← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 93

Sashe 3

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ahayyyyeee,Allah gani inji gurguwa, watarana kau kuturu zai hadiyi yawu da quda,dan wani alkakin na sarakai ne,ba na siyan gama gari bane...keni rabu dani da d'umin banza, bamu labari mi na na ki ka son hwada mana dazu ki ka ga dodon ki,ki ka gudu"

Wadda ake kira da Ta Yahai (Yahya kenan) ita ce cikin dariya ta ce,

"'Dana ya shigo gari kenan, dan albarka me maganin munahukan shiyya"

Dariya suka sanya, Yabbuga kuwa rai ta bata, dan ta san ci mata fuska suke, sun san yanda take tsoron Lawwali.

"Ke rabu da Ta Yahai, bamu musha" In ji Lamishi da ta qagu ta ji me' Yabbugan zata fada masu.

Zama ta gyara dan jin an sosa mata inda ya dame ta da qaiqayi.

"Hummm na taba ku da alheri, kishiya ta taɓa kishiya da bakin wuta....jiya akai dirama a kwarkwadar mu, tsakar dare nijji ana ihu, ana bada hankuri, nittashi zaune ni da Dan Jumma, ko da mun ka saurara, ashe mutuniyar aka liqa wa mugun kashi,"

"Kaiii wanga mutuni ba dan Sunnah bane, mi tai Mai halan?" Cewar Mai Buruji da ta matsa daf da Yabbuga tsabar son jin gulma .

"Yo ai abun ba sabo bane, sun yini ba bu ko kwayar hatsi,dare ya yi,ya tai amsar haqqi nai ta hana, shi ko yabbuge banza, ya amshi abi nai, ya barta nan ta na kuwwar banza"

"Ohhhh wanga shi aka kira qarfin hali, a dake ka kuma a hana ka kuka, gaskiya mutunin ga azzalumi na" Lamishi da ta qi jinin ta ji ana wulaqanta mace ta fadi hakan, lokuta da dama ji take da ace su na magana da Hansatun Isa da sai ta mata magana, ta koya mata yanda zata kwaci 'yancin ta wajen Isa, ko ya hakura da mugun halin shi su zauna lafiya.

To amma Hansatu ta kame kan ta, mace ce mai kame wa matuqa, da kiyaye dik wani abu da zai hada ta hulda da su Yabbuga, tunda ta san halin su.

Su na nan su na gulmar ta, ta na gida ta na fama da matsanancin ciwon qirji, ba komai ne ya kawo mata shi ba, illa rashin cin abinci, yaran ta ta kalla guda uku, biyu mata ,daya namiji, suna ta kai loma, hannu baka, hannu kwarya, akan qanzon da ta masu fate da shi.

Lallabawa ta yi ta dan debi loma daya ta kai bakin ta, wani irin zafi da murdawa qirjin nata ya yi, sai da ta durqusa,tare da rintse ido, hawaye ne suka sauka mata, da sauri ta share,dan kar yaran su gani,bata samu nasara ba kuwa, qaramin yaron ta mai shekara hudu ya ga sanda ta ke share hawayen,dakatar da cin abincin ya yi, ya ce,

"Umma sannu, qirjin ki na ka ciyo?"

Cikin murmushin yaqe ta ce,

"Eh shi na ka ciyo Ahmad, amma yayi sauqi, kaga Ni ma har na tashi ? Maza ka ci abincin ka yaron kirkin Ummaa,ku ta tahiya makarantar Allah"

"To Umma"

Amina da Bilkisu ma sannu suka mata, sannan suka dauki dan sauran faten da suka rage, suka aje a gaban ta, suka ce sun qoshi.

"Abincin da ba shi da yawa, ku canye shi maza, kahin ku dawo,inshaa Allahu zan sama mana wani abun, ku canye ku tafi makarantar Allah maza"

Qin ci suka yi, tare da barin kwanon a gaban ta suka tafi da gudu wanke hannu, suna gama wankewa, Amina mai shekara goma,ta shirya Ahmad cikin wasu yagaggun uniform din da sun dage masa, ita kuma hijabi kawai ta saka tamiqawa Bilkisu mai shekaru takwas nata hijabin, su na kammala sakawa suka yi wa umman su sallama suka fita, bakin su dauke da addu'a .

Ta gaban su Mai Buruji yaran suka wuce, sai da suka gaishe su sannan suka tafi,amsawa sukai su na bin su da kallo.

"Dazu fa Baban su har da shi a garkar mu, wajen cin abinci"

"Ai wadda kika san dan shi d'ai muka zuwa aiki,kullum shi na garkar mu, da ya qare cin abinci shi tai yawo"

Yabbuga ce ta karkace zata yanko wata gulmar Isa ya taho zai shige gida,cikin izza da isa da taqama ya ke tafiya , wanda be san shi ba zai rantse wani namijin azziqin ne.

Har su na rige rigen gaida shi ,juyawa ya yi, ya amsa tare da tsokanar su Lamishi .

"Ah ah matan Dan Talo kenan, irin wanga gayu haka awaz-zaku biki? Ko dake masu hidima gidan Gwauna ai dole ku wataya "

Murmushi suka yi, su na irin abun nan na mata in an yabe su, Yabbuga kuwa tsaki ta ja, sannan ta ce,

"Haramun dai, ka tsaya yabon matan wani, ka baro ta gida ba yabo"

"Yabbuga kishi takai da ku wallah, kun San bata iya ganin wani ya yi abu, batai ba"

Dariya suka sanya har da shewa, ya shige gida,ya bar Yabbuga da mita.

