← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 93

Sashe 26

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan lokaci ne na qaratowar zabe,lamura ka yi ma wasu daga cikin mutanen qasa wahala da tsanani, tare da qunci , wasu kuma lokacin ne suke cikin walwala, da nutsuwa da yalwa, harkokin samun su ta bude, rayuwar su ta yalwatu da dukkan abinda suke burin samu.

Gidan gwamnati Hajiya Ikee ta koma da zama, mutane na zuwa, wannan ya shiga wancan ya fita, watarana har fita take da muqarraban ta unguwanni dan kai masu taimako, mutanen mu kuwa dake a hannu suke, ana buqatar abincin da wasu kayan masarufin duk sun manta da wahalhalun da suka sha abaya, da rashin kula su da gwamnatin bata yi ba a baya, ta na da manyan mata a unguwanni daban daban, da ke rabon kayyaki da abinci, tare da kudi wa mata a gidaje, domin a sai quri'un su, ko me ya sa da ba a tallafi matan ba sai zabe ya zo a bi su da dubu ko dari biyar da atampa oho.

Motoci ne masu numfashi, da qoshi ke yawo a saman hanyar  qauyen da duk titin ya farfashe, mutanen qaramin kauyen kuwa, sun yi babban shirin tarbar Gwamna da muqarraban shi.

Motocin na tsayawa, securities suka zagaye motar Gwamna, 'yan jarida na tsaye na jiran fitowar shi su fara daukan rahoto, manyan motocin abinci da suka zo da su ne suka qaraso, qatti na ta sauke buhunan abincin, mutanen qauyen natsaye su na kallon su, sai da suka bari Gwamna Halliru ya fito an fara daukan shi,tare da fadin rahotanni na son rai da zuciya, sukai  ta fitowa da gorori, da bulalai, tare da duwatsu, dukan motocin suka fara, tare da jifan su da duwatsu su na fadin

"Ba ma yi ! Ba ma yi !"

A gurguje Gwamna ya fara qoqarin komawa motar shi, cikin rashin sa'a wani matashi ya maka masa gora a goshi, babu bata lokaci kuwa daya daga cikin masu tsaron gwamna ya zari bindiga ya harbe matashin, qarar bindigar ne ya sanya mutane rudewa, wajen ya kacame da hatsaniya, wasu na qoqarin guduwa, wasu na ganin ko za su rasa ran su sai sun cimma abinda suka yi niyya.

A guje motocin gwamnatin ke guduwa, wasu daga matasan kuwa sun hana a dauki manyan motocin abincin, sun kakkare ko ina.

Haka wasu daga muqarraban gwamna suka gudu da qafafun su.

Sultana ba ta jima da komawa gida ba, ta idar da Sallah ta kwanta, ta na hutawa ta ji qarar motoci, dan tsaki ta ja ta daki pillow ta toshe kunnen ta, tare da yin goho a gadon, ta na dukan gadon, cikin dan kukan shagwaba ta dauke pillown daga kan ta ta miqe, idanun ta lumshe take tafiya, kafin ta isa motocin sun shiga gidan, labule ta daga ta leqa qasa, ta na hamma, tare da murza idanun ta, ba shiri ta wattsake  daga baccin da ya taru a idon ta.

Mahaifin ta ta gani cikin jini, farar babbar rigar shi ta gaba tayi faca faca da jini, da sauri ta bar jikin window ta zari rigar ta ta saka, ta manta gaba daya kanta ba dankwali ta fita parlour ,securities na waje, gwamna ya shigo, ciki, cike da bacin rai, wani daga securities din ne ya shiga ya sanar da zuwan doctor, Dr zama ya yi a kujera ya na fidda kayan aiki, Gwamna Halliru na tsaye ya na bada mummunan Umarnin da ya sanya Sultana kusan suma a tsaye, da wa mahaifin ta yake waya haka? Wanne azzalumin ke taya mahaifin ta aikata mummunan aiki irin wannan?

Zama ya yi ya na fitar da wani irin hucin bacin rai da baqin ciki, Dr ya fara gyara masa ciwon shi, ko zafi bai nuna alamar ya na ji ba, tsabar yanda ran shi ya kai qololuwa wajen ɓaci, tsoro ne ya kama Sultana, har ta kasa qarasawa wajen shi .

Hawaye ne kawai ke zuba a idanun ta, bakin ta na rawa, zuciyar ta na bugawa da qarfi, hannu ta sa ta shafi kan ta, ta juya sama da gudu, wayar ta ta dauka, ta na kallon ta, shin Hajiya za ta kira? Ko Sultan? Ko kuma......

Lawwali ne ya fado mata a rai, lokuta da dama in mutum na cikin damuwa, ba wanda ke fado masa a rai sai masoyin shi, wannan dalilin ne ya sanya Sultana tunawa da mahaifiyar ta, da d'an uwan ta, qarshe ta dire akan lawwali, (hakan na nufin Sultana ta kamu da son Lawwali?) cikin hanzari ta kira shi, ta jima ta na ringing bai daga ba har ta katse, sake kira ta yi, ya na fara ringing ya dauka, a gaggauce ya ke magana, daga baya ya tsaya cak, saboda jin kukan Sultana da ya yi.

"Ran ki shi dade lahiya? Me ya hwaru ki ke kuka?"

Ta kasa magana sai kuka take, da kyar ya samu ta nutsu.

