi, ya ja ta ta zauna a jikin shi da kyau, sannan ya kama hannayen ta ya na wasa da su, kan ta ta ɗora a qirjin shi ta na sauraran bugun zuciyar shi, a hankali cikin sanyin jiki da murya ya ce,

"Sultyna sai yanzu na gano wani abu, wato duniyar ga aikin banza ce wallah, amma muke ta aikata sabon Allah, da ace na mutu ina kisan mutane fa? Da ace na mutu ina jagorantar ta'addanci da fasikanci fa? Da shi kenan wuta zani ko? da shi kenan ni rayuwa ta na zo a wahale zan koma a wahale, Sultana ba na jin na samu cikakke kuma ingantaccen jin dad'i, nutsuwa da kwanciyar hankali tunda an ka haihe ni na shekara hudu a duniya nake faman shan wahala, daga wannan na fad'a wancan, kullum cikin damuwa nake, shi kan shi farin cikin da ni ke ganin ina samu, ta hanyar shaye shaye, zunubi ne, kuma wahala ce wallah, indai har kin tabbata Allah zai yahe min duk kalar abinda na aikata, ko yanzu mutuwa ta risken ba ni da baqin ciki"

Da sauri ta kalle shi, tare da kada masa kan ta, murya na rawa ta ce,

"Auwal na tabbatar , kuma na yi imani da Allah, Allah ya yafe maka, domin shi ya yi alqawalin yafewa duk wanda ya nemi gafarar shi, ka kuma nemi gafarar shi, ina kyautata wa Allah zato, amma ba daidai bane ka dinga tunanin mutuwa ta dauke ka, in mutuwa ta dauke ka na zauna da wa?"

Hawaye ne suka fara zuba daga idanun ta, ita kan ta ba za ta iya tantance kalar soyayyar da take wa Lawwali ba, amma ta na da tabbacin duk sanda aka ce yau ba shi ba zata iya ci gaba da rayuwa mai kyau ba.

"Dan Allah ka dena irin maganar nan, ba na so"

"To ban koma wa, shi kenan?"

"Eh shi kenan,"

"To wace hira za mu yi?"

"Ina zuwa,"
Chapter 78 · 0% Book details