Kafin ya qarasa shiga ya daure fuska tamau kamar ba shi ne ya gama hira da matan wasu a waje ba.......

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 4:

Jin motsin shi ne ya san ya ta miqe wa da kyar, hankalin ta tashe, domin shi din kamar wani dan aiken mutuwa n ne a gare ta, rashin fitar ta tsakar gida zai iya ja mata masifa a wajen mijin nata da take tsananin so da qauna.

Murmushin yaqe ta sanya a labban ta, tare da yi masa sannu da zuwa, bai amsa ba, sai shura buta da ya yi da qafar shi ta hagu, cikin wani irin mummunan yanayi ya juya ya kalle ta, yawu ta hadiya da kyar, cike da tsoro, bakin ta na rawa ta ce,

"Ka yi hankuri, su Amina na sun ka wanke hannu, Na....naaa manta ban zuba ruwa ba"

"Zaki debo min ruwa ko surutun banza za ki tsaya yi min?"

Da sauri ta tafi daukan butar, kafin ta sa hannu ta dauka ya tura mata da qafa, dan baya ta ja saboda kar ta bige ta, sannan ta duqa ta dauki butar, wajen diban ruwan daidai inda yake a tsaye ne, ya diba kawai, amma sai ya wahalar da ita.

Ta na gama zubawa ta duqa ta fara zuba masa, qamshin miya ta ji a hannayen shi a lokacin da ya tara su gaban ta dan ta zuba masa ruwa.

Murmushi mai ciwo ta yi, ta tabbata yau ma ya ci abinci a waje, ba tare da ya damu da ita ko yara sun ci ko basu ci ba.

"Baban Amina, nicce akwai dan kuddi wajen ka na dahwa muna abinci?  Yau kwana uku ba mu ci abincin kirki ba, dazu ma qanzo na nissamo gidan Yabbuga niddahwa mun ka ci, kuma da alama yaran nan basu qoshi ba"

Hannayen shi ya sanya a qugun shi ya na kallon ta, irin kallon nan mai kidimar da wanda ake kallo, ta gigice matuqa, dan bata san me zai je ya zo ba, amma koma mene ne, bata da zabi, dole shi ne zai kula da su, shi ne zai yi mata duk wani abu da take buqata ita da yaran su .

"Kin raina Ni ko? Na ce kin raina Ni ko? Kin fara min tambayar titsiye ko? To ina da kudi,kin gan su, ba zan bayar ba"

Hannu ya sanya a aljihun shi ya zaro dari bakwai, ya nuna mata, sannan ya miqa su daidai fuskar ta,

"Ko zaki kwata ne? Tunda na ga kin yi qarfin halin yi min magana yanzu, ban sani ba ko kin yi qarfin duka na ki amshi abu a hannu na ne"

Kada kai take ta yi, tare da fadin,

"Ah ah, ka yi hankuri, ba haka nika nuhi ba"

"Hansatu , Hansatu, Hansatu ki kiyayen, kar ki bari na juyo kan ki ba zaki ji dadi ba"

Duqar da kan ta tayi, tare da share majinar da ke diga daga hancin ta, saboda kukan zuci da take,

Daki ya shige, ran shi a matuqar bace.

Babban abinda ya ban mamaki, haushi, da tausai shi ne, kwano ne ajiye a wata shimfida, abinci ne a ciki, kalar wanda ta bawa yaran ta da rana, duk yunwar da take ji, bata iya ci ba, sai da ta aje masa.

Dan mugunta irin ta Isa dauka ya yi, ya fara ci, sai da ya cinye tass ya sude kwanon ya yi fatali da shi ya bar gidan.

Qarfe biyar da rabi, ta rasa ya zata yi, dan haka mayafi ta dauka, ta yafa a saman kan ta, sannan ta saka takalmin ta silifa da ya sude, ya ke qoqarin bulewa.

Jan qofar gidan ta yi, ta nufi dandalin gulmar su Lamishi, duk wanda ya kalle ta da kyau zai tabbata ta sha kuka, amma ya zatai, ba zata iya boye yanayin da take ciki ba, tunda mai rufa mata asirin ya tone shi kowa ya san halin da suke ciki,  (ba mai rufa asiri sai Allah).

Ta na zuwa ta Gaishe su, dikkan su amsa wa sukai, cikin zumudin son jin me ya faru, ba wai dan su taimaka mata ba.

Shiru ta yi, can suka ci gaba da hirar su, amma hankalin su na kan ta, gani ta yi lokaci na tafiya, cikin sanyin murya ta ce,

"Uhmmm... Nicce ko akwai wadda ke da wanki cikin ku? Ku kawo na hwara na kuddi, amma za a hada da kuddin wanki da klin da toka(sabulu) "

Kusan a tare suka hada baki suka ce babu, ji ta yi kamar an daki zuciyar ta, da me za su ci abinci dare?

"Ko wani aiki ba ku da shi? Wanda zan yi ku biya Ni?"

Lamishi ce ta ja ta  gefe, ta ce,

"Ina da wankau, amma fa na yau ne kawai zan baki, ba wai kullum zaki zanka(dinga) yi min wanki ba"

Kamar ta durqusa a qasa ta gode mata, haka Hansatu ta hau godiya.

Gidan Dan Talo suka koma , Lamishi ta bata wankin, ta bata kudin omo da sabulu, ta biya ta ladan wanki dari uku, godiya ta dinga yi har da kwallar ta.
Chapter 3 · 0% Book details