← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 93

Sashe 49

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye take a daya bangaren, ta kasa tafiya ta na so ta masa magana, duk ya bi ya hade gabas da yammar fuskar shi, ya qi sakin ta, zagayawa ta yi saitin inda yake zaune ta duqar da kan ta, wani irin qamshi ya ji ya shaqa mai kwantar da hankali, bai gama shaqar qashim ba Muryar ta mai sanyi da kwantar da hankali ta daki kunnen shi, sai da tsigar jikin shi ta miqe,

"Auwalll.."

Rintse idon shi ya yi, da suka yi jawur, dan bacin rai, ya wara su a kan ta, maganar da ta kwaso a bakin ta take so ta yi, tini ta maqale a maqoshin ta, cikin sauri ta bar wajen, ta shiga office din ta, ta jima a zaune kafin nutsuwa ta same ta.

Lawwali kuwa wajen ya bari, bai tsaya ko ina ba sai wajen da ake horar da No 1, zaune ya gan shi, an bashi abinci da ruwa, Lawwali ya san mene ne yunwa, a lokacin baya can kafin tsohon Gwamna Lamido da suka kashe ya ja shi jiki, sai su kwana su yini basu ci ba, wannan dalilin ne ya sanya, ba ya qaunar barin duk wani wanda ke qarqashin shi da yunwa ko da kuwa kai mai laifi ne a wajen shi, qiyyyar No 1 da ke ran shi bata hana ana bashi abinci sau uku a rana ba, kuma abinci mai rai da lafiya.

Ya na zuwa danqar wuyan No 1 ya yi, ya danna a cikin doya da kwan da yake ci, sannan ya dago kan shi ya dinga falla masa mari,

"Duk a dalilin ka ne, a sanadin ka ne qauna ta ta samu mummunan tabo, da baka sace ta ba, da ba mai yi mata kallon 'yar iska, da baka sace ta ba, da har yanzu martabar ta da qimar ta na nan a idon mutane, yarinya ce mai daraja, yarinya ce kamila,ba ta da laifin kowa akan ta, in na muku laifi ku zo gare ni in kun cika maza, amma qauna ta? Qauna ta, mi tai muku halan, dole na sai kun tabe ta? Ka lalata wa qaunata rayuwa, ka mata tabon da ita kan ta ta na kyamatar kan ta, ta na zargin kan ta, me ya sa? Me ya sa kun ka taba qauna ta? Sai na yi ajalin duk wanda ke da hannu akan tabin qauna ta, wannan alqawarin Lawwali na,"

Wurgi ya yi da No1 gefe daya, ya fadi yaraf kamar tsumma, fuskar shi ta kumbura sintim, kamar wanda akai sukuwa akan ta,

Da rarrafe ya kama qafar Lawwali, ya ce,

"Oga...dan Allah,...dan Allah ...ka kashe ni ...in huta...na gaji....na gaji da shan kashin wahalar ga..dan Allah ka kashe ni..."

Damqo wuyan shi Lawwali ya yi, sannan ya ce,

"In kashe ka? In dinga huce haushi na a ina? Ai daga yau na dena kisan kowa in rayuwa ta ta ɓaci, wajen ka zan taho in huce haushi na"

Wani irin kuka mara hawaye No 1 ya saki, kuka ne na azaba, da tashin hankali, wurgi Lawwali ya yi da shi, ya fita ya bar wajen, wani dan bayan gida ya shiga dake a cikin wajen, ya samu ruwa a jarka ya tsiyaya a buta ya wanke hannun shi da fuskar shi, sannan ya bawa yaran shi umarnin, su ci gaba da gana wa No 1 azaba, amma kar su sake su bari ya mutu.

Amsawa suka yi da

"To Oga"

Sannan suka raka shi har bakin mota, ya tafi.

Sai da ya biya ta wani super market ya sayi kayan kwalama, da abin sha mai sanyi, sannan ya wuce, kafin ya isa sai da ya daidaita nutsuwar shi, sannan ya isa NGO din, ya na zuwa ya tadda ta zaune a saman kujera ta na ta danna laptop din ta, ta yi matuqar bada hankali akan laptop din ya shiga ba ko sallama, har yau ya kasa sabawa da yin sallama in zai shiga waje.

Daga kai ta yi, a dan tsorace ta kalle shi, murmushin da ta gani a saman fuskar shi, ya jawo nata murmushin waje, dan kuwa nan da nan ta bayyanar da haqoran ta a waje, kamar yaron da aka yi wa dariya ya rama.

Hannun shi na maqale a bayan shi ya shiga, sai da ya samu waje ya zauna sanan ya ce,

"Ran ki shi dade in shigo?"

Wata hararar wasa ta mishi sannan ta ce,

"Inna ce ah ah komawa za ka yi? Tunda har ka yi wa kan ka wajen zama"

"Eh sai in koma mana, tunda haka ki ke so"

Dan tura baki ta yi kadan sannan ta ce,

"Dan Allah ka daina hushi, ka daina hushin da zai tsorata ni har na kasa yi maka magana"

Dan bata rai ya yi, na wasu yan dakiku da ba za su wuce uku ba, ya sake fuskar shi,

"Mu bar waccan maganar, yanzu za ki sha wanga?"

Ledar ya dakko ya miqa mata, wani irin haske da annuri ke fita a fuskar ta, ba dan bata taɓa shan chocolates ba, ko sauran kayan kwalamar da ya kai mata ba, ah ah ,nashi na daban ne, kuma ko ba komai dama ta fara jin yunwa.

