← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 93

Sashe 58

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amarya na shiga gidan hankali ya koma kan ta da qawayen ta, Sultana ta gode ma Sultan a ran ta ya fi sau a qirga, ba dan shi ba da sai dai ta yi ta yawo ba qawaye, da kuwa abun bai yi armashi ba.

Bayan an yi sallar azahar ne aka daura auren Auwal da Sultana a Central mosque, da ke cikin garin na Gusau, a kan sadaki Naira dubu dari biyar, lokacin da Dan Talo ya ga Uban kudin da Lawwali ya damqa masa a hannun shi ya ce na sadaki ne, ji ya yi kamar ya suma dan takaici, a cewar shi wannan qarawa mai qarfi qarfi ne ai.

Haka dai ba dan ya so ba ya bada sadakin nan.

Kowa ka gani cikin farin ciki yake, Lawwali kuwa ba a magana, bakin shi ya qi rufuwa, sai doka murmushi yake, daga qasan zuciyar shi, ya na jin wani irin dadi mara misaltusa, kwanciyar hankali da nutsuwa ta baibaye shi.

Bangaren gwamna Halliru kuwa, zuciyar shi baqiqqirin haka yake jin ta, amma haka yake ta murmushi da dariyar dole, ga mutanen da suka halarci daurin auren.

Lawwali ne ya ja abokan shi gefe ya ce musu,

"To an daura auren hwa, daga yanzu zuwa kowane lokaci wasan zai fara"

"To Oga, muna maka fatan alkhairi"

"Godiya ni ke, da irin jajircewar ku, da tsaya min bisa gaskiya da amana, sai na taho"

Sallama suka mishi, suka koma inda suka fi wayo, masu iyalin cikin su, sai da suka leqa iyalin su, da iyayen su, sannan suka tafi daji.

*************************

Gidan Alhaji Dan Talo mutane ne danqam,Lawwali ya saki bakin aljihu, sai wadaqa ake da abinci da abun sha, Hajiya aunty 'Yabbuga su ne akan abinci, sai abinda tace a zuba, a gefe kuwa Kareema 'yar ta ta zo itama, sai ta debi kaji, da drinks ta boye a zani, ta wurga mata, ita kuma Kareema ta dauke ta kai gida, in ta juye ta koma, haka suka dinga yi, sai da 'Yabbuga ta tara naman kaza me yawa da snarks da drinks .

Kusan duk wanda ya zo daga kan 'yan uwan Lamishi da Mai Buruji, da Dan Talo sai da suka yi ta tambayar Mubaraka, Lamishi ba ta da amsar bayarwa, dan haka sai ta shashantar da maganar, Mai Buruji ce ta qirqiri karya ta ce Yayan ta ya kai ta karatu qasar waje,shi ya sa ba a gan ta ba.

Ba qaramin dad'in wannan qaryar Lamishi ta ji ba, sai ta ji ta qara son kishiyar ta ta, Dan kuwa Mai Buruji abokiyar zama ce ta gari.

Lawwali ya sanar da su, ba sai sun je daukan amarya ba, shi da kan shi zai dau amaryar shi, su yi bikin su kawai anan.

****************************

Kamar yanda al'adar amare take, yin kuka a duk sanda za a kai yarinya dakin mijin ta, Sultana ma, ba a barta a baya ba, daga ita har Gwamna Halliru kuka suke, Hajiya Ikee kuwa idon ta kyamas ba alamar hawaye, sai dariya take musu, Gwamna Halliru na matuqar ji da Sultana, gashi ya zama dole a gare shi ya hannun ta ta zuwa ga Lawwali, Lawwali da kanshi ya je daukan amarya, ko aboki daya bai raka shi ba, Hajiya Ikee ta tanadi wanda za su raka amarya dakin ta, ba su da wani yawa.

Da kyar Sultan ya samu ya banbare Sultana daga jikin Gwamna Halliru, ya na kuka, itama ta na kuka, haka Sultan ya damqa ta a hannun Lawwali, wanda ya ke jin zuciyar shi ta karye matuqa.

Anya zai iya bada auren Mubaraka kuwa? Wani iri yake ji a zuciyar shi na rauni, wanda ya sanya shi zubar hawaye, bashi da abinda yake so sama da mubaraka a rayuwar shi, nisan da ta mishi ba qaramin qona zuciyar shi yake ba, kallon gwamna Halliru yayi, cikin tsananin takaici da tsana ba dan shi ba, da tini da Mubaraka a wajen.

Da sauri ya ja Sultana suka shige motar da ya zo da ita.

Hajiya Ikee sai da ta ga Sultana a mota ta tabbata tafiya zata yi, sannan ta ji hawaye na gangare mata, daga musu hannu mutane suka dinga yi, mota biyar ne suka dafe musu baya, dan raka amarya dakin mijin ta.

Gidan da Lawwali ke da zama suka nufa, gidan ya sha gyara, an qawata shi sosai da sosai .

Lawwali qin bude motar ya yi, ya ce ma driver ya sanar da su, su shiga su ga gida, in sun gama su tafi, da kan shi zai shigar da amaryar shi.

Dariya mutane suka dinga yi, su na ganin he is very romantic, qawayen ta dik sun mata sallama, kuma sun shiga sun ga waje, sun yaba, mota suka koma aka maida su hotel din da suka sauka, washegari kowa zata koma garin su da qasar su.

Sai da wajen ya rage daga Sultana sai Lawwali, Sannan ya fita, ya bude mata qofa, ta na zira qafafun ta waje, ya sunkuya ya dauke ta, driver ya buɗe musu gate ya na dariya, wayar Lawwali na hannun shi ya na musu video.

