← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 93

Sashe 13

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me? Au wanga? Babu zahi,bari kuka barakan Yah Lawwali"

Dan murmushi tayi, cikin hawaye ta ce,

"Ni dai Auwal sunan ka, ba Lawwali ba"

"Tau na jiya, Auwal suna na ba Lawwali ba, mi na na ka saki kuka?"

"Sai yaushe na za ka dena kashe bayin Allah?"

Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba, can ya nisa ya ce,

"Sai sanda wadda nika so ta hwara so na"

"Yah Auwal ka bar wannan maganar , kayi tuba domin Allah, mutanen hwa da kuke kashewa bayin Allah ne, Allah ne ya halicce su, ya sanya musu rai, ya basu 'yancin su yi rayuwa, amma ku ke kashe su, ku ke hana su 'yancin da suka samu a wajen Allah na rayuwa, Yah Auwal in watarana aka zo har gida aka kashe wani a gidannan fa? Ko kuma su ka sace ni, ya z...."

Maruka kyawawa guda biyu ya ɗebe ta da su, a fusace ya daga pillow ya dakko qaramar bindigar shi, ya dora ta a saman kan shi, ya maida ta kan ta, daga baya ya daga ya harbi sama, sai da ya bula soron dakin, cikin tsananin fushi, idanun shi sun koma jajawur, ya kalli Mubaraka wadda ta ke durqushe kuma a takure a qasa tsabar tsoro,daga ta ya yi ya na son ta kalle shi, amma ta gama tsora ta da shi,cikin murya mai razanar wa ya ce,

"Duk wanda ya yi karambanin taba ki, ko wani nawa, se na kashe shi, sai na kashe dangin shi kafff, da mutanen garin su, duk wanda ya yi kuskuren taba koda tsilin gashin kan ki na, sai na ga bayan shi da dangin shi kafff, ke din rayuwa ta ce, ina son ki, sama da yanda nika son uwayen da sunka haifan, Barakan zan aurar da ke da hannu na, da hannu na da kai na zan kai ki dakin auren ki, barakana ke rayuwa ta ce, duk wanda ya tab'a ki ni ya taba, ko hararar ki mijin ki ya yi sai na ɗebe mai ijiya, (ido)"

Rungume junan su sukai, cikin kuka ta ce,

"Yah Auwal indai ka na so na kamar yanda ka ce, to ka dena abinda ka ke"

Rintse idanun shi ya yi, saboda abinda ke masa yawo a kan shi, zama ya yi, ya dafe kan shi, ita kuma ta na tsaye ta na kallon shi.

Kashe mutane a jinin shi yake, an horar da shi hakan tun da quruciyar shi, ya shiga gari ya tada masu zaune tsaye ba wani abu bane a wajen shi,su shiga gari su kashe kowa su kwashe dukiyar su da mata, da hatsin su ba komai bane, su yi ma 'yan mata fyade su kashe su ko su tafi dasu ba komai bane,amma duk da haka, akwai zuciya a qirjin shi, wadda bai san ta na aiki ba sai an tabo Mubarakan shi, a yanzu ya qara tabbatar da akwai zuciya a qirjin shi tunda ya fara son sultana, Mubaraka zuciyar shi ce, Sultana kuwa jinin da ke gudana a cikin zuciyar shi ne, in ba daya a cikin su, ba zai iya ci gaba da rayuwa ba.

Shi ya sani shi mugu ne, shi wata iriyar halitta ce, wadda ba ta da suna ,saboda sharrin ta, amma dik da haka ya fada so, shi so baya shawara da kowa in zai shiga zuciya, da ya na neman shawara da bai shiga zuciyar mutum kamar shi ba, da ko qanwar shi Mubaraka ba zai so ba.

Da ba zai damu da dangin shi ba har ya dinga zuwa gare su, duk da ya san hatsari da hakan zai iya haifar wa, a rayuwar su, soyayyar da yake masu ke kawo shi wajen su, duk da cewa tunda ya fara wannan harka bai taba sama da awa uku a gida ba, kuma ya kan jima bai zo ba. Miqewa ya yi, ya dafa kafadun ta ya ce,

"Barakana ki tai zuwa dakin ki, zan dan je wani waje, na kuma miki alqawarin daina wannan harka, amma fa ba yanzu ba, akwai abinda nika son yi,sai kuma na samu sauyin aiki"

Murna ta fara sosai, duk da ta so ya ce ya bari a take a wajen, amma akwai hope watarana zai bari, kamar yanda ya ce.

Ciki ta shiga da murna, Lamishi na zaune tsaki ta ja mai qarfi sannan ta ce,

"Gantalalliya in kin gama kai qarar mu wajen uban mu Lawwali sai ki je ki bidi makashin wuta ki kashe muna wuta,  dan kuwa b uban ki DanTalo ka biyan kuddin wuta ba ni ka biyan su"

Mubaraka bata ce komai ba ta wuce dakin ta, ta kashe fitila kamar yanda aka ce ta yi, tsabar masifa Lamishi ta manta cewar Gen ne ma aka kunna ba wutar nepa ba.

Lawwali kuwa takalmin shi da ta cire masa ya dauka zai saka ,ya na ganin shi fess ya saki murmushi, ya San aikin barakan shi ne.

Bindigar shi ya dauka ya soke ya fice.