Lemo mai sanyi ta dauka za ta bude, hannu ya sanya ya karba, hannayen su sauran kadan su gogi na junan su, Lawwali ya yi saurin janye na shi.

Murmushi ya yi, sannan ya bude ya miqa mata, a baki, ta kawar da kan ta,

"Ran ki shi dade, mi na na ki ka tsoro, ni hwa ba dodo ba ne,"

"Ni dai ban ce maka dodo ba, kuma ni ban ji tsoro ba,"

Miqewa ya yi, zai zagaya inda take, ya na wani kashe mata idanu, ta na ganin haka ta fara tari, saboda kwarewa da ta yi, shi kuwa dariya ya fara sosai, ya zira hannayen shi duka biyun a aljihu, ya yi hanyar fita, sai da ya bude qofar sannan ya kalle ta ya ce,

"A haka ki ka son aure na ki na jin tsoro na? Ko kin zata na zuba wani abu ga lemon na? Ni ba dodo bane, Ni masoyin ki na Sultana, ina son ki, ina son ki da dukkan wata tsoka da jini na jiki na, ina son ki da ruhi na, duk randa aka ce maki Lawwali ya daina son ki, to ki tabbata ruhin shi ne babu"

Rufe qofar ya yi,ya na zuba Murmushi ya tafi, shin wannan ma kalaman yaudara ne? Domin jin su yake su na fita daga qasan zuciyar shi, ba qarya a cikin su.

Bayan fitar shi Sultana narkewa ta yi a kujerar, da kyar ta iya daidaita zaman ta ta ci gaba da aikin da ke gaban ta, duk cikin wata daqiqa dake wucewa cike take da farin ciki, da annashuwa a wajen ta, wanda bata yi zato ba, mussmman in ta tuna yanda suka zo wajen, rai a bace.

Lokacin tashi na yi, Lawwali ya dauki Sultana ya wuce da ita wajen cin abincin da ya taba kai Mubaraka, a tare suka ci abincin ya na ta musu hotuna, sultana ba qaramin dadi ta ji ba ranar, ta tabbatar wa da zuciyar ta, ba ita kadai take haukan son Auwal ba, shi ma ya na son ta.

Basu koma gida ba sai yamma liss, Sultana ko duba lokaci bata yi ba, sakamakon ranar ta na cikin yanayi na mata, ba sallah zata yi ba,ta kula da abu daya, wanda ya tsaya mata arai game da Lawwali, haka za a kira sallah a gama, bai je ba,gashi har an yi la'asar, ba ta son bata moment din su, dan haka ta bari kawai, sai watarana za ta masa magana.

Hajiya Ikee na ta jimamin ina Sultana ta tsaya, dan dai ta san duk iskancin Lawwali ba zai taba diyar Gwamna ba, akan abinda ta yi dazu (hummm baki san oga ba lalinyaaa🤭)

Motar su na shiga ta tashi a guje har ta na buge qafa da jikin kujera, ta leqa window, dauke ta ga Sultana da ledojin shopping, shi kuma ya rataya jakar ta ya na yanga, irin na mata, Sultana na ta kyalkyala dariya.

"Kan uban can, wato yaron ga ta nan ya bullo ko? Zai ko ci uwar shi Lamishi, gobe Daddyn su zai dawo, sai na sa an yi gunduwa gunduwa da naman jikin ka, na kaiwa karnu (karnuka)sun canye"

Kallon su ta ci gaba da yi, ta ga ya je daf da Sultana kamar zai hada jiki da ita, ita kuma ta sunkuyar da kan ta qasa, hannu ya sa ya daga kan ta, cikin kasala, ta wara idanun ta akan fuskar shi, tare da cije leben bakin ta na qasa kadan.

"Sulty Babyn Daddy, da gaske za ki iya auren driver din ki, kuma mai tsaron lahiyar ki?"

Cikin bude kyakkyawan bakin ta, tare da sassanyar magana ta ce,

"Auwal alqawari fa na maka zan aure ka, ba zan taba saba wa ba, ni ba na daga mutane masu saba alqawari"

"Kin tabbata kin yi alqawari za ki aure ni? A kowanne hali nake, kuma a kowanne yanayi nake?"

"Auwal in ka sake min fuska natsuwa ta ta dawo jiki na zan baka amsa ta gaskiya"

Murmushi ya yi mai sauti, sannan ya sake mata fuska, Itan ma murmushin take, sannan ta gyara tsayuwar ta ta ce,

"Na maka alqawari zan aure ka, a kowane yanayi ka ke, ba ruwa na da yawa ko qarancin ilimin ka, ba ruwa na da nakasar ka in ma akwai, ba ruwa na da kyau ko rashin kyaun ka, ni dai kai nake so, zuciyar ka ce ta qulla soyayya da tawa, ruhin ka ne ya ga ruhi na soyayyar ta qullu, gangar jiki na ta yarda taka ta zama abokiyar  rayuwar ta, Auwal zan aure ka, this is my promise to you"

Lawwali jin shi yake kamar ba ya duniyar,kalaman ta sun shige shi sosai .

"Idan Daddy ya dawo ki na ganin za ki iya tuntubar shi, maganar aure na, dan naturo manya na?"

"Ya ka ke magana kamar ka shiga zuciya ta ka yi leqen asiri?"
Chapter 49 · 0% Book details