"Daddy ne...Daddy ne na ji ya na waya....wai za a je wani qauye a tashi garin,....ya na so a kashe kowa...har mata da qananan yara...ba ya so a bar kowa ya rayu, saboda sun zubar masa da jini...ya bada umarnin a sa wa garin wuta..Auwal ya zan yi? I need your help pls"

Kuka ne sosai ya kwace mata, fita ta ɗan yi waje ta tsaya jikin bene, ta na hango Gwamna Halliru ya na bada umarni ga 'yan jarida kar su kuskura su saka abinda ya faru a zuwan su qauyen a kowacce kafa ta yada labarai, har kuma abinda zai faru washegari.

Sultana sanar da Lawwali tayi abinda taji ya na faruwa, Lawwali kuwa ya jima da dauke wuta, ya na cikin tsaka mai wuya, shin wa zai bi? Gwamna ko Sultana? Ta na neman taimako a wajen shi,ba tare da sanin shi ne wanda aka bawa Umarni ya je da yaran shi su tashi qauyen ba.

Amma zai jira ya ji wanne irin taimako take nema a wajen shi.

"Ran ki shi dade sanar da ni irin taimakon da ki ke nema a waje na"

Cikin kuka sultana ta ce,

"Ban sani ba...Ni ma ban sani ba...just stay with me on the phone, har sai Sultan ya dawo, ina jin tsoro, ba na son kasancewa ni kadai, ina jin tsoro"

Takure take a jikin matattakalar benen, a gaban idon ta mahaifin nata ke ta abubuwan da ba ta taɓa zaton zai aikata ba, Lawwali na sauraron kukan ta, har cikin qoqon zuciyar shi, yaran shi na tsaitsaye su na jiran umarnin shi.

Jin zuciyar shi yake kamar wuta, kiran Gwamna ne ke shiga wayar shi, cikin sanyin murya ya ce,

"Ran ki shi dade, ina da wani kira mai mahimmanci na shigowa, ki yi min hankuri na daga, zan sake kiran ki"

Shiru ta yi, bata amsa ba, banda kuka ba binda take yi, kashewa ya yi ya dauki wayar Gwamna, cikin tsawa da fada yake magana.

"Shin kun tahi ko kuwa?"

"Mun shirya yanzu za mu tai"

"Ku kashe kowa, kar ku bar kowa da rai,"

"Tau ranka shi dade"

Ya na gama magana da gwamna ya sake kiran Sultana, bata dauka ba, ta na zaune a wajen ta na kuka, komai ya tsaya mata cak, tsoro da mamaki duk sun kau daga zuciyar ta, gata nan ne dai kawai.

Jin bata dauka bane, ya sa Lawwali bawa yaran shi umarnin tafiya, nan da nan kuwa suka fita, suka shisshiga motocin su, dauke da muggan makamai, da bindigogi, da bama bamai,basu shiga kauyen ba sai da suka  je dajin su suka tsara komai, sanan suka qara mayaqa, cikin dare suka shiga garin, mutanen garin sun sakankance, su na ta murna, da jin dadin samun kayan abincin da suka yi, tare da korar azzalumin gwamnan nasu.

Kwatsam suka fara jin harbi ko ta ina, da tashin qananan bama bamai.

Gari fa ya rude, da tashin hankali da iface iface, duk wanda ya san Lawwali a zahiri ba zai gane shi ba a yanzu, gaba daya wannan mutumin ba shi da digon imani, ba tausayi a zuciyar shi.

Kashe mutane kawai yake kamar ya na kisan kiyashi.

Basu suka bar garin nan ba sai da suka maida shi kamar toka, daidaikun mutane ne suka samu guduwa, suka bazama daji, da wasu qauyukan da ke kusa da su.

Qarfe sha biyu na dare, suka bar qauyen, direct gida Lawwali ya nufa a motar shi,ya na zuwa ya yi wanka ya ci abinci, ya kwanta, juyi ya dinga yi, wanda ya rasa dalilin yin shi,a hankali tunanin Sultana ya fara mamaye zuciyar shi mai kama da dutse, soyayyar ta da soyayyar mubaraka ne kadai ke raya zuciyar shi, banda su ba shi da wani abu da ke narkar da zuciyar shi.

Wayar shi ya dauka ya dinga kallon hotunan su, ya na sakewa, ya rasa yanayin da yake ciki, ko kuma abinda yake ji a zuciyar shi .

Bai san sanda ya danna kiran Sultana ba, ya kara a kunnen shi, cikin shaqaqqiyar Muryar  da ta ci kuka ta gode Allah ta dauka.

"Ran ki shi dade, baki bacci ba?"

Kallon qur'anin da ta gama karantawa ta yi, ta lumshe idon ta hawaye suka zuba, ta ce,

"Eh ban yi bacci ba, kai me ya hana ka bacci?"

Shiru ya yi, tare da gyara kwanciyar shi, ya lumshe idanun shi ,sanan ya ce,

"Na kasa bacci, ban san me ke damu na ba, Sultana ina da wani babban al'amari a tattare da ni, wanda ni ka jin matuqar tsoro akai"

"Me ne ne wannan al'amarin? Ko zan iya sanin shi?"

Da sauri ya kawar da maganar ta hanyar tashi zaune ya ce,

"Ran ki shi dade, ya kamata ki kwanta ki bacci, akwai gajiya a tattare da ke sosai "
Chapter 26 · 0% Book details