← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 93

Sashe 60

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lawwali na can na casun shi, da mutanen shi, kamar ba abinda ke damun shi, nan kuwa qarfin hali ne, ba ya so ya gina rayuwar auren su akan qarya, tsakanin shi da Sultana ya na so su fahimci juna, su gina zaman su akan gaskiya da gaskiya, in ya yi nasara ta karɓe shi, ta aminta da shi,zai fi kowa farin ciki, da hakan zai amfani, wajen musguna wa Gwamna Halliru.

In ta qi karbar shi ya na da sauran shaidun da zai nuna mata, ya tabbatar da cewa za ta yarda da shi, za kuma ta zauna da shi.

Bai koma dakin ba sai sha biyu da rabi na dare,dauke yake da abinci, wanda gasasshiyar kaza ce, da madara, sai ruwan sha.

Ajiye wa ya yi, ya zauna a bakin gadon ,a zaton shi ta yi bacci ne, ya ja bargo ya rufe ta da shi, zai tashi, ya ji Muryar ta da ta sha kuka ta gaji, ta ce,

"Me ya sa ka biye musu, ku ke aikata barna a bayan qasa? Mai ya sa ka zama daga bayin Allah wadan da yake fushi da su, ya tsine musu? Ko ka san hukuncin wanda ya kashe rai kuwa a wajen Allah? Me ka ke nema a duniya da ya kai ka aikata munanan zunubai haka? Kaico na ni Sultana na yi asara a duniya, ban yi dacen masoyi da iyaye ba, kaico na, kaico na"

Yanayin yanda take kuka, sai da ya kawo wa Lawwali kwalla a idon shi, cikin qunar rai ya ce,

"Ba da so na bane, ba laihi na ne ba, laihin shugaban nina ne, sun qi su bani taimako a lokacin da na je musu ina cikin mawuyacin hali, na je su tallafe ni su agaje ni a lokacin da nake tsananin buqatar hakan,amma suka maida ni dan ta'adda,mai sace yaran mutane ya kai musu, ba na mantawa ina da qarancin shekarun da ba za su wuce shekara sha biyar ba, lokacin mahaifi na ya na ganiyar zaman banzan shi, caca da shan sigari su kadai ya sanya a gaba, ga iyayena mata basu da aiki sai dambe da tashin hankali a shiyya ( unguwa).

Duk inda zaman lafiya bai samu ba, talauci ya fi wahal da wadannan mutanen.

Sai mu kwana mu wuni ba mu ci abinci ba, a lokacin mahaifiya ta na dauke da cikin Mubaraka, na matsu matuqa na samu qani ko qauna, wanda zan dinga gani na ji dadi ga rayuwa ta, wanda zan dinga hwadi wa abin da ka damuwa ta, tunda iyaye na basu damu da rayuwa ta ba tun asalin tashi na, sai na kwana na wuni ban ci ba, ban sha ba, ba mai tambaya ta ya na wuni, ko ya na kwana, sai nai ciwo na warke ba wanda ya sani,sai an ga na rame a ce 'Baka da lahiya ne halan?'

Na sha wahalar rayuwa matuqa a baya, saboda wahala dole na bar makaranta, na fara bin abokan banza bayan na sauke qur'ani, na ajiye boko, ina Jss 2, na fara bin wani babban dan daba a nan shiyyar mu, muna bin qananan 'yan siyasa, su na saka mu nemo musu yara qanana, tun ban san mi ake da yaran ba, har na sani, sai da  ya zamana na hwara dokan yaran shiyyar mu ina kaiwa, sai dai a nemi yaro a rasa, kuma da ni za ai ta bid'a a shiga nan a shiga can, in yi shiru .

Mahaifi na kuwa tun da yaga na dena kwana da yunwa, ina sauya kayan sawa ta, sai ya fara ja na a jiki, inna tafi na samo  dan wani abu, sai na samma sa, ana haka Lamishi ta haihu, ta samu diya, an ka sa mata Mubaraka, tun da na dawo daga yawo na, na dora ido na kan Mubaraka na ji qaunar ta ta shiga zuciya ta, na sha ji a wajen Lamishi in mai jego na samun abinci me kyawu diya na samun ruwan nono mai yawa mai kyau, daga nan na hwara siyo abinci ina kawo wa dan ta ci qauna ta ta samu ruwan Nono mai kyau, kar ta zauna da yunwa kamar yanda na yi rayuwa da yunwa.

A hankali a hankali na hwara zama gagararre, kuma mutane suka hwara sanin mi nake ina samun kuddi, ni dinnan da kin ka gane ni, na yi gidan yari, sai da ya zamana in an kama ni, 'yan siyasa da kan su, suke hiddo ni, saboda ba qaramin nasara suke samu ba in suna tare da ni.

Gwauna da ya gabata shi ne ya tsunduma ni a babbar harkar da nake ciki yanzu, shi ne ya dauki su Lamishi aikin wanke wanke a gidan, mahaifin ki kuma shi ne wanda ya hwara koya min kisan mutane, har sai da ya zamto in ban kashe mutum ba a rana ina jin kamar ban tabuka komi ba a ranar, sai da ya zama ni ke jagorantar kisan gari guda,na qone shi ni da yara na, duk bakowa ne ya maishe ni haka ba face mahaifin ki.

