← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 93

Sashe 45

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

No 1 kuwa asalin matsoraci ne dama shi, makircin shi da iya hada tuggun yaqi ne ya sanya aka bashi muqamin da yake da, amma ba jarumta ba, hankalin shi in ya yi dubu ya tashi, wani irin duka aka sakar mishi a qirjin shi, da bakin bindiga, sai da ya fara jin jiri, daya daga matasan ne ya wuce su, ya bude dakin , ya fidda yan matan, sannan ya kai su mota, tayar da motar ya yi, ya shiga gari da su,sai kuka suke, su na bashi hakuri, sun fara bashi haushi, ta madubi ya ga yarinya daya ko a jikin ta, kallon waje kawai take, ta na lumshe idanu, ita bata damu ba kenan ko sace ta za ai?

"Kaiii dalla kun cika min kunne, Oga ne ya aiko mu, wace ce Mubaraka cikin ku?"

Da sauri suka nuna ta, cikin ran shi ya ce,

'Dole ki taurin rai yarinya,'

Sai da suka shiga garin sosai,ya tsaida mota ya wurgawa su Murjanatu kudi, ya ce su bace masa da gani, in sun je gida kome aka tambaye su, su ce basu sani ba, idan qaiqayin baki ya sa suka fadi wani abu, Oga da kanshi zai sa a kashe ahalin su gaba daya .

Sai kada kai suke, su na tabbatar masa sun gane, ba wanda zai ji komai, sun yi alqawari,godiya suka dinga musu, sannan suka fita daga motar a guje, yanzu tsoron yarda da mutane ma suke, tunda kusa da unguwar su ne, ko abun hawa ba su nema ba, da qafa suka nufi gidan su.

Mubaraka kuwa gidan Oga aka yi da ita, Lawwali na can ya yi order din abinci a best restaurant na cikin garin Zamfara, ya haɗa mata ruwan wanka da kan shi,ya gyara ko ina da kan shi,yaran shi na ta so su taya shi yaqi amincewa, so yake ya burge Mubarakan shi,so yake ya mata tarba ta musamman.

Ya na da qarfin kawar da duk wanda ya so, ba tsoro bane ya sa shi jinkirtawa har wannan lokacin, ba kuma gudun tashin hankali bane, kawai komai da lokacin sa, yanzu ne lokacin da ya debar wa Gwamna da iyalan shi,duk da a tsarin shi sai gwamna ya dawo, amma inaaaa ba zai iya jira ba, dan wannan karon bai neme shi ba, bai bashi wani aiki ba, ya tabbata akwai wani shiri mara kyau da yake akan shi,gashi yau Hajiya Ikee ta tsokane shi iya tsokana.

Ya na tsaka da kallon yanda ya gyara wajen, ya ji horn din mota,da sauri ya fita ya tsaya,yaran da ya debo guda uku, daya daga cikin su ne ya bude gate suka shiga.

Zuciyar Lawwali ta karye da ganin qanwar shi, idanun shi ne suka cika tafff da hawaye, cikin azama ya nufe ta ya rungume ta, sai da ya raba ta da qasa.

Jin ta a faffadan qirjin shi ne ya sanya ta sakin kukan da ya taho da wani irin qarfi da ciccira, da kuma daukewar numfashi, qoqari yake ya kwantar mata da hankali , ta nutsu ta dena kukan amma inaa, sai yi take, ta na qarawa, duk ta gigita shi,  ta kidima shi,rabon shi da shiga irin tashin hankalin yau tun sanda ya tabbatar da batan ta.

Daukan ta yayi cak ya shiga da ita ciki, daga shi har ita hawaye suke, gashi yanayin yanda take kuka da ciccira yaqi tsayawa.

Zaunar da ita ya yi a saman cinyar shi ya na lallashi sun jima a haka daga baya ya ji ta yi shiru,ta na ta sauke ajiyar zuciya mai qarfi, ya na dago ta ya ga ta yi baccin wahala.

Ba datti a tattare da ita, ba yunwa a tattare da ita, hasali ma gani ya yi kamar ta yi qiba ta yi haske.

Dakin da ya tanada domin ta, ya nufa da ita, dauke a kafadar shi, ya kwantar da ita, zama ya yi a bakin gadon ya na kallon ta, cike da tausaya wa, shi ne Silar shigar ta wannan mawuyacin halin, amma daga gobe komai yazo qarshe .

Cikin fushi ya miqe, ya sanya rigar shi a saman vest din jikin shi, ya dau bindigogin shi, sannan ya dau key din motar shi, basu zame ko ina ba sai gidan da aka ajiye su Mubaraka.

Ya na shiga ya tadda su a tsakar gida, No 1 cikin jini, No 4 na zaune a kujera, sai sauran yaran a tsaye sun yi shirin ko ta kwana.

Lawwali na shiga kowa ya miqe da kyau, direct wajen No 1 ya nufa, ya daga shi, ya dinga naushi, sai da ya sumar da shi sannan ya ce a sheqa masa ruwa a dakko shi.

Ba musu haka suka ja shi a qasa kamar buhu, suka wurga a bayan mota, suka rufe gidan suka tafi.