************************

"No 1akwai wata yarinya na yi tambaya cikin gida an ce mun qaunar Lawwali ta, ina so a dauke ta ba tare da sanin shi Lawwali ba, a adana ta, domin da alama ranar da kuka kawo almajiri dan yin aikin nan ta gani"

A tsorace No1 ya kalli uban gidan nashi.

"Ranka shi dade Excellency sir akan yarinyar nan, Lawwali na iya tada jihar Zamfara kafff, ina ganin a jarraba ta a gani, in ta san sirin ka, sai a dau mataki, in bata sani ba, a barta kawai, in oga ya birkice sai zaman garin nan ya gagare mu"

"Me ya hwaru?"

Ba No 1 ba, hatta da gwamna Halliru,sai da ya tsorata, cikin kidima, da in ina suka juya maganar, da yabon shi akan aikin da suka cika ma wani kauye.

Bata rai ya yi, ya nemi waje ya zauna .

"Excellency sir zuwa na yi a sauyan wajen aiki, na gaji da shiga tafasa, cikin dokar daji kullum, ka aje ni kusa da kai, ina so ko yaushe qaunata ta so gani na, ta gane ni, kar ka damu, daji ne ba zan sake zuwa ba, amma in wani aiki ya taso, zani , ba tare da ta sani ba"

'Tabbas yarinyar ta san wani abun'

"Ok to na ji me kace, kuma na amince, za ka na bi na duk inda na ke, amma sai ka sauya shigar ka, da askin ka,"

No 1 na son magana gwamna ya katse shi ,

"Kai kuma daga yau, kai za ka dinga kula da maboya, kai ne incharge ,"

"Seeee ka yiiiii excellency, se ka maimaita ko su na so, ko ba sa so, ko mu kashe kowa a zauna ba kowa"

Kirari sosai Lawwali ya wa gwamna,kafin ya tafi ya nufi gida dan ya na son ya bawa Mubaraka labari.

Gwamna na wa Lawwali  kallon biri, shi kuma Lawwali  ya na masa kallon ayaba......

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 14:

Lawwali ya tattare ya koma sabon gidan da gwamna Halliru ya siya masa, ya na matuqar ji da Lawwali saboda shi din babbar kadarar shi ce, abokan siyasan shi na ja da baya da shi sosai saboda Lawwali , da ace ya inganta rayuwar Lawwali ne ya sanya shi a wata harkar halal da zai more shi, da matsalolin da za su shiga a gaba da basu faru ba.

Gida ne madaidaici mai kyau, dakuna biyu kowanne da bayi, sai tsakar gida da madafi irin na zamani, an zuba komai na more rayuwa, Lawwali ya yaba da wajen, gida ne da ke cikin unguwar da gwamna Halliru da iyalan shi suke ciki, a son Lawwali ma shi a kai shi cikin gidan, komai zai fi masa sauqi.

Har gida ya sa No 1 ya kai shi, ya dakko Mubaraka suka je ta ga wajen, Ita dai bin wajen take da kallo, shi kuwa kallon ta yake ya ga farin cikin da za ta nuna, amma ya ga shiru ,

"Barakana ba ki ga sabon gida na ba ne?"

"Yah Auwal na gani , a ina ka samu kuddin sayen wanga gida mai kyawu hakan ga,"

"Ohh baraka ki sa albarka kawai, ba ke ce ki ka ce na sauya sana'a ba? Tau wanga shi na matakin hwarko, duk wani laihi da na ke aikatawa na bari, yanzu diyar gwamna zan dinga tuqawa ke ga uniform Dina can? Ke gane su? Ina zuwa bari na saka ki gani ko suna yi min kyawu"

Daki d'aya daga cikin d'akunan ya fada, hannun ta da ta daga dan dakatar da shi, ta mayar ta na murmushin zumudin da yake, ta fara zaga wajen, No 1 na tsaye a waje ya na hango su tare da sauraren su, y na nad'e komai.

Lawwali ne ya dawo sanye da uniform kalar fari da baqi, wanda suka yi matuqar yi masa kyau, matsala daya, jikin shi ka na gani za ka san riqaqqen dan daba ne, hakan bai boye kyaun da ya gada wajen mahaifin shi ba, Dan Talo, domin kuwa da ace Dan Talo zai gyara da kyau, wata budurwar ma sai ta ce ta na son shi.

Murmushi ne mai kyau ya kwace wa Mubaraka ,ko ba komai ta kan yi farin ciki duk sanda ta ga yayan ta ya sanya manyan kaya, in suka fito da shi ya yi tsaf sai ya yi kyau gwanin sha'awa.

"Ka gan ka kuwa Yah Auwal , shin ka diba yanda kayan  ga sun ka yi ma kyawu? A gaskiya ba da ban ba dan ba sai na ce Aunty Sultana..."

"Shiiii,"

Shi ne abinda Lawwali ya ce, sannan ya wayance,ba ya son No 1 ya San shirin shi, ya jima da sanin No 1 na neman matsayi na musamman wajen Gwamna, so ba zai bari ya ji qudirin shi akan Sultana ba.

Daki suka shiga ya zaunar da ita bakin gado ya ce,

"Barakana ki fada min me ne ne a ran ki, gaba daya bakya farin ciki, murmushi kawai ki ke, amma ba har zuciyar ki ba"

"Yah Auwal ni dai gaskiya ina jin tsoro, in Aunty Sultana bata ji wani abu ba game da yanda ka ke ji fa?"
Chapter 13 · 0% Book details