Mahaifin ki ya aikata min laifin da ba zan iya yahe masa ba, ya sa an sace qauna ta, an yi lalata da ita da qananan shekarunta, duk wani buri nawa da nata an rusa mana shi.

Shi yasa na yi alqawarin yanda ya cutar da  qauna ta, da nafi so a rayuwa ta, ni ma sai na cutar da abinda ya fi so a rayuwar shi, na so kwarai na cutar da ke, kamar yanda ya yi ma qauna ta, amma ki sani a baya na yi zina, daga baya da na girma sosai na fara jin kyankyamin ta,se na dena, dan haka ni yanzu a duk abinda ni ke bana zina, na biyu soyayyar da nake miki ta hana ni cutar da ke ta kowace hanya, dan haka da na yunqura zan yi lalata da ke sai na kasa, Sultana ke da Mubaraka ku na da matuqar mahimmanci ga rayuwa ta, ba zan bari a cutar da ku ba, balle ni na cutar da ku da kai na.

Kamar yanda na yi miki alqawari, duk sanda ki ka ji ba ki so na, ki fadi min zan sauwaqe maki aure na, ki koma ga iyayen ki, amma fa ki sani, ba zan kyale mahaifin ki ba, sai na dau fansar abinda an ka yi wa qauna ta ta wani wajen,zaman ki anan zai banna mai rayuwa (bata masa rai) sama da yanda kike tunani, domin na zauna da shi, kamar yanda mubaraka take a waje na, haka ki ke a wajen shi"

Sultana ta ma rasa me zata ji a wannan labarin da Lawwali ya gama bata, abu daya kawai ta sani shi ne ta na son shi, alqawarin da ta masa ya na nan ba za ta sab'a ba, ta sani mahaifin ta ya fi bada mahimmiyar gudun mawa wajen lalacewar Lawwali, duk da ba shi ne ya fara b'ata shi ba,
In ba a taimaki matashin da ke da basira ba to kuwa zai illata qasa shima, kamar yanda Lawwali yake yi a yanzu.

Miqewa ya yi tsaye, ya ce,

"Wannan shi na dalilin da yasa ban kusance ki ba, ina jiran na samu yardar ki da amincewar ki, saboda ban aure ki dan sha'awa ba, na aure ki ne dan ina son ki, kuma ina so in dauki fansar abinda Gwauna ya yi wa Mubaraka na"

Shirun da ya ji, ya tabbatar masa da cewar Sultana bata yarda da shi ba, dan haka takawa ya fara yi, zai bar dakin, har ya kama hannun qofar ya ji Muryar ta da ta gaji da kuka ta ce,

"Ina zaka je ka bar amaryar ka ta na jin yunwa?"

Ta na nan kwance cikin bargon da ya rufe ta, ta ke maganar, cikin farin ciki ya juya ya na qare mata kallo, komawa ya yi ya zauna a gefen ta, ya janye mayafin da ya rufe mata gefen fuskar ta, ya shafa kuncin ta sannu a hankali .

'Daga ta ya yi kamar ya na daukan k'wai, a saman cinyar shi ya zaunar da ita,ya bata abincin, ta ci ta qoshi.

Sannan shi ma ya ci, qarfe daya da rabi na dare ya yi, a tare suka shiga dan bandakin da aka yi musu na musamman, duk da cewa na qasa ne, amma dai ba a hade yake da wanda kowa ke shiga ba.

Gani ya yi ta na alwala bayan ta wanke bakin ta, fita zai yi abin shi ta ce,

"Ba zaka yi alwala ba? Na ga baka yi sallah ba fa"

Kamar ya fada mata shi ya manta rabon da ya dora goshin shi a qasa ma, kawai ya tsaya, ya na kallon ta, bata sake masa magana ba, ta idar ta fita, ya jima a tsaye kamar ba ze yi ba, ya dau butar ya yi alwala, ya bi bayan ta.

Babu abin sallah a wajen, a saman carpet din wajen ta tsaya, ta ce

"Bismillah ka ja mu, muyi sallar isha'i, dare na yi, kar lokacin ta ya fita"

Shafa kan shi ya yi, ya zauna a bakin gado, ya ce,

"In ma na yi sallah yanzu ba zata karbu ba sultana basshi kawai ke ki yi sallar ki, na tabbata Allah zai karb'i taki, saboda baki zamo daga mutane iri na ba"

Gyara zama ya yi a saman gadon ya kwanta.

Mamaki ne danqare a cikin zuciyar Sultana me yake nufi da hakan???.......

*Hummmm hummmm*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 45:

A daren ranar haka Sultana ta na ji ta na gani, mijin da ya ke nata ya kwanta bai sallah ba, ba ta samu bacci ba sai da ta yi sallolin ta, sanan ta roqi Allah da ya shiryar mata da shi, a da in ta ga bai sallah ba sai ta yi tunanin ko ya yi a waje kafin ya je wajen ta, ko kuma zai yi in ya koma gida, amma tabbatar mata da ya yi, ya jima baya sallah abun ya daki zuciyar ta, mummunan duka kuwa.

A qasan carpet din ta kwanta, har bacci ya dauke ta.
Chapter 60 · 0% Book details