Kowa dai ya san mutum kamar Lawwali zai wahala ace maboya daya gare shi,dan haka daya daga cikin maboyar shi suka nufa, waje ne kamar daji, ba gida gaba ba gida baya, ihun ka banza.

Su na shiga Lawwali ya bada umarnin a daure masa No 1 sama a qasa, sannan a banqara hannayen shi baya a daure.

Cikin abinda bai fi minti goma ba har sun gama.
A wahalce No 1 ke magana, duk qoqarin su na su ji kasawa suka yi, sai da wani a cikin yaran Lawwali ya kasa kunne a bakin shi sannan ya ji me ya ce, dan murmusawa ya yi sannan ya ce,

"Oga ya ce ka kashe shi dan Allah"

Banza Lawwali ya yi da su, ya kammala hada abinda yake haɗawa, ya sa suka juya masa bayan No 1 ya sa a kunna Camera a dauki abinda yake yi.

Ana juya masa bayan nashi ya debi ruwan acid ya kwara masa a bayan, wata iriyar qara da ihu No 1 ya saki, daga baya ya yi shiru, jikin shi ya saki, suma na biyu kenan, jikin No 4 sai rawa yake, tsabar tashin hankali, wannan azabar ya gudar wa kan shi tun asali.

Kamar Lawwali ba zai magana ba, ya duqa ya kama fuskar No 1 ya ce,

"Amma dai ka hi kowa sanin ba aikin Allah muke ba ko? Da aikin Allah muke da masallaci za a same mu, dan haka in ka na ganin ka hwara bautar Allah da gaskiya, daga yanzu tau ka hwara addu'a tsakanin ka da Allah'n shi dau rayuwar ka ka huta,amma da kai, da duk wani mai hannu cikin sace qauna ta, ko wane ne shi,ko uba na na sai na ga bayan shi, ko shi anka bawa mulkin qasa baki daya ba gwamna ba, sai na ga bayan shi , wannan alqawarin Awwal yayan Mubarakaa ne"

Da qarfi ya saki fuskar No 1, jikin shi ya hau lilo a wajen.

Kashe Video akai, ya amshi wayar shi, ya bar wajen, No 4 ya bi shi, cikin matsanancin tsoro,

"Ka shirya komai akan abinda muka yi magana ?"

"Eh...oga...na kammala komi"

"Good, gobe da qarhe shidda na sahe zan same ku a tasha"

"To Oga"

"Kafi kowa sanin hali na in aka ci min amana, kar ka yi wasa da amana ta, rayuwa ta zan dauka na baka, kar ka ci amana ta, Taheer in ka bari quda ya sauka akan Barakana, hummm"

Iya abinda Lawwali ya fada kenan,ya fada mota ya bar wajen.

**************************
Mubaraka bata tashi farkawa ba, sai ukun dare, ko da ta farka a tsaye taga Lawwali ya na kallon ta, hannu ta miqa masa cike da shagwaba, shi kuwa da sauri ya kama, ya zauna a gefen qafar ta, ya kai hannun ta bakin shi ya sumbata.

Murmushi ta yi, sannan ta ce,

"Yah Auwal ina so na ga Ummaana"

Wata tsawa ya daka mata sai da dakin ya amsa, Ita kuwa ta manne da jikin gado tsabar tsoratar da ta yi, nan da nan ta hau kuka, jikin shi ne ya yi sanyi, a hankali ya daidaita nutsuwar  shi,ya zauna gefen ta, ta yi baya, ta na zubar da hawaye,

"Barakana duk irin kewar ki da na yi, ki rasa me zaki fara magana akai, sai mutanen da basu damu da batan ki ba? Mutanen da ba su daina duk wata harkar su ta yau da gobe ba akan batan ki? Barkana Ni kadai ne na damu, Ni kadai ne na ke kasa bacci saboda rashin ki, basu damu dake ba, gobe zaki bar garin nan, ki yi nesa da kowa, ban damu da abinda zai same su ba, ke ce rayuwa ta, kowa ya san da haka,abokan gaba za su iya amfani da ke dan cutar dani, dan Allah kar ki min musu, ki bi duk abinda na ce ki yi, kin sani ba zan cutar da ke ba ko?"

D'aga kai ta yi a hankali, maganganun shi sun qona ran ta sama da yanda wuta ke qona leda, ta yaya za a ce iyayen ta basu damu da batan ta ba, iyayen ta fa na cikin ta, amma ba abun mamaki bane, ga duk wanda ya san halayyar su.

"Yah Auwal na ji na amince, amma ina neman alfarma"

"Kar ki ce mun zaki je ganin su"

Shiru ta yi ta na kuka a hankali,sautin kukan ta kamar ruwan dalma ake diga masa a tsohon ciwo,

"Ok tau ya isa haka nan, ina kai ki gobe"

"Yah Auwal ina so na ga Aunty Sultana, na yi kewar ta, na san ta damu da bata nako? Har mafalkin ta ni kai"

Murmushi mai sanyi ya yi, wanda shi kan shi bai san ya yi ba, Mubaraka na ganin haka ta tabbata har yanzu akwai soyayya a tsakanin su .
Chapter 45 · 0% Book details