Har saman gado ya ajiye ta, sannan ya amshi wayar shi, ya je ya rufe gida,ya koma dakin amarya, wadda ke ta kukan rabuwa da gida.

Lallashin ta ya dinga yi, ya na bata hakuri, da kyar ya samu ta yi shiru, gani ta yi ya cire kayan shi ya sanya na bacci, ya haye gado ya dau laptop din shi, da kallo ta bi shi, dama haka ake yi? Ina dan abinda ake kawo wa amarya? Ba zai je su yi Sallah ba dan godewa Allah? Ba zai mata addu'a ba da ake wa amare? Me ke damun shi?

Muryar Mubaraka ce ta karade dakin, cikin zumudin son gani da jin Muryar ta yake magana,

"Barakana an gama komai , an daura auren, an kuma kawo min amarya ta, ohh ni na manta, ni na dakko abata ta da kai na,"

Murna wajen Mubaraka ba a magana, se dariya take, ta na sanya albarka,

"Yah Auwal ina Aunty Sultana? Yaushe za ka turon pictures videos na yau,na ga na jiya, sun yi matuqar kyau,ba kadan ba gaskiya"

Da hannu ya yafici Sultana, wadda ita ma ta ji dadin ganin Mubaraka, gaisawa suka yi Mubaraka, ta musu fatan alkhairi, sultana ce ta ce.

"Wai Ni ina ki ka tafi ne akai bukin ba ke?"

Cikin shagwaba Mubaraka ta ce,

"Ina nan a Kan....."

Kit Lawwali ya kashe kiran, ran shi a dan bace, ya dauke laptop din ya sauka daga gadon.

Mamaki ya gama kashe Sultana a zaune, me kenan?

"Me ya faru? Bamu yi sallama ba ka kashe muna? Ban gama jin mi tace ba, ko dake da dukkan alamu Kano take son cewa"

Wata iriyar firgitacciyar tsawa Lawwali ya bugawa Sultana,

"Inji uban waye yace a Kano take? Ko kin ji sanda tace a Kano take? Kar na sake jin maganar inda Mubaraka take a wajen ki, ko da da nj ne, ballantana da wani"

Wasu irin hawaye ne masu quna, suke zuba a idon Sultana, mamakin shi ya hana ta rufe bakin ta, bin shi kawai ta dinga yi da kallo.

Bayan ya aje laptop din kwanciyar shi ya yi, ya juya bayan shi, ya na kallon gini .

Jiki ba kwari haka Sultana ta miqe, ta rage kayan jikin ta, ta shiga bathroom, ta yi alwala, ta zo ta tada Sallah ,dan a yanda ta kula ran shi ya dagule ba ta jin zai yarda su yi nafilar ma a tare.

Ta na idarwa ta miqe ta kashe fitila, ta kwanta cikin tsananin tsoro.

Lawwalin duk ya sauya mata a dare daya, dama maza haka suke lokaci qanqani za su sauya, to amma me ta masa da zai bata ran shi haka?

A hankali ta zira hannun ta jikin shi, cikin murya mai sanyi ta ce,

"Ka yi hankuri, ba zan sake maka, maganar inda Mubaraka take ba, balle in wa wasu."

Hannun ta ya riqe sosai a na shi, sannan ya ce,

"Dan Allah kar ki sanar wa da kowa, inna ce kowa ina nuhin kowa,"

"Inshaa Allahu"

Sultana dai na ta jira ta ji ango ya yi wani motsi ta ji shiru, har bacci mai dad'in gaske ya yi awon gaba da ita.........

*Ikon Allah, wannan wanne irin ango be????*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 44:

Abu kamar wasa, Lawwali ya qi sam wata alaqa ta auratayya ta had'a shi da Sultana, ba dan ta san dad'i ko wahalar abun ba, amma dai ta san kowanne miji da mata suna kasancewa a inuwa guda, bayan aure.

Duk wata kulawa da soyayya Lawwali na bawa Sultana, amma banda ta auratayya.

Yau sati Daya cif cif kenan da auren su, sultana na zaune gaban Laptop din ta, dan yanzu duk wani abu da ya danganci qungiyar ta, ta social network ta ke gudanar da shi, ta na transfer din kudi, da bada umarnin bude store a debi kaya duk ta internet ba tare da ta je ba.

Lawwali ne ya shiga gidan, cike da gajiya, da dukkan alamu ya yi wani aikin ne fitar shi, dan kuwa har da ciwo ya ji a hannun shi, da sauri Sultana ta isa gaban shi, ta kama hannun, ruwan dumi ta samo a yar qaramar roba, ta sanya detol ta wanke masa hannun, duk Surutu da sannu da zuwan da take masa bai amsa ba, sannan bai nuna mata yanda yake jin zafin taba ciwon da take ba, kalmar da taji ta fito daga bakin shi, shi ne ya  bata mamaki, dan bata ga dalilin sake yi mata tambayar ba.

"Kin ce kin amince za ki zauna da ni a ko ina ko?"

Cikin mamaki ta amsa masa, tare da qarewa fuskar shi kallo.

"Kin amince kin ji kin gani, ki na so na a kowanne hali nake a dukkan yanayin da nake ko?"

D'aga masa kai ta yi, alamar Eh, dan ita da kan ta ta rubuta masa hakan a wani message da ta taɓa yi masa.

"Kin yi alqawari ba zaki sauya alqawarin ki ba komai wuya komai rintsi? Kuma ko da ke san asalin gaskiyar wane ne Lawwali?"
Chapter 58 · 